Saturday, 5 May 2018




BIRNIN SAHARA 8

Home BIRNIN SAHARA 8
🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲

♻♻ *PWA* ♻♻

_08185819176_

••••••••••••••••••••••••••••••
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
     *BIRNIN SAHARA*
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
••••••••••••••••••••••••••••••

             ________________________________________


   _______________________
         *ѕtσrч/wríttєn ву✍🏻:*
👉🏻© *_Haiman Khan Raees_*
        

            (℘ᾰ❡ḙ 8)



¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤

Al'amarin Sarauniya Dayana Kuwa, tun bayan da ta tabbatar da cewa an kama Haiman kuma harma an kaishi gidan yarinta an kulle, sai hankalinta ya kwanta ta daina zulumi da fargaba.

Daga nan bata zarce ko ina ba face gidan sarautar birnin Sahara wanda ya kasance tamkar wani ɗan ƙaramin ƙauye saboda girma.

Gidan ya ƙawatu ƙwarai da gaske, ko ina a cikin gidan haske ne ke fita sakamakon ginin katangun gidan an yi su ne daga duwatsun wuta waɗan da aka sarrafasu izuwa fararen duwatsu masu matuƙar ban sha'awa. Shi kuwa shafen da akayiwa bangon ginin ya kasance wani ɓangare ne daga yaƙutu da kuma zubardaji, yayin da shi kuma daɓen gidan sarautar gaba ɗaya anyi shi ne da zallan zinare. Saman ginin kuwa an ƙawata shi ne da zallan azurfa.

Kai in tsaya bayyana maka irin kyawun gidan sarautar zai iya jawo sanadin da zaka kirani maƙaryaci domin kyawun gidan ya wuce ƙima.

Daga ƙofar gidan sarautar zuwa ɗakin da Sarauniya Dayana take kwana akwai ƙofofi guda goma sha uku, kofar farko wacce ita ce ƙofar shiga gidan tana ɗauke da kimanin dakaru ɗari biyar kuma ko wannen su yana ɗauke da Muggan makaman yaƙi.

Su kuma sauran ƙofofin suna ɗauke ne da dakaru ɗari uku uku a kowace ƙofa, yayinda a cikin ɗakin da Sarauniya Dayana take kuma akwai kuyangi kimanin dubu ɗaya da ɗoriya. Shi kanshi ɗakin da Sarauniya Dayana take yana da ɓangarori uku. Ɓangare na farko shine inda aka tanada mata domin ajiye kayan shafa da kuma kayan sawa.

Ɓangare na biyu kuma shine inda banɗakin Sarauniya yake wanda ke ɗauke da makewayi da kuma wani ƙaton bawon wanka wanda yayi girman wani ɗan ƙaramin tafki.
Shi kuwa ɓangare na uku a nan ne makwancin Sarauniya Dayana yake. Gado ne faffaɗa wanda yake ɗauke da wata Luntsumemiyar katifa mai matuƙar laushin gaske wacce inda gajiyayye zai kwanta akai zai iyayin kwana uku yana bacci akai bai farka ba domin a tunanin sa awa ɗaya kawai yayi a kwance.

Daga ɗaya ɓangaren dake ɗakin dake kallon gadon kuma wasu ɗirka ɗirkan kujeru ne masu taushin gaske waɗan da aka tanada domin zaman manyan baƙi. Koda Sarauniya Dayana ta isa turakarta, sai nan da nan kuyangi suka kamata suka kaita ɓangaren da makewayinta yake,a wannan lokaci wannan ƙaton baho da na baka labari a baya cike yake da ruwa mai ɗumi gami da furanni masu ƙamshin gaske sun mamaye ko'ina.

Da zuwansu sai wasu kuyangi su uku suka cire wa Sarauniya Dayana Tufafin dake jikinta, sannan sai wasu ukun sukai kama_kama suka sakata a cikin wannan bahon mai girma.

Dama akwai wasu guda uku a cikin bahon, don haka daga shigarta sai suka shiga cuɗa ta a ruwan. Kafin kace kwabo, sun kammala mata wankan.

Daga nan wasu uku suka fito da ita, bayan ta fito ne sai kuma wasu ukun suka tsane mata ruwan dake jikinta. Daga nan kuma sai wasu ukun suka kawo mata wata doguwar riga ta alfarma suka sanya mata.

Bayan nan sai kuma wasu kuyangi ukun suka kama hannayenta izuwa inda kayan shafanta suke wanda wani ƙaton madubi yayiwa ado na girma da Alfarma. Har ila yau dai wasu Kuyangin uku daban suka zo yi mata kwalliya na ban girma. Kai in dai taƙaice maka labari komai na aikin gidan haka kuyangin suke gabatar dashi uku uku kamar asiri.

Wani abin da nasan zai baka mamaki idan na faɗi shine, Sarauniya Dayana fa ba wata babbar mace bace, kwatakwata shekarunta goma sha bakwai a duniya.

Bayan an kammala mata kwalliya da komai da komai, sai kuma aka kaita gaban teburin abinci wanda ke ɗauke da kayayyakin ciye-ciye da lashe-lashe gami da kayan ƙwalama irin na tanɗe-tanɗe da tsotse-tsotse.

Koda Sarauniya Dayana ta kai hannu domin ta ɗauki wata Tuffa data birgeta sai kawai taga fuskar Sadiya tana mata murmushin Mugunta. Cikin razana ta ɗan ja da baya. Nan da nan sai Shugabar kuyangin Sarauniya Dayana, wata mace kyakkyawa da ake kira Hameedah ta zo gabanta ta duƙa tana mai cewa: ''Ya shugabata mene ne ya wanzu a gareki naga kin tsinci kanki a wani yanayi na firgita? Shin wani abu nayi daya firgita ki? Idan har hakane ina mai nema afuwarki ki yafemin, ba da nufin ɓata miki rai nayi ba, asalima ni kaina ban san nayi ba.
Sarauniya Dayana ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce: "Ya ke Hameedah, ki sani cewa tun da nake dake baki taba bata min rai ba ko da sau daya ne, kuma baki taba sabama umurni na ba, in kuwa hakane, to me zai sa in yi fushi da ke?" 

Hameedah ta Rusina kasa sannan tace "ki gafarce ni Ranki Shi dade", 

SARAUNIYA Diana ta yi ajiyar zuciya sannan tace ''In baki manta ba tun kan mahaifina ya rasu ya ce bai yarda da kowace kuyanga ba a gidan nan sama da ke don haka ne ma ya zaɓar min ke a matsayin wace zata dinga kula da ni tare da bani shawari na musamman akan al'amuran rayuwata.

Lallai yau ranarki ta tazo kuma ina fata ba zaki bani kunya ba,''
''Faɗi buƙatar ki ya shugabata, kowace irice zan tabbatar da yiwuwarta domin ganin farin cikin ki koda kuwa hakan na nufin sanadin salwantar rayuwata ce,'' Hameeda ce tayi wannan furuci.

Sarauniya Dayana ta sake yin ajiyar zuciya sannan ta ɗaga kai ta dubi sauran kuyangin dake ɗakin, kafin kace me! Tuni sun fice daga ɗakin. Bayan kuyanging sun fice daga ɗakin sai Sarauniya Dayana ta kama hannun kuyanga Hameeda suka shige cikin turakarta domin su tattauna.

Wannan shine abinda ya faru a tsakanin sarauniya Dayana da Kuyangarta Hameeda.

^^^^^^^^^^^^^^^^^^^

Zan Ci Gaba In Shaa Allaah 

_*Phone:*_
 08185819176

_*Web:*_ www.haiman.com.ng 

_*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees 

_*Twitter:*_ @HaimanRaees 

_*Instagram:*_ Haimanraees 

_*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com


🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲

♻♻ *PWA* ♻♻




Share this


Author: verified_user

0 Comments: