Monday, 5 February 2018




MU KOYI YAREN INDIA DAGA ZAUREN INDIA

Home MU KOYI YAREN INDIA DAGA ZAUREN INDIA

*** MU KOYI YAREN INDIA ***
.
16,12,2018
***** DAGA ZAUREN INDIA *****
.
KALMOMI DA JIMLOLI MASU MUHIMMANCI DON BUNQASA KOYON YAREN HINIDI
.
Shirine Daga Cikin Jerin Kyawawan Jadawalin Shirye-Shiryen Musa Gudana Acikin Wannan Zauren, Inda Shirin Yake Koyar Da Yarukan India, Inda Yau Muka Xo Da Muhimman Kalmomi Da Jimlarsu Game Da Daya Daga Cikin Yarukan India Wato Hindi
.
GUNDARIN DARASIN
******************
GinShiQan Kalmomin Hindi, Tare Da Jimlolinsu.
.
Barka (Hello) – Namaste Kokuma Kace Pranam
.
Barkanka Dai Mubarak – Namaste Mubarak ji (ji Ana Amfani Da Ita A Qarshen Suna Badon Komaiba Sai Don Nuna Mutuntawa Ga Wannan Mutumin)
.
Ni – Mai
Daga Nigeria Nake – Mai Nigeria se hum
.
Nawa (Mine) – Mera
Wannan Nawane – Ye mera hai
.
Naka (Yours) – App ka
Wannan Nakane – Kya ye aap ka hai
.
Waye – Kaun
Kai Waye – Aap kaun hai
.
Kayan Sawa (Clothes) – Kapra
Ina Kayan Sawata Suke – Mera kapra kaha hai
.
Shayi (Tea) – Chai
Ina BuQatar Kofin Shayi – Mujhe ek cup chai chahiye
.
Ruwa (Water) – Paani
Ina BuQatar Kwalbar Ruwa – Mujhe ek bottle paani chahiye
.
Abinci (Food) – Khana
Bani Abinci – Mujhe khana do
.
Kana Jin Yaren HausaDo – Kya apkaa Hausa bolte hai
.
Yi Magana Ahankali – Dheray boliye
.
Eh (Yes) – Haa
a'a (No) – Nahi
Don Allah (Please) – Kripya
Nagode (Thank you) – Dhanevaad.
.
WASU JIMLOLIN HINDI MASU AMFANI
yaya Kake – App kaise hai
Ina Lafiya – Mai thik hu
Naji dadin Hadu Da kai– Aap se milkar khusi hui
Kai Waye – App kaun hai
Yaya Sunan ka – Aap ka kya naam hai
Sunana Mubarak – Mera naam Mubarak hai
Daga Ina Kake – Aap kaha se hai
Daga Zauren India Nake – Mai Zauren India se hu
Ina Zauren India Yake –zauren India kaha hai
Ina Mitar Take Tsaywa – Bus stand kaha hai
Ina Ban Daki Yake – Toilet kaha hai
Kaana Iya Taimakona – Kya aap meri madaad karenge
Menene Haka – Ye kya hai
Ina Sin Sayen Wannan – Mujhe ye kharidna hai
Nawa Wannan Yake – Ye kitnay ka hai
LRage Farashin – Daam kum kijiye
.
Da Akwai Wani Abu Da Yake Kawo Tangarda Wajen Koyon Yaren Hindi. Yaren Hindi Yana da Jinsin Suna Namiji Ko Mace (masculine or feminine); Inda Hakan yana Daga Cikin Abu Mai Wahala Wajen Koyon yaren Hindi. Baya Ga Haka Wasu Jahohin Da Dama Na Qasar India Suna Aiwatar da Yaren Hindi Daban Daban. Misa Yankin Bihari Suna Yaren Hindi Daban Da Yadda Yankini Delhi Sukeyi. Amma Muna Nan Mun Shirya Tsaff Don Warware Muku Xaree Da Abawa Afagen Koyon Yaarukan India.
.
Duka Duka Anan Muka Kawo Qarshen Wannan Shirin Sai Wani Satin Idan Allah Yakaimu, Wannan Shirin Yana xuwa QarQashin Gabatarwa:
Prof. SUAJ

Share this


Author: verified_user

0 Comments: