Thursday, 2 November 2017




WASU MALAMAN SUNCE BABU MATSALA ZUBAR DA CIKIN DABAI WUCE KWANA ARBA'IN BA




HISNUL-MUSLIM



         TAMBAYA
Assalamu alaikum malam,ga tambaya game da zubar da ciki,wasu malamai sunce ba matsala xubar da ciki matukar cikin bai wuce kwana arba'in ba,wasu kuma sunce matukar ba'a busa masa rai ba.to malam minene gaskiyar magana


          AMSA


To duk wani ciki haramunne azubar dashi saidai idan akwai dalili wanda addini ya amince dashi
Misali idan mace tanada ciki kuma likitoci suka tabbatar dacewa bazata iya haihuwaba zata mutu to koda cikin yakai wata nawa idan akwai yanda za,ayi azubar dashi aceci rayuwarta to yahalatta domin rayuwarta tafi muhimmanci fiyada wanda yake ciki dominshi baizo duniyarba



         Wata 4 shine ake busarai ga jariri acikin mahaifiyarsa sabanin malami shine waishin idan ciki baikai wata 4 ba idan akazubar dashi kisankai akayi tunda baikai lokacin busamar raiba? Sai wasu sukace bakisankai bane amma haramunne tunda ba abusamar raiba sai wasu malman sukace duk dahaka kisankaine domin daba azubarba shima zaisamu rai din kuma ba asan maize zamaba


Amma maganar cewa haramunne zubar da ciki wannan babu sabani duk malamai sunyadda cewa haramunne zubar da ciki koda yau akasamu cikin haramunne wannan babu sabani akan wannan fatawar saidaifa idan akwai wani dalili dayanuna sai anzubar idan dalilin muslunci ya amince dashi to shikenan
      
JUNAIDU BALA ABDULLAHI
Abu Salmah

Masu buqatan shiga Wannan Zaure na hisnul Muslim   suyiwa daya daga cikin wadannan  number  magana ta whatsApp+2348065523065
+2348162067271
    Domin Neman Karin bayani akan wata fatawa sai Ku kira wannan numbar↓
+2347065588557
سبانك اللهم وبحمدك، اشهد ان لا اله الا انت استغفرك واتوب اليك، 
Kuna iya samun mu ta  facebook ta wannan link indanke Qasa
https://mobile.facebook.com/Hisnul-Muslim-667684316700356/?fref=none

Share this


Author: verified_user

0 Comments: