TAMBAYA TA 19
Post By:
Hausa Novels
Tambaya Mabudin Ilimi
TAMBAYA ========= đ Assalamu Alaikum malan barka da warhaka sannu da kokari da amsa mana tambayoyi da kake yi Allah yasaka da alkhairi Allah yasaka maka ladan acikin mizaninka mln tambayane gareni mu 2ne agurin mijinmu to ita uwargidan nawa nurse ce tana zuwa aikin dare ta kwana kuma ba gidanmu daya ba kowace da gidanta to mln duk ta tafi zai iya zuwa gida na ya kwana?sannan idan ta kare aikinta na kwana sati daya zai rama mata kwananta ne ko kuwa munason ataimaka mana da amsa gudun shiga hakkinta AMSA ====== đ Al'amarin rabon kwana Allah baice ga yadda za'ayi ba, wato baice dole sai kwana Biyu-biyu za'ayi ba haka baice sai kwana ukku-ukku ba, da dai sauransu, abinda Allah tace muyiwa junanmu adalci. Wato mutum ya zama mai adalci a tsakanin matansa. Sannan Ya danganta da tsarin da kuka zauna kukayi ke da ita da Kuma shi Mai gidan, kuma ya zama akwai yarjajjeniya akan hakan, kuma ba wanda aka zalinta, wato ita bata zalinceki ba, kema baki zalinceta ba, haka shima maigida Baku zalunceshi ba. Kenan idan Ku dukanku kun gamsu da yadda kukeyi, shikenan magana ta kare. Abinda ba'aso anan shine, a tirsasawa wata dan dolenta ta yarda Sabida tana son zaman gidan, alhalin kuma akwai zalunci a ciki. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876



0 Comments: