🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲
♻♻ *PWA* ♻♻
_08185819176_
••••••••••••••••••••••••••••••
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
*BIRNIN SAHARA*
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
••••••••••••••••••••••••••••••
________________________________________
_______________________
*ѕtσrч/wríttєn ву✍🏻:*
👉🏻© *_Haiman Khan Raees_*
(℘ᾰ❡ḙ 1)
Na buɗe idanuwana a hankali yayinda hasken rana yake ƙoƙarin sani in rufesu. Cikin yanayin dagewa nayi yunƙurin tashi daga kwanciyar da nake amma sai abu ya faskara, domin kuwa ji nake tamkar an ɗauramin dutsen
# kwatarkwashi a ƙirjina.
Koda yake ina cikin hayyacina , amma sai kuma
gaɓobina suka kasa amsar umurnin da zuciyata take basu na su miƙe tsaye.
Tambayoyine sukayimin kwayam a cikin kwakwalwata a dai dai wannan lokaci; A ina nake? Me ya kawo ni nan Kuma ya akayi nazo nan?'' Waɗannan tambayoyine da bazan iya baiwa kaina amsar su ba. Na runtse idanuwana tsawon kimanin daƙiƙu talatin ina mai karanta kalmar shahada tare da yiwa Annabi S.A.W Salati, aikuwa ina buɗe idanuwan nawa sai abin mamaki ya faru domin nan take naji duk wata gajiya ta kau daga jikina tamkar a mafarki. Na miƙe tsaye yayinda na ke duban hagu da dama na.
A wani babban fili na tsinci kaina mai cike da rairayi, ga dukkan alamu dai a sahara nake. Filin a zagaye yake da wata irin murtikekiyar katanga mai matukar kauri da kuma Tsawo, yayinda a gefe ɗaya kuma wasu 'yan ƙananan gidaje ne masu kama da bukkoki. Gaba gare ni kuma wasu ɗirka_ɗirkan mutane ne masu kama da samudawa. kaida ganinsu kaga ƙarfafa. Ko wanne daga cikinsu sanye yake da wata baƙar riga ga kuma zabgegiyar takobi riƙe a hannun sa. Dakarun zasu kai kimanin dubu da ɗoriya. Nayi matuƙar mamakin ganina a wannan wurin, domin abun da zan iya tunawa shi ne, kwanciya bacci a daki na da nayi. Na ɗanyi taku ɗaya da nufin yin 'yar tafiya. Aikuwa sai waɗan nan dakaru suka zare takubbansu da nufin haiƙe min. Cak! Na tsaya sannan na koma inda nake tun da farko, kamar aljanu sai dukkan dakarun suma suka koma yadda suke. ''lallai za'a yita,'' na ayyana a Raina yayin da gaba na ke dukan Tara-tara. Nandai na fara tunanin yadda za'ayi inbar wannan wuri, ina cikin wannan tunani ne naji anbuga wani tambari mai matuƙar ƙara wanda nan take ƙarar tambarin ta cika duk ilahirin wajen. Bayan gushewar ƙarar tambarin ne sai naji alamar wani abu na tunkaro ni daga bayana. Cikin hanzari na juya ina mai kai dubana izuwa ga abinda ke nufo ni.
Dam!!! Naji gabana ya faɗi sakamakon abinda na gani. Bakomai na ganiba face *DIANA* sanye da kayan sarauta ga kuma dakarunan a tare da ita tamkar zasu yaƙi. Diana ta ƙaraso gabana tana mai murshi, koda ya rage baifi saura taku shida a tsakanin mu ba sai ta tsaya cak!!
A wannan lokaci muna iya jin numfashin JUNA ni da ita. Ta ƙuramin ido yayinda fuskarta ke ƙara faɗaɗa da murmushi, sannan kuma idanunta cike da wasu bayanan da na kasa fahimta. Bayan wani ɗan lokaci sai ta buɗi baki a cikin sansanyar murya tace dani...
Hmm me kuke tsammanin zata faɗi min? Mu tara a gaba. *HAIMAN KHAN*
🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲
♻♻ *PWA* ♻♻
_08185819176_




0 Comments: