Thursday, 29 March 2018




NAMIJI ZAI IYA YIN KUNSHI?

Home NAMIJI ZAI IYA YIN KUNSHI?

*_NAMIJI ZAI IYA YIN KUNSHI !!!_*

                              *Tambaya?*
Assalamu alaykum Warahmatullahi, Da fatan malam yana lafiya, Malam ya halatta namiji yayi kunshi?

                                   *Amsa:*

Wa'alaikum assalam, Ya halatta namiji ya yi kunshi a gemunsa da kansa, da launin da yake ba baki ba, kamar yadda Annabi ﷺ ya yi umarni a yiwa Abu-Khuhafa mahaifin sayyadi Abubakar R.A lokacin da ya musulunta ranar bude Makka a hadisin Ibnu Hibban mai lamba: 5472 Wanda Shuaibu Al'ar'na'u'd ya inganta.

Ya wajaba namiji ya nisanci duk wani kunshi da zai zama kamanceceniya da mata, saboda Allah ya la'anci namijin da yake kamanceceniya da mata kamar yadda ya tabbata a hadisin Tirmizi mai lamba ta: 2784.

 Yana daga cikin ka'diojin da ya kamata a sani cewa: Kamanceceniya da mata yana iya banbanta daga wuri zuwa wuri, yana sabawa daga al'ada zuwa wata.

Allah ne mafi sani

15/11/2016

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: