Wednesday, 25 April 2018




BIRNIN SAHARA 4

Home BIRNIN SAHARA 4

🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲

♻♻ *PWA* ♻♻

_08185819176_

••••••••••••••••••••••••••••••
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
     *BIRNIN SAHARA*
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
••••••••••••••••••••••••••••••

             ________________________________________

   _______________________
         *ѕtσrч/wríttєn ву✍🏻:*
👉🏻© *_Haiman Khan Raees_*
       

            (℘ᾰ❡ḙ 4)



Ka taimakeni Haiman!! Kazo ka taimakeni!

Ganin ta a cikin wannan hali ne yasa Nan take naji wani irin baƙin ciki ya lulluɓeni saboda tsantsar ƙaunar da nake mata. Kawai sai Na nufi inda take da wannan azababben gudu nawa da nufin in taimaka mata, sai da yarage baifi taku huɗu ba in isa gareta kawai sai naji wani abu mai nauyi da kuma ƙarfin gaske ya doki ƙeyata.

Daga nan ban sake sanin abin da ke faruwa ba sai dai kawai tsintar kaina nayi a wani ɗaki mai matuƙar faɗi tare da tsawo. A ƙalla tsawon ɗakin zai iya cinye tafiyar daƙiƙa ɗari da ashirin don bana ma iya hango ƙarshen sa.
Yayinda na tsinci kaina a wannan hali, sai na kasance mai baƙin ciki domin na fuskanci cewa kamani akayi. Ina cikin wannan hali sai naji alamun motsi daga ɓangaren dama na, na kai dubana izuwa gurin da motsin yake fitowa, aikuwa sai nayi arba da wani tsoho tukuf. Fuskarsa cike take da farin gashi wanda wuya ta sanyashi ya koma rawaya.

Gabaki ɗayan fatar jikinsa ta tamuƙe tamkar ɗanyar gyaɗar da aka shanyata ta bushe, amma wani abun mamaki shine; idanuwansa ƙyarr tamkar na matashin da ba zai wuce shekaru ashirin da biyar ba.

Nayi matuƙar mamakin wannan al'amari, amma sai ban nuna alamun mamakina a fili ba sakamakon ganin yadda tsohon ya ƙuramin ido ko ƙyaftawa baya yi. Nan fa muka fara kallon-kallo ni da wannan tsoho ba tare da ɗayan mu ya ce da ɗayan uffan ba, bayan mun ɗan daɗe a haka sai naji yace dani: "amincin Allah ya tabbata a gareka yakai ɗanuwana Haiman, ina mai maka barka da zuwa ɗaki mafi karamci daga cikin ɗakunan gidan yarin *BIRNIN_SAHARA !*

Na zazzaro ido cikin alamun mamaki don naji ya faɗi sunana kuma ma har yana dangantani da ɗan uwansa. Wane ne kai? Kuma me kake yi a nan? Sannan me yasa ka kirani da ɗanuwanka alhalin bamu taɓa haɗuwa ba? Na jera masa waɗannan tambayoyi yayinda nayi ƙoƙari na mike tsaye.

Sai a wannan lokaci ne na lura cewa ashe ma ƙafata a ɗaure take da wata murtukekiyar igiya anyimin ɗaurin talala. Koda ganin haka sai nayi murmushi kawai don nasan wannan aikin banza akayi. Na dubi tsohon nace kai nake jira ka bani amsa.

''ni sunana Imran kuma ni mutumin Habasha ne, a ƙalla yau wata na biyu a kulle anan, sakamakon wani aikin sihiri dana aikata akan wani azzalumin barden Sarauniya_Diana ita kuma shine ta mai dani tsoho kamar yadda ka ganni ɗinnan da nufin horar dani."

Bayan Imran ya gama waɗannan bayanai sai na sake tambayarsa da cewa: to kai kuma mene ne dalilinka na aikata aikin sihiri a gareshi? Sai Imran yace dani: labarin yana da tsawo gaskiya amma dai ina so ka sani cewa mahaifina ya kasance ƙasurgumin Boka na gaban kwatance kuma nima na gajeshi ta wannan fannin kuma tun asali akwai gaba mai tsanani a tsakanin zuri'ar mu data su Diana....

Yana kawo nan a zancensa sai mukaji takun sawaye yana nufo inda muke don haka sai Imran yayi tsit. Bamu ɗauki wani dogon lokaci ba sai ga dakaru sun tunkaro ɗakin da muke, wani gabjejen ƙato ne a gaba yana riƙe da wata zabgegiyar bulala kamar ta dukan dawakai. Ga kuma sauran dakarun masu tarin yawa suna take masa baya.

Koda suka zo daidai ƙofar ɗakin da muke sai suka rabe gida biyu inda daga tsakiyarsu sai ga farincikin rayuwata Sadiya ta bayyana a ɗaure, gabaki ɗayan ilahirin jikinta yayi matuƙar yin datti yayinda tufafinta suma sun yayyage, kyakkyawar fuskarta ta kumbura saboda tsananin tsabar tsagwaron wahala. Koda ganin irin halin da masoyiyata take ciki, sai naji wani irin bakin ciki ya rufeni ƴayinda tausayinta ya kamani bansan sanda ƙwalla ya fitomin daga idnuna ba saboda nasan duk a sanadiyya ta ne ake bata wannan wahalar. Banyi aune ba sai naji muryar shugaban nasu ya ambaci sunana. ''Haiman! Haiman! Kenan mai masoyiya! To Haiman ga masoyiyarka na kawo maka domin kuyi ganawar ƙarshe saboda daganan sai dai a ƙiyama kuma kaida ƙara ganinta.

Koda jin haka sai nayi sauri na rarrafa inda take yayin da itama ta ƙara so kusa dani. Tsawon lokaci muna kallon juna ba tare da wani ya cewa wani komai ba. ''sadiya ki gafarceni nasan cewa duk a dalili nane kika shiga wannan hali..... Dakata haiman, ta katse ni, sannan ta ci gaba da cewa kasani cewa na gano wani abu da baka sani ba a gidan nan don haka duk yadda za'ayi ka tabbatar ka tserar damu daga wannan wuri, nasan zaka iya masoyina, kada ka manta da alƙawarin mu kuma kada ka manta da kokai wanene. Ina ƙaunarka haiman.

Daga nan bata ƙara cewa komai ba. Abinda ya ɗauremin kaima shine duk da tayi maganarta a fili amma kamar ni kaɗai ne naji maganar nata. Banyi aune ba sai kawai naga sun jata zasu koma da ita shi kuma shugaban dakarun yana ta ƙyalƙyala dariyar mugunta. Shin me kuke tunanin zai faru?

Zan Ci Gaba In Shaa Allaah.

# www.haiman.com.ng
# www.facebook.com/HaimanRaees
# @HaimanRaees
# HaimanRaees
# Infohaiman999@gmail.com

🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲

♻♻ *PWA* ♻♻

_08185819176_

Share this


Author: verified_user

0 Comments: