Thursday, 29 March 2018




HUKUNCIN LADANCI A SALLAH

Home HUKUNCIN LADANCI A SALLAH
HUKUNCIN LADANCI A SALLAH ? Tambaya : Assalamu alaikum Malam Meye hukuncin ladanci a sallah haram ne ko in akayi ba laifi ? Amsa: Wa alaikum assalam To dan'uwa mutukar liman yana daga murya, to yin ladanci bidi'a ne kamar yadda wasu malaman suka fada. Amma idan liman yana da lalura ko rashin lafiya ko kuma masallacin yana da girma ta yadda dukkan mamu ba za su ji muryarsa ba, to ya halatta, saboda a lokacin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi rashin lafiya, sayyidina Abubakar ya kasance yana daga murya da kabbara saboda ba'a jin na Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda Bukhari ya rawaito Allah ne mafi sani . Amsawa DR. JAMILU YUSUF ZAREWA 9/1/2014

Share this


Author: verified_user

0 Comments: