Thursday, 29 March 2018




HUKUNCIN YIN ASIRIN MALLAKAR MIJI

Home HUKUNCIN YIN ASIRIN MALLAKAR MIJI
HUKUNCIN YIN ASIRIN MALLAKAR MIJI : TAMBAYA TA 2437 ****************** Assalamu Alaikum malam barka da safia. malam ina cikin wani yanayi shine nace bari in nemi shawara gurin ka. Malam ina Shan wiya agidan aurena. Mujina ya kasance baya ganin darajata da kimata. ba so ko daya. Duk maganar da ta fito bakinsa sai ya fada min duk zafinta. Wulakanci kala kala. shekara Tara ina zaman hakuri darajar aure da darajar iyayena. Malam abin kamar an farraka mu. Duk Inda na samu addu'a don zaman lafia da soyayya yinta nake. Malam har da addu'o'in karya sihiri nayi sau dayawa. Mal shine aka ban shawara da in yanke faratuna  in kona in hada da jinin haila in bashi yaci zai daidaita. shine nace bari in tambaya shin ya dace inyi hakan. na gode Allah ya saka.in bukatar reply AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Baiwar Allah ki sani cewa zamanki agidan Mijinki zaman ibadah ne. Kuma ita ibadah ga mimini alkhairi ne. Kuma ba lallai ne dole sai komai ya tafi kamar yadda kike so ba. Dole sai kinyi hakuri da duk halin da kika tsinci kanki. Shi hakuri abu ne mai lada sosai kuma Mumini yana samun Qarin lada da daukakar darajoji ta, dalilin hakurinsa akan halin da ya tsinci kansa. Allah Madaukakin Sarki yace : "KAYI HAKURI SABODA HUKUNCI UBANGIJINKA.. ". Wata Mata takai Qarar mijinta wajen Manzon Allah (saww) akan halinsa. Sai Manzon Allah (saww) yace mata "KI DUBA, MIJIN NAN NAKI SHINE WUTARKI KUMA SHINE ALJANNARKI (WATO IDAN KINYI HAKURI DASHI KINYI MASA BIYAYYA ZAKI SAMU ALJANNAH. IDAN KUMA KIKA SA'BA MASA ZAKI SHIGA WUTA). Ki sani cewa Mijinki duk taurin kansa da wulakancinsa bai kai Fir'auna ba. Amma ga Matar Fir'auna nan ta shiga Aljannah saboda dalilin hakurinta da kuma Qardin imaninta. Kada ki biye ma Qawaye da 'Yan uwa Mata masu baki miyagun shawarwari. Hakika zasu sanyaki cikin ramin shirka ne da tsafe-tsafe irin na kafirci. Farce da kuma jinin haila duk Qazanta ne. Yadda kika san ke kanki ba zaki iya ci ba, to bai halatta ki sanya ma mijinki cikin abincinsa ba. Kuma bayan zaluncin dake cikkn yin hakan ga kuma Shirka ne da champe-champe. Kuma Allah ya hana. Kiji tsoron Allah ki tsaya bisa abinda yake na halal. Wato addu'a da kuma neman mafita awajen Allah. Tare da Qaurace ma bin miyagun shawarwari irin na bokanci. Ki duba amsar tambaya ta 1952 acikin jerin fatawoyin Zauren Fiqhu zaki ga mun rubuta halastattun hanyoyin da ake bi domin karya sihirin raba tsakanin ma'aurata. Kuma bayan shi ma mun sha yin rubuce-rubucen ayoyin karya sihiri. Ki binciko ta google ko facebook zaki samesu. Allah ya shiryi Mijinki ya ganar dashi gaskiya, Ya ha'da zuciyoyinku ku zauna lafiya ameen. WALLAHU A'ALAM. DAGA ZAUREN FIQHU (12-05-1439 29-01-2018).

Share this


Author: verified_user

0 Comments: