Monday, 7 May 2018




BIRNIN SAHARA 9

Home BIRNIN SAHARA 9
🌲🌲*_PRODUCTIVE
WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲

♻♻ *PWA* ♻♻

_08185819176_

••••••••••••••••••••••••••••••
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
     *BIRNIN SAHARA*
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
••••••••••••••••••••••••••••••

             ________________________________________


   _______________________
         *ѕtσrч/wríttєn ву✍🏻:*
👉🏻© *_Haiman Khan Raees_*
        

            (℘ᾰ❡ḙ 9)

_______________



KADUNA


A cikin birnin Kaduna kuwa, tuni labarin bacewar mutane biyu a rana guda kuma a kusan lokaci guda ya mamaye dukkan kafofin yaɗa labarai, kama daga gidajen talbijin da kuma kamfanin buga jaridu har zuwa gidajen rediyo.

Yayin da 'yan uwan waɗan da abin ya shafa kuwa, babu abinda ake musu face jaje da tayasu jimamin abin da ya faru sakamakon irin halin da suka shiga.

Gidan Talbijin na Alheri wanda ke haɗe da gidan rediyon sa shine gidan Talbijin na farko da ya fara bayani dangane da ɓacewar mutanen. A cewar shugaban jami'an tsaro na jihar kaduna kuwa, cewa yayi ko a tarihi bai taɓa jin in irin wannan al'amari ya faru ba. Kuma ya tabbatarwa manema Labarai cewa akwai sa hannun Aljanu ko kuma wasu ma'abota aikin Tsafi da sihiri a cikin al'amarin.

Babbar Jaridar nan ta Hausa kuwa wato Aminiya cewa tayi akwai yiwuwar maƙiyan mutane ukun ne suke bibiyar rayuwarsu tare da wasu makusantansj domin yin garkuwa dasu wajen cimma burin su.

Kada FM na ɗaya daga cikin Gidajen Rediyon da aka fi sauraro a cikin garin kaduna da kewaye. Kuma suma sun bayyana cewa abin da ya faru dai kam akwai alamar tambaya a cikin al'amarin. Kamfanin Jaridar Leadershi pHausa ta buga wani rahoto mai taken YADDA ABIN YA FARU, inda tayi bayani kamar haka: A Ranar Laraba uku ga watan mayu da misalin ƙarfe 12:38 na rana yayin da wani matashi mai suna Kabir wanda aka fi sani da Haiman suke gudanar da aikinsu a gidan Biredin Farida Bread dake No 18 Bello Abdullahi Road unguwan Dosa dake kaduna ta arewa yayi wata tafiyar da zamu iya kiranta da TAFIYAR ƘADDARA, sakamakon yadda tafiyar ta kasance cikin gaggawa kuma ba tare da shiri ba.
Al'amarin dai ya farune yayin da Matashin tare da sauran abokan aikinsa suke ƙulla biredi a cikin gidan biredin na farida inda suke wasa da raha a tsakanin su kamar yadda suka saba.

Kawai babu zato babu tsammani sai aka ga wata irin jar iska ta ratso ta jikin ginin gidan biredin ta suri Matashin (HAIMAN) ta makashi a jikin bango inda take ya suma, sannan daga baya kuma ta ɗauke shi tayi sama da shi. Manajan gidan biredin, wanda abin ya faru a idanunsa kuma ya kasance ɗan'uwa ne ga matashin ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya bayyanawa manema labarai cewa:

''Tun da safe yake ce mana shi dai yau jikinsa na bashi cewa wani abu zai faru dashi har muna tsokanar shi da matsoraci, ashe - ashe da gaskiyar sa.

A dai dai lokacin da ake wannan jimami ne kuma labari yazo daga gidan su yarinyar da shi matashin yake so (SADIYA) cewa itama wannan jar iska tazo ta sumar da ita kuma tayi sama da ita.

Duk iya irin ƙoƙarin da ya kamata a ce jami'an tsaro sunyi, jami'an tsaron jihar Kaduna gami da na sintiri sunyi amma a banza domin kuwa ko wanda ya ji labarin su ma ba'a samu ba. Wani malamin bincike ya tabbatarwa manema labarai cewa: ''wannan al'amarin aljanune kawai,'' domin indai iskace wacce muka sani ta zahiri bata iya ɗaga mutum saboda darajar da Allah yayi masa''.

Yanzu dai kimanin kwana uku kenan da ɓacewar waɗan nan matasa amma babu wani labari dangane dasu, sannan labarai iri iri suna nan suna yaɗuwa a gari dangane da lamarin.

Abin tambayama anan shine:

WAYE YA SACE SU? ME YASA YA SACE SU KUMA ME SUKA YI MASA? A WANE HALI SUKE CIKI YANZU KUMA YAUSHE ZASU DAWO GA 'YAN UWANSU?

Zan Ci Gaba In Shaa Allaah 

_*Phone:*_
 08185819176

_*Web:*_ www.haiman.com.ng 

_*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees 

_*Twitter:*_ @HaimanRaees 

_*Instagram:*_ Haimanraees 

_*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com


🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲

♻♻ *PWA* ♻♻




Share this


Author: verified_user

0 Comments: