Sunday, 22 April 2018




BIRNIN SAHARA 3

Home BIRNIN SAHARA 3

🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲

♻♻ *PWA* ♻♻

_08185819176_

••••••••••••••••••••••••••••••
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
     *BIRNIN SAHARA*
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
••••••••••••••••••••••••••••••

             ________________________________________

   _______________________
         *ѕtσrч/wríttєn ву✍🏻:*
👉🏻© *_Haiman Khan Raees_*
       

            (℘ᾰ❡ḙ 3)


Banyi aune ba kawai sai naga waɗan nan Samudawan sun durfafoni da niyyar cafke ni. Da farko har na yanke shawarar in tsaya su kamani kawai don nasan dai in ma an kaini kurkukun dole a fito dani, amma daga baya kuma sai nayi tunanin me zai hana inyi ƙoƙarin guduwa? Tunda ance mai rai bai rasa motsi? A dai dai lokacin da nake wannan tunani tsakanina da dakarun Diana bai fi tazarar taku Ashirin ba. Don haka banyi wata_wata ba na falfala da gudun tsiya na nufi wata ganuwa da na hango.

Haba! Nanfa aka kasa tsere a tsakanina da waɗannan dakaru nata. A zahiri sun fini gudu, to amma kasancewar ni gudun ceton rai nake yi sai na ƙara dagewa. Amma fa a duk sanda na waiga sai in gansu dab dani. Babban abinda yafi ɗauremin kaima shine, sahara ne wajen babu daɗin gudu, badon ma Allah yasa mun saba da gudu a cikin yashi ba a ƙauyen mu to da tuni sun kamani, kuma gashi ban kai ga isa ganuwarba.

Haka dai na wanzu ina mai ci gaba da falfala gudu baji ba gani amma sai ya zama na banza domin kuwa gab dakarun Diana suke da su cimmin.

Kwatsam! Sai na hango wani tarin itace da aka jera a jikin wannan ganuwa dake zagaye da inda muke. Nan fa na kara azama wajen ganin na kai ga wannan tarin itace. Ni da nufi na shi ne in yi matakala da shi in haura Katangar.

Ina zuwa kuwa banyi wata wata ba wajen hawa kan wannan tarin ITATUWA, sai da ya zamana bai fi Taku biyar ba kama Katangar sai naji an kwala min kira da wata murya wacce take tasa naji gabadaya Na'urorin jikina sun tsaya cak! wani tunani ya faɗo min arai: Sadiya! Kwakwalwata ta fara zarya a tsakan kanin abubuwan da suka faru dani a baya, inda cikin ƙan ƙanin lokaci ta kamomin fuskarta a cikin zuciyata.

SADIYA itace macen da nake matuƙar so a rayuwata kamar yadda nake son tawa rayuwar, kuma tasha salwantar da tata rayuwar domin tawa. Yanzu shikenan mun rabu da ita? Ina labarin Abokaina waɗan da nine sanadin murmushin da kan sauka a fuskarsu? Lallai ya zama Dole na rayu domin saduwa dasu.
Waɗannan da ma wasu maganganu makamantansu sune suka yita min karo a cikin zuciyata.

Feu! Feu!! Feu!!! Naji karar kibiyoyi suna wuce ni. ''Tashin hankali! Na faɗi a fili ba tare da nasan na faɗi ba Yayinda hankali na kuma ya komo jikina. Nan take na fara karanta Ayatul kursiyyu tare da LA'ILA HA ILLAH ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZZALIMIN a zuciyata. Aikuwa nan take naji wani sabon ƙarfi ya shige ni kuma gaba ki ɗayan wani tsoro da fargaba gami da gajiya sun fita daga zuciyata.

Cikin Wani irin Baƙin zafin Nama na juyo da baya ina mai falfalawa da wani irin azababben gudu na ban mamaki tamkar tauraruwa mai wutsiya.

Aikuwa sai gashi cikin abinda baifi daƙiƙa sittin ba na dawo da baya ina ratsawa ta cikin wadannan dakaru kamar iska. Kafin su Ankara har na wuce su gaba daya na basu rata.

Nan dai na ci gaba da wannan gudu ina mai bin sautin muryar Sadiya dake ta kira na cikin Karaji da kururuwar neman Taimako.

Yayinda na iso dai dai inda na farka tun a Karon farko sai nai turus, ba komai ne ya sani yin hakan ba face ganin da na yiwa Sadiya daure cikin sasarin bakin karfe kamar wata baiwa.

Ta dago kai a hankali ta dube ni tana mai cewa....

Zan Ci Gaba In Shaa Allaah.

# www.haiman.com.ng
# www.facebook.com/HaimanRaees
# @HaimanRaees
# HaimanRaees
# Infohaiman999@gmail.com

🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲

♻♻ *PWA* ♻♻

_08185819176_

Share this


Author: verified_user

0 Comments: