Wednesday, 9 May 2018




BIRNIN SAHARA 10

Home BIRNIN SAHARA 10
🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲

♻♻ *PWA* ♻♻

_08185819176_

••••••••••••••••••••••••••••••
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
     *BIRNIN SAHARA*
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
••••••••••••••••••••••••••••••

             ________________________________________


   _______________________
         *Ρ•tΟƒrΡ‡/wrΓ­ttΡ”n Π²Ρƒ✍🏻:*
πŸ‘‰πŸ»© *_Haiman Khan Raees_*
        

            (℘αΎ°❡αΈ™ 10)

_______________


A Can wani bangare daban na birnin Sahara kuma, iyalan Zuri'ar Su Dargazu ne Sukayi Cirko-Cirko akan Dargazun, Yayinda shi kuma ya zauna kafa a harde sai huci yake yi kamar wani Maciji. Kowa ka gani daga cikin Zuri'ar Tasu ransa a bace yake, kuma ba komai ne ya jawo hakan ba face irin Bakaken Maganganun da Wannan Bakon Da Sarauniya Diana Ta sa aka dauko yayi masa. Kuma kowane mutum daga cikin Zuri'ar tasu saida ya sha alwashin ganin bayan wannan Bakon, amma hakan bai sa hankalin Dargazu ya kwanta ba.

Ana cikin haka ne sai aka ji karar takun zuwan wani, cikin sauri kowa ya waiga yana kallon inda sautin Sawayen yake fitowa. Basu dade a wannan hali ba sai ga wata kyakkyawar budurwa wacce ba Zata wuce Shekaru goma sha TAKWAS ba ta Kunno Kai, duk iya inda ake neman kyakkyawar mace wannan mace takai, Abu daya ne ya bata zancen, wannan kuwa ba komai bane face Kirar Sadaukai da take da shi da kuma Fuskar Shanu da take yi a koda yaushe. Haka ta taho cikin tafiyar Izza ta iso gaban Dargazu. Ko da zuwan ta gaban nasa sai ta rusina da Guiwa daya a kasa sannan ta Dunkule hannun ta na dama ta daura shi a Kirjinta tana mai Dukar da kanta kasa, daga nan sai ta fara magana da cewa; "yakai Abbana, Wane Mai karar kwana ne ya bata maka rai? Wanene shi da har zai ja da kai? Na rantse da girma da Darajar Abar BAUTAR mu Tayatata Sai na kamo shi da hannaye na, in yanka shi sannan in baiwa Abar bautar mu jinin sa a Matsayin Fansar bacin ranka". Haka dai wannan budurwa ta ci gaba da shan alwashin ganin bayan wanda ya batawa Mahaifin ta rai. Bisa mamaki sai ga shi Kalaman wannan budurwa sun sa Dargazu ya sauko daga bishiyar fushin da ya hau, bayan ya kawo wani gwauron Numfashi ya ajiye, sai ya dubi wannan budurwa cikin wani irin YANAYI na karaya yace: "yake 'yata Dardira! Ki sani cewa, babu Mahalukin da ya taba kallo na ido cikin ido batare da ya Firgita ba, amma sai gashi yau an samu wani dan Tatsitsin yaro yana kallo na yana gaya min sai yaga bayana? Ni fa gani nake kamar wannan Bakon yaro yana tattare Da wani Bakon al'amari, domin irin Wutar bacin ran da na gani a idanuwan sa Yayinda yake magana..."

"Haba baba! Ta ya za'a ce kana sarkin Yakin Birnin Sahara amma kana Shakkar wani dan Mitsilin Yaro wanda zuwa daya zan mai in Sheqe shi, shin Anya Abbana ne kuwa da na sani a da yake tare da ni a yanzu? Anya kuwa Dargazun da na Sani ne wanda ya kama zaki da hannun sa ya maida shi abin farauta? Dardira ce tayi wannan furuci Yayinda ta katse Mahaifin ta daga zancen da yake yi.

Aikuwa kamar wanda Aljanu suka shafa sai aka ga Dargazu yayi Zumbur ya Mike tsaye sannan ya Takarkare ya rusa wani uban ihu wanda sai da dakin da suke ciki ya girgiza, bayan yayi I hun sa ya gaji sai kuma ya kama yiwa kansa kirari. Bayan ya gama sai ya dauko wani katon tulun Giya dake gefen sa ya daga shi ya Tuttula a cikin sa ya shanye tas! Sannan yayi wata gyatsa mai kama da tashin tsohuwar mota. Daga nan sai ya barke da dariya kawai abinsa kamar babu abinda ke damun sa, suma Jama'ar dake tare da shi sai suka kama dariyar kamar sabbin mahaukata.

Wannnan shi ne abinda ya faru tsakanin Sarkin Yaki Dargazu da Diyar sa Dardira tare da sauran jama'ar sa.

Zan Ci Gaba In Shaa Allaah 

_*Phone:*_
 08185819176

_*Web:*_ www.haiman.com.ng 

_*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees 

_*Twitter:*_ @HaimanRaees 

_*Instagram:*_ Haimanraees 

_*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com


🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲

♻♻ *PWA* ♻♻





Share this


Author: verified_user

0 Comments: