Saturday, 21 April 2018




BIRNIN SAHARA 2

Home BIRNIN SAHARA 2
🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲

♻♻ *PWA* ♻♻

_08185819176_

••••••••••••••••••••••••••••••
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
     *BIRNIN SAHARA*
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
••••••••••••••••••••••••••••••

             ________________________________________


   _______________________
         *ѕtσrч/wríttєn ву✍🏻:*
👉🏻© *_Haiman Khan Raees_*
        

            (℘ᾰ❡ḙ 2)



Bayan wani ɗan lokaci sai ta buɗi baki a cikin Sassanyar Murya tace dani: '' Barka da zuwa Birnin Sahara yakai Haiman! kasani cewa abin alfahari ne kasancewar wanzuwarka a cikin wannan Birni namu mai albarka!'' Nayi ajiyar zuciya sakamakon jin kalamanta domin na fahimci cewa akwai yiwuwar zan iya samun damar barin wajen Lafiya. Amma duk da wannan tunani da nayi, hakan bai hanani tambayarta abinda ke damuna ba, ''Diana ina ne nan? Na tambayeta yayinda na dai daita yanayin fuska saboda kada ta fahimci wani abu dangane da abinda ke damuna.

 ''Birnin Sahara kenan, kuma nan inda muke yanzu shine gidan da ake baiwa jarumaina horon yaki. Ta bani amsa. ''ehmm Jarumanki fa kika ce? Kina nufin duk waɗannan Samudawan a ƙarƙashinki suke? Na tambaya cike da mamaki. ''hahaha ta fashe da dariya, ta ci gaba da dariyarta har saida ta gaji sannan sai tace dani: ''tabbas waɗannan jarumai suna ƙarƙashina ne kuma ko rabin su ma baka gani ba, kuma su sun kasance masu biyayya tare da girmamawa a gareni kasancewata sarauniya a gare su.

'' ''Oh! Wai dama ke sarauniya ce? Na tambaya ina mai riƙe ƙugu tare da girgiza kai, to amma me yasa baki taɓa faɗamin ba? ''kai!!! Wani garjejen ƙato ya daka min tsawa yana mai nuna ni da wani ƙaton mashi wanda saboda kaifi har walƙiya yake a cikin hasken rana. Na ɗanja da baya sakamakon ganin wannan al'amari, amma bisa mamaki na sai naga Diana ta bashi umurnin ya ƙyaleni. ''Haiman ka sani cewa ni sarauniya ce mai ƙarfin iko, don haka ka kyautata kalamanka a gareni, in kuwa ba haka ba to zaka fuskanci hukunci mai tsanani irin wanda baka taɓa fuskantar kamarsa ba. Diana ce tayi wannan furuci. 

''to naji Sarauniyarsu, yanzu mene dalilin kawo ni nan? Na tambayeta cikin alamun jin kai da taƙama. ''hmm tayi ajiyar zuciya sannan taci gaba da cewa: na fuskanci har yanzu kana tantamar girman sarautata don haka ina mai baka Shawara da ka ajiye zafin kanka kayi biyayya domin nan fa Birni na kake in kuma ba haka ba zan nuna maka cewa da dayanzu ba ɗaya bane'. 
SARAUNIYA Diana ce tayi wannan Furuci. Ko da jin haka, sai nima na bushe da dariya irin ta keta, bayan nayi ta ishe ni, sai na Kalli Diana ido cikin ido na ce da ita: "Amma lallai na lura cewa kwakwalwar ki ta samu matsala, yanzu in banda tsabar rashin adalci da tsantsar Mugunta, ta yaya za'a yi ki Sato mutum daga gidan su ki kawo shi wannan rairayin kuma kice kina bukatar yayi miki biyayya? Kuma ki rasa Wanda ma zaki yiwa hakan sai ni? Shin Kin manta cewa ni ruwa ne bana son takura? Lallai ya kamata ki sake tunani, domin abinda kike tunani ba fa zai yiwu ba". Wadannan kalamai nawa ba karamin batawa Diana rai suka yi ba domin tunda na fara dariya ta naga ta turbune fuska, ai kuwa ina gama wannan jawabi nawa sai Sarauniya Diana ta kalli wadannan Lafta laftan Samuwadan a fusace tace da su: "Ku kamashi ku kaishi kurkuku! Nan take suka nufo kaina da nufin su yimin Kamun kazar Kuku...

Zan Ci Gaba In Shaa Allaah.


# www.haiman.com.ng 
# www.facebook.com/HaimanRaees 
# @HaimanRaees 
# HaimanRaees 
# Infohaiman999@gmail.com 

🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲

♻♻ *PWA* ♻♻

_08185819176_

Share this


Author: verified_user

0 Comments: