Friday, 8 June 2018




alkawari

Home alkawari

[10/9, 15:25] 80k: đŸŒč ALKA'WARI...đŸŒč đŸŒč {The promise } NA UMMU BASHEER PURE MOMENT OF LIFE WRITERS 💧 ( We don't just entertain and educate,we touch the heart of readers.) PAGE 1~2 ® *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* _ɯɛ É–ÆĄĆ‹'Ƨ ÆĄĆ‹Ùłáƒ§ ɛƋƧɛƙƧąıƋ Ƌɖ ɛɖƳĆąƧɛ, áƒȘƳƧ ɯɛ Ä…ÙłĆžÆĄ Ć§ÆĄĆłÄ†É§ ɖ ɧɛąƙƧ ÆĄÊ„ ƙɛąɖɛ'ƞ_ #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM *#IG PML WRITERS* #https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 #http://maryamsbello.blogspot.com Zaune yake a office ya ku're gudun A.C yana kan kujera yana buga game a waya sai juyi yake akan kujeran DOCTOR SAMEER UMAR BINA kenan matashi da'n kimanin shekara ashirin da takwas,fari ne mai dauke da siririn hanci yana 'dauke da manyan ido bakin shi da'n dai dai ne ja kamar ya shafa jambaki 24hrs,bazan iya fasalta muku shi ba Ama kyakyawa ne na kar'she, knoking akayi a kofa yace"come in" wani babban mutum ne ya shigo cikin shigar kayan likitoci dakun gan shi kun san shi ya haifi SAMEER, kalon shi yayi cikin daure fuska yace"me ka keyi har yanzu baka fara ganin patient ba?" yamutsa fuska yayi tare da cewa"yanzu zan gansu dad" cikin fada Dad ya fara magana"tun 7am kazo Ama baka ga patient ba sai yanzu wurin 11am nasan halin ka fa na rashin son aiki,dan haka ka fara ganin su yanzu kar ranka ya baci" cikin rashin damuwa da maganan Dad dan ya riga ya saba yace"ok Dad" cikin ba'cin rai Dad ya fita tare da banko k'ofan da k'arfi, bayan minti biyar wani matashin doctor ne ya shigo sa'an SAMEER, ya ka'rasa kan kujera ya zauna yace"kai fa da'n iska ne SAMEER yanzu naga Dad ranshi a ba'ce ya fitoh nan,wai kai sai yaushe zaka daina haka?" cikin ko'in kula yace"NASIR ka dameni kaje kayi aikin ka" yace"ai kai naga aikin kakeyi baka iya komi ba sai aikin buga game gaji ka k'ure gudun A.C" nan ya tashi ya rage yace"ni mura na keyi" shidai SAMEER sai buga game ya keyi har NASIR ya gama surutun shi ya fita,sanan yaga patient ya fito ya shiga motar shi mai ki'ran BMW ash colour ya figeta a guje ya nufi gida, Yana shiga gidan ya nufi wani hadada'n flat babba mai kyau yana shiga palon ya hadu da kakan shi SITTI tana hakimce akan kujera tana kalon labarai ta k'ure' idon ku kunce tana jin abin da ake cewa ne, SAMEER ne ya nufeta ya 'daura kanshi akan kafad'arta ita kuma ta shafa bayan shi tace"maigida na har ka dawo,yau ma ka tashi da wuri ko?" saida ya dau'ki minti 5 kafin yace"nifa yunwa nakeji" ya ka're maganan cike da shagwb'a ta kwalama wata mai aiki kira tace"maigida na ya dawo a shirya mai abinci yanzu" cikin ladabi mai aikin ta tashi cikin sauri dan danan ta shirya komi, ya zauna yaci ya ko'shi sanan ya nufi side di'n shi dan hutawa, flat ne da'n dai dai mai dauke da 2 bedroom da kitchen ,gaskiya ya hadu ba kadan ba, direct bedroom ya nufa ya cire kaya ya shiga toilet,wow nace dan toilet din ya hadu,saida ya zuba turaren wanka sanan yayi daya gama ya nufi wani dressing mirrow dake toilet di'n ya shafa wanan ya goga wanan,ni kuwa cewa nayi ashe maza ma na shafe shafe haka kamar mace,bakin shi kuwa saida yayi amfani da abin wankewa har kusan kala shida,dan shi kam akwai sun tsabta da gayu, bayan ya gama yaje ya kwanta sai barci, NABILA,NABILA,MAMA ce ke kwala kira,wata matashiyar budurwa ce 'Yar kimanin shekara sha tara ta fito daga cikin wani da'ki cikin shirin tafiya kyakyawa ce fara sol tana da tsawo da'n dai dai idanowan ta farare ne tass ta saka baka'r doguwan riga ta nad'a da'n kyalen shi akanta kamar balarabiya,,cikin shagwab'a da da'n guntun hawaye tace"ni dama nasan kin gaji da gani na har kin ko'sa in tafi" Mama ta jawota jikinta tace"ni na isa ince na gaji dake kawai dai naga yayanki sai jiran ki yake a waje za'ku tasha kar ku rasa mota kinsan yamma tayi" kafin tayi magana wani yaro ya shigo mai shekara goma sha biyu yace"Aunty Nabila yaya KHALIL yace kiyi sauri" Hararan yaron tayi tace"ai kai ma Hamza ka gaji da ni ko?" da sauri ya girgiza kai yace" Aa ai kina bani sweet meyasa zan so ki tafi?" ta da'n talabe mai ke'ya tace"zanyi kewar ka HAMZIZINA" ba'ta rai yayi yace"mama kin ganta ko?" Nan dai ta fita waje ta had'u da yayan'ta suka nufi tasha suka hau mota sai Kaduna. TAKU A KODA YAUSHE UMMU BASHEER✍đŸ» [10/9, 15:25] 80k: đŸŒčALK'AWARI đŸŒč đŸŒč { The promise } *NA UMMU BASHEER* ® *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (*We don't only entertain and educate,but we also touch the heart of reader's*) #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM *#IG PML WRITERS* #https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 #http://maryamsbello.blogspot.com PAGE 3~4 Fitowa yayi da shirin shi na tafiya office misalin karfe takwas ,k'wala ma wani kira yayi cikin fad'a yace"mai yasa baka wanke wancan motan ba?"tare da nuna wata hadad'iyar mota, Yace"oga kayi hakuri wancan na wanke na 'dauka da ita zaka fita" Sameer ranshi a b'ace yayita ma mutumin fad'a daga karshe ya hau wanda aka wanke haka nan, Daidai wani Restaurant mai kyau yayi parking yana son zai sai nescafe dan kullum sai ya sha to jiya ne ya k'are gashi yanzu yana ta sauri waya ya 'dauka yana magana yana kalon kasa, Nabila ce ta dauko wani tray da abinci aciki zata ajiyema wani customer jikinta sanye da kayan aikin Restaurant d'in,shi kuma dai dai ya shigo kenan kawai sai sukayi karo abincin gaba d'aya ya zube a jikin shi wayan shi ta fadi kasa ta tarwatse,ai baiyi wata wata ba ya sharara ma Nabila wani itin gigitacen mari har saida ta fad'i kasa ta saki ihu mai k'rfi tunda tazo duniya ba'a tab'a yin mata irin wanan marin ba,mutane duk suka taro a gurin dan ganin mai ke faruwa, Cikin b'acin rai ya kaleta yace"stupid,idiot " Kawai ya juya abin shi cikin b'acin rai mai tsanani ya nufi gida ya cire kayan yasa a bola dan bazai k'ara sa kayan ba,haka ya shiga bayi ya dinga wanka har sau biyar ama yana jin wari dan shi mutum ne mai son tsafta kamar zai canza halita haka ya fito da bathrobe a jikin shi ya zauna a kujeran shi yana cije lebe dan ji yake kamar ya cire fatan shi yasa wani haka kuma yake jin tsanar y'arinyan a ranshi,(ni kuwa nace sai kace wanda aka watsa ma kashi,abinci ne fa wanan wani irin mutum ne?) Nabila tunda ya tafi take zaune gurin ta kasa ko motsi ne ,kawarta ce tazo kusa da ita ta d'agota tana mai bata hakuri,kalonta kawai Nabila tayi tace"wallahi Basma bazan kyale shi ba sai na rama abin dayayi min" Sanin halinta yasa Basma cewa"Aa karki haka kiyi hakuri ki barshi kinsan fa mai kud'i ne dan nasha ganin shi yana zuwa nan siyan cofee " Tace"ni ba ruwa na da k'udin shi tunda ya iya wulak'anta mutane ,ban sani ba na bige shi ama shine zai min irin marin nan to bazan hakura ba dan duk duniya ba wanda na tsana irin shi" Bayan kwana uku da faruwar haka da yamma Sameer ya fito zai kuma Restaurant d'inan zayi siyyaya, (nace baka san dara ba kenan) Zai hau mota kenan sai ga wata mota mai kyau ta shigo gidan a guje k'idan na tashi duk ko'ina ya cika da k'ida, Wani matashi ne ya fito daga motan,,Sameer ne ya k'arasa gurin shi yana zuwa yayi baya da sauri sakamakon warin giya daya bugi hancin shi, Kallon shi yayi yace"ya SAFWAN meyasa har yanzu baza ka daina shan abin nan ba kasan cewa mahaifinka bai so sanan ran SITTI yana b'aci" Cikin maye yace"to sai me in sunga dama su kore ni a gidan " Ya bangaje Sameer ya shige side d'inshi,shi kuma girgiza kai kawai yayi aranshi cewa yake Allah ya shirye yayan na shi,ya shige mota ya fita daga gidan, Nabila kullum cikin shirin abin da zatayi ma Sameer take,Basma ta bata hakuri har ta gaji,kawai ranan har sun tashi aiki zasu gida sai ga motan shi,cikin murna taje ta dauko wani k'aton sanda ta r'ike ta bayanta tazo kusa da motan shi, Sameer kalonta yake cikin mamaki dan ya tunota ita ce ta zuba mai abinci a jiki,cikin daure fuska yace"ke mara kunya meye kike anan wurin?" Gani yayi tayi mai wani irin mugun kalo sananta daga wani sanda sama ta dage iya k'arfinta ta buga a glass din motan shi,da sauri yayi baya kad'an sakamakon yanda glass d'in ya tarwatse, Juyawa tayi tana wani irin tafiya mai d'aukar hankali ta jawo hanun Basma data saki baki da hanci tana kalon abin mamaki,janta tayi suka shiga taxi suka nufi gida, Sameer ko motsi ya kasa tsabar mamaki da hanin abin datayi mai, Wayan shi ya daga ya kira abokinshi doctor Nasir yazo ya d'auke shi, yace mai "lapiya mai ya same ka?" Cikin fad'a yace"nace kazo kawai " Toh fa Shin menene asalinsu? Ku biyo ni danjin mene ne Asalin su, *TAKU A KODA YAUSHE* *UMMU BASHEER*✍đŸ» [10/9, 15:25] 80k: đŸŒč *ALK'AWARI*đŸŒč đŸŒč *NA UMMU BASHEER* ® *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart of reader's)_ #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM *#IG PML WRITERS* #https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 #http://maryamsbello.blogspot.com PAGE 5~6 *WANAN SHAFIN SADAUKARWA NE GARE KA DADDYN FATY* SAMEER UMAR BINA,Asalin maihaifinshi wato Alhaji umar d'a ne ga DALHATU BINA ya auro y'ar k'asan Misra balarabiya ce inda shi sana'a ne ya kaishi kasan har suka fara soyyaya da k'yar iyayyenta suka yarda akayi auren inda zai dunga yawan kawota tana ziyartan iyayyenta ,suna zaune ne a Kaduna inda ta haifa mai yara maza guda biyu UMAR FARUQ DA SA'ID, sun taso cikin gata da tarbiya sunyi karatun su har sun fara aiki sai Sa'id ya fara aure matan tana da ciki akayi auren Umar inda ya auri wata y'ar uwan maman shi acan misra sunanta HALIMATUS~SADIYA,suka dawo Nigeria suka ci gaba da rayuwa lokacin da ta sami ciki lokacin ne matar Sa'id mai suna RAHINA ta haifi d'anta namiji aka sa mai suna SAFWAN yaron iyayyen sun shagwab'a shi sosai ga shi Rahina bata shiri da Halima saboda tana kishin ta fita kyau kuma ita y'ar masu k'udi ne k'iyaya ne mai tsanani a tsakani su ita ma Halima bata sonta, Ana cikin haka ne ta haifi d'a namiji aka sa mai suna SAMEER,nan fa Rahina ta fara kishi mai tsanani ganin Halima ta haifi d'a namiji,ta yanke zuwa gurin boka ,inda tayi ma Alhaji Umar ya wayi gari da tsanar Halima har ya saketa,ta shiga cikin firgici sosai gani suna zaman lafiya da mijinta,tambayan duniyan nan anyi mai yace ba komai,SITTI mahaifiyar su Umar bata ji dad'i ba,kuma Alhaji Umar yace ba inda zata mai da d'a lokacin SAMEER watan shi goma ko yaye shi ba'ayi ba hakanan aka raba uwa da d'anta, Bayan shekara goma,SITTI ita ta cigaba da rainon SAMEER alokacin ne mahaifinsu UMAR ya rasu,sun girgiza sosai da mutuwan shi, Bayan shekara Alhaji Umar da k'yar ya auri wata bazawara sunanta SAFIYA tana da y'arinya mai suna ILHAM, Rahina ta k'ara haihuwan y'a mace akasa mata suna Suhaila , ILHAM DA SUHAILA sa'oin juna ne sai dai iyayyen su mata basa shiri, Haka Hajiya Safiya ta tsani SAMEER kuma ga shi duk kansu yana musu biyaya Ama Hajiya Safiya ta cusa mai k'iyayar mahaifiyar shi a rai wai ta gudu ta barshi tun bai shekara ba,haka zai zo yayi ta kuka yana fad'ama Sitti wata rana tace ya shirya zata kaishi yaga mahaifiyar shi,haka kuwa akayi sunje ama tayi aure harda yaranta maza guda biyu,yanda Sameer yaga take taji da yaran yasa bai ji ya damu da ita ba,su kanyi waya ko in sunje kasar da Sitti yana zuwa gidan ya gaisheta Amma ba sosai ba, Haka rayuwa taci gaba Sameer yayi karatun likitanshi kasan cewar mahaifin shi likita ne sai yana aiki a hospital d'in mahaifin shi, Ama ko kad'an baya son aiki dan bai damu da mahaifinshi ba dan yana ganin mai zai sa Dad d'inshi ya saki Ummien shi(mahaifiyar shi) yana ji da kakan shi Sitti dan ita ce komi nashi,kuma halayen shi gwanin ban sha'awa matsalan shi kawai yana da miskilanci sai zuciya ga shi bai son raini yana takura ma Ilham da Suhaila dan basu da natsuwa iyayyensu mata sun sangarta su haka suke abin dasu ka ga dama Ilham kuwa club take zuwa tasha giya gasa matsatsun kaya Amma dai bata bari maza sun nemeta ba,gashi tana mutuwan son Safwan wanda bai ma san tana yi ba, Shi kuma yana da kyan shi dai dai gwargwado Amma yana shan giya ga neman mata,ga yin caca haka koda yaushe iyayyen ke fama da shi dan sun san halayanshi, *Wanan kenan* *TAKU A KODA YAUSHE* *UMMU BASHEER*✍đŸ» [10/9, 15:25] 80k: đŸŒč *ALK'WARI*đŸŒč đŸŒč *NA UMMU BASHEER* ® *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart of reader's)_ #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM *#IG PML WRITERS* #https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 #http://maryamsbello.blogspot.com *PAGE* *7~8* *NABILA USMAN IBRAHIM*shine cikaken sunanta,Asalin mahaifinta d'an Kano ne su shida ne gurin iyayyen su duk maza sai y'ar autan su mace,duk sunyi aure shine na hud'un su,yayi karatunshi dai dai gwargwado,shi principle ne a wata makaranta ya auri wata fulani mai suna Falmata su biyu ne wurin iyayyen su ita da yayar ta wanda suke kira Hajo ita ma tayi aure yaranta hud'u biyu mata biyu maza,duk gari d'aya suke zaune wato a Kano cikin wani kauye mai suna KURA, Shekaran su d'aya da aure ta haifi yaron ta namiji aka sa mai sunan kakanshi wato IBRAHIM Amma ana kiran shi da KHALIL bayan shekara shida sanan akaiyi mai k'anwa kyakyawa son kowa k'in wanda ya rasa ranar suna taci sunan kakanta na wurin Uwa wato NABILA , Nabila ta taso cikin gata da kulawar iyayye da yayanta Khalil wanda sam baya son b'acin ranta,bayan wasu shekaru aka haifi HAMZA k'anin ta, Familyn su gwanin ban sha'awa sun sami tarbiya mai kyau,Nabila akwai kokari wurin karatu Amma akwai ta da tsokana gata ba k'arfi haka zata yo tsokana Ya Khalil ke tare mata,tayi primary ta gama sanan ta shiga secondry tana j.s.s 3 babanta yace zai mata aure aiko ta dinga kuka ita bata so tana so tayi karatu ta zama likita haka ya Khalil ma yayi ta ba baban hakuri har ya hakura maman ko bata so ba dan ita tafi son y'arta tayi aure, Tana s.s 2 Alokacin ne ya Khalil yayi aure dayake a kaduna yayi University d'inshi inda wani abokin baba ya taimaka mai a gidanshi ya zauna har ya gama to ashe yana soyyaya da yarinyan abokin baban na shi to yana gama karatun akayi auren sunanta JIDDA tana mutuwan son Khalil sai da akwai ta da son kud'i Amma tana da kirki , Bayan auren ne mama ta matsa da cewan ita fa sai Nabila tayi aure,aiko da baban da Nabila da Khalil suka taru suka fara bata hak'uri Nabila tace"Mama baki so ne in zama likita in dinga kula da lafiyar ki?" tace"ina so Amma nafi son inga kinyi aure" To da kyar ta yarda,inda Khalil ya rok'e su akan cewa su bashi ita zai tafi da ita ta k'arasa karatun ta a Kaduna,haka akayi kuwa ta shirya tabi shi sai murna take, Aunty Jidda akwai son mutane taji dad'in zuwan Nabila,kusa da gidan akwai wata yarinya Basma anan suka k'ula k'awance da Nabila suna son juna kamar y'an uwa haka suke islamiyar su d'aya haka makaranta ma kwana kawai ke raba su inkun ga Nabila to zaku ga Basma, Ganin yanda abubuwa suka taru suka ma yayanta yawaga Aunty Jidda da tsohon ciki ,yasa Nabila tayi tunani gara ta nemi wani aikn tana taimaka musu,shine ta gayama yayanta yace bazai yuwu tayi wani aiki ba da k'yar ya yarda ya nemo musu aiki a wani Restaurant ita da Basma, Ahaka dai suka fara aikin,Nabila a rayuwarta akwai ta da son girki shiyasa ta dage tana koya sosai gurin Aunty Jidda da yake ita ma ta abin da ta karanta kenan haka kuwa ya Khalil duk da bai da kud'i haka nan yake siyo abubuwa suna girki masu dad'i, Tsakanin Nabila da ya Khalil akwai shak'uwa mai k'arfi yana ji da ita ko me take so indai yana da hali zaiyi mata,haka ita ma bata son abin da zai b'ata mai rai ko kad'an,yanzu haka suna shirin yin jarabarwar fita secondry ne ,a wanan lokacin ne ta had'u da SAMEER. *CIGABAN LABARI* Suna tafe cikin mota bayan Nasir ya d'auko shi, Nasir ne ya kale shi yaga yanda fuskan shi yayi ja tsabar b'acin rai yace"wai ni meya faru da kai ne?" Ko kula shi baiyi ba ya k'ara cewa"ko Accident kayi ne cux naga glass d'in motan ka ya fashe?" Cikin gajiya da tambayan Nasir yace"kai meyasa ka cika surutu ne,haba ka sani gaba sai tambayoyi kake min kaman d'an jarida" Yace"to kai kafi son inyi shiru insa maka ido kenan?" Sai bayan 5 minute kamar ba zai ce komi ba yace"wata aljanar yarinya ce ta fasa min mota" Cikin mamaki yace"aljana kuma?" Can ya saki dariya yace"wata yarinya ce haka mara tsoro,zan so inganta" Sameer ya kaimai naushin wasa yace"kai fa banza ne" Haka Nasir yayi tayin mai dariya, da Sameer yaga abin nashi iskanci ne yace"sauke ni anan d'an iska kawai" Yace"wallahi sai na kai ka har gaban Sitti na gaya mata abin daya faru" Da yaga dai bazai daina ba kawai sai yasa earpiece a kunne yana buga game, muje zuwa masu karatu, *TAKU A KODA YAUSHE* *UMMU BASHEER*✍đŸ» [10/9, 15:25] 80k: đŸŒč *ALK'AWARI*đŸŒč đŸŒč {The promise} *NA* *UMMU BASHEER* ® *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart of reader's)_ #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM *#IG PML WRITERS* #https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 #http://maryamsbello.blogspot.com *PAGE* *9~10* Tana zaune tana ta faman karatu dan saura sati d'aya su fara jarabawa ,data gama ta fito parlour Aunty Jidda na zaune tana yanke farce,tace"Aunty naji Basma yau shiru bari inje in duba ko lafiya" Tace"toh ki gaida maman ta kice wai yaushe zan kawo barkono ayi min yaji" Tace"toh Aunty" Tana shiga ta tarar da maman Basma tana tankad'e a tsakar gida,ta gaishe ta fad'a mata sak'on Aunty sanan tace"Mama ina Basma naji ta shiru?" Tace"kinsan ta sarkin barci tana can tanayi sai kace kasa" Tace"koma fa ta san zamuyi karatu shine take ta barci" Tace"shiga tana cikin d'aki" Tana shiga ta ganta ta bararaje sai munshari take,aiko ta dage ta d'aka mata duka,afirgice ta tashi tana cewa"wayoo mama Aljani" Nabila ta tuntsire da dariya tace"yanzu Aljanin ya fita da gudu" Basma ta kai mata duka tace"dan wulak'anci haka ake tashin mutum barci" Tace"ai wallahi maganin ki kenan,yanzu dai ki tashi muje mu fara karatu sai dai kuma inbaki so ki zama doctor ne dan ni kinsan ba wasa" Nan dai suka d'an tab'a fira sanan sukayi karatu, ******* ********* Yana zaune kan kujera kamar koda yaushe yana aikin buga gama, Bud'e kofa akayi aka shigo,har ya d'ago zai fara masifa dan bai san damuwa kwana biyu bai jin dad'i sai yaga ashe Dad ne, Dad yace"kai sai yaushe zaka canza hali ne,aiki kazo ko hutawa?" Shiru yayi bai ce komi ba,cikin jin haushi Dad yace "ka fara duba patient yanzu sanan akwai wani theater daza muyi anjima" Zai fita kenan da sauri Sameer yace"Dad bana jin dad'i " Ba tare da ya juyo ba Yace"haka nan za muyi aikin" ya fita, Takaici duk ya cika Sameer wannan wani irin mahaifi ne haka, Sai around 7:00pm sanan Sameer ya koma gida tsabar bak'in cikin dayake ciki kawai sai ya wuce wurin Sitti yana zuwa ya tarar ta idar da sallan magariba tana zaune kan praying mat yaje kusa da ita ya d'aura kan shi a cinyar ta,murmushi tayi tace"Sameer akwai ka da san jiki fa kamar mage" Shiru yayi jin yayi shiru bai ce komi ba ta tab'e shi da sauri ta cire hanunta jin yanda jikin shi yayi zafi kamar wuta tace"Sameer meya sameka baka da lafiya ne?" Girgiza mata kai yayi yana cewa"Sitti ke kad'ai kika damu da halin dana ke ciki,meyasa Dad baya ganewa, meyasa iyayyena basa sona,laifin me nayi musu,ita Ummie ta manta dani,mijinta kawai da yaranta take so,shi kuma Dad Aiki kawai yasa agaban shi gaba d'aya bai damu da halin da nake ciki ba" Wasu hawaye ne masu zafin gaske yake zubarwa , Cike da tausayawa tace"Sameer na kar kace haka iyayyen ka na sonka,shin ko ka tab'a ganin inda Uwa tak'i d'anta ne?" Yace"Amma ni basa sona ko menayi musu?" Ahaka dai tayi tayin mai kalaman kwantar da hankali har ya d'an sake yaci abinci yasha magani ita da kanta ta raka shi side d'in shi , Dai dai zata wuce ta side d'in Safwan (daya ke flat d'insu d'aya da Sameer sai dai kowa da bangaren shi) Safwan ta gani cikin maye yana tafe yana layi ya shige side d'in shi tare da bugo k'ofa da k'arfi, Ran Sitti ya b'aci sosai ya zama dole ta d'au mataki, ******* ********* Nabila sunyi jarabawar su lafiya inda suke jiran sakamako, Bayan kwana uku tace ma ya Khalil tana son taje hutu gida yace ta shirya zau kai ta Amma fa kar ta jima in ba haka ba sai mama ta matsa da ayi mata aure aiko Nabila taji tsoro tace sati d'aya zatayi ta dawo,yace ai gara,Aunty Jidda tace"am going to miss u Nabila" Itama tace"me too i will miss u " Ahaka dai suka tafi kwanan ya Khalil d'aya ya koma ya bar Nabila anan, Bayan kwana biyu ta shirya taje gidan kakanta,tana shiga tace"ina tsohuwa mai ran karfe" Fitowa tayi daga cikin d'aki tana cewa muryan wa nake ji kamar takwarata" Tace"eh nice kin k'i ki mutu muci gumba" Cikin wasa tace"sai kin fara mutuwa" Tace"to ni ba yanzu ba,wai naji gidan ya cika da k'amshi ne" Tace"to sarkin k'wadayi,dambu ne" Da murna tace"dama na kwana biyu ban ci ba" Ranar sun sha fira da yamma ta fara shirin tafiya Kaka tace"wai ke sai yaushe zaki fito da miji kiyi aure ko sai na bada ke sadaka" Ta b'ata rai tace"Allah ya sauwak'e a ba dani sadaka" Tace "duk sa'oin ki sunyi aure harda yara Amma ke ba ko tsayaye" Tace"to ni ina ruwana dasu nifa sai na zama likita zanyi aure ehe" Tace"baki isa ba kam" Ahaka dai ta tafi gida , Washegari da safe taji maman ta fara maganar aure habawa ai sai ta kira ya Khalil yazo ya d'auketa, Haka akayi kuwa Ya Khalil ya dunga rok'un mama har ta hak'ura ta barsu suka koma tare, *TAKU A KO DA YAUSHE* *UMMU BASHEER*✍đŸ» [10/9, 15:25] 80k: đŸŒč *ALK'AWARI*đŸŒč đŸŒč {The promise} *NA* *UMMU BASHEER* ® *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart of reader's)_ #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM *#IG PML WRITERS* #https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 #http://maryamsbello.blogspot.com *PAGE* *13*~ *14* Batare da b'ata lokaci ba aka shiga da ita Emergency Dad ne ya shiga duba lafiyarta, Ya khalil da ke ta faman zagaye guri sai addu'a yakeyi ya d'auki waya ya kira Nabila alokacin ita kuma ta tashi daga gurin aiki kenan,ya gaya mata abin daya faru ba tare da b'ata lokaci ba ta zo Hospital d'in shigowan ta keda wuya sai ga su Sameer dasu Sitti,ko kalon shi batayi ba ta nufi gurin ya Khalil cikin tashin hankali, Sitti na zuwa ta d'aga hannu ta mari Safwan,da sauri Sameer ya rik'eta yana bata hakuri,ina ai sai fad'a take ma Safwan ta juyo ta kali mami(mommyn Safwan) Tace"duk ke kika b'ata ma yaron nan tarbiyya " Tace"kiyi hakuri Ummie"(duk haka iyayyen ke kiranta su kuma yaran su kira ta da Sitti wato kaka) Sai alokacin Nabila ta kale su cikin mamaki ta nuna Sameer tace"Kai ne?" Ya d'aure fuska yace"me kike anan mara kunya?" Khalil yace"kin san shi ne?" Kafin tayi magana sai ga Dad sun fito,Ya Khalil ya nufe shi yana tambayan lafiyan matan shi, Dad yace ba wani matsala kuma cikin ba abin daya same shi sai dai tana buk'atar hutu sanan tayi targad'e a k'afa,nan Khalil yayi hamdala,Dad ya nufi gurinsu yana tambayan mai ke faruwa nan Police d'in yayi musu bayani,ya Khalil yace kuma bai yarda ba sai an kule shi sakamakon tuk'in gangancin daya keyi,nan Sitti ta bashi hak'uri Amma yace shi bai yarda ba aiko nan suka fara fad'a da ya Khalil da Sameer dan Sameer na son d'an 'uwanshi,Nabila ce taja hanun ya Khalil sukaje gefe tace"Ya Khalil dan Allah kayi hakuri mu tausaya ma kakansu tunda tace kayi hak'uri ni agaskiya ta bani tausayi tunda kaga Aunty ance da sauki jikinta kuma mu bamu da kud'in daza muja dasu koh yaya?" Yace"eh kinyi gaskiya wancan ne ya ban haushi"ya nuna Sameer, Yace" Amma ba komi shikenan" Taje gurinsu tare da cewa"kuyi hakuri da abin da yayana ya fad'a kuma wannan abin daya faru k'adara ce dan haka mu dai mun yafe" Sunji dad'i da kalaman yarinyan Amma ban da Sameer dake zabga mata harara,nan dai ta wuce d'akin da aka kwantar da Aunty jidda,su kuma sauran suka tafi gida, Sitti ta nufi d'akin tace ma Nabila"Yarinya ina miki godiya sannan ina k'ara baku hak'urin abin da yafaru " Tace"Aa wallahi ba komi dama haka Allah ya rubuta sai abin yafaru" Sitti taji wani irin dad'i a ranta tace"ya sunan ki?" Tace"sunana Nabila" Nan take taji son yarinyan ya shigeta,can sai ga Sameer ya shigo ya kali Sitti yace"mu tafi inkai ki gida dare yayi" Tace"Aa ba inda zani saina ga ta tashi tukun naji ba abin dake damunta" Ya b'ata rai yace"oh please Sitti ki bari da safe sai ki dawo kinga garin akwai sanyi" Tace"toh shikenan muje" Nabila ce ta cire rigan sanyin dake jikinta ta d'aura ma Sitti ajikinta tace"Sai da safe" Sitti ta mik'a mata rigan tace"ki barshi ai ke kike buk'atanshi saboda sanyi ni kinga gida zani yanzu" Girgiza kai tayi tace"Aa ki tafi dashi kawai" Anan sukayi salama Sitri tayi gaba,Sameer dake kalon duk abin dasu keyi ya tab'e baki yace"karki tunanin ganin na kyale kine na abin da kikayi min,kuma wanan d'an iskan yayan naki sai na koya mai hankali" Cab babbar magana antab'o mata yayanta tace"wallahi yayana ba d'an iska bane" Yace"I don't have your time"yayi tsaki ya juya ya tafi abinshi, Haushi duk ya cikata,bayan minti goma da tafiyan su Khalil ya dawo d'auke da abinci wanda maman Basma ta bashi ya kawo musu,Nabila ta tashi ta karb'a yace"har yanzu bata tashi ba?" Tace"eh har yanzu,Amma yaya ya kamata a kira su baba afad'a musu koh" Yace"Aa insun san tana hospital hankalinsu zai tashi bari sai an salame mu tukun" Tace"toh ya Khalil " Missalin 11:00pm Aunty jidda ta farka da sauri suka k'ariso kusa da ita sunna mata sanu ,ta tambaye su meyasame ta ya Khalil ya fad'a mata meya faru, ******* ********* Washegari Sitti tasa masu aiki suka shirya abinci tasa driver ya kai ta hospital d'in ,lokacin da ta shiga d'akin ta tarar da Jidda a zaune tana shan magani,anan dai suka gaisa tayi mata ya jiki,Nabila ma ta gaishe ta sanan tace ance ta kira doctor in drip d'in da akasa ma Aunty jidda ya k'are ,nan ta fita tana neman office d'in ance offici d'in *Doctor Sameer Umar Bina*nan taga office d'in ta nufa tare da tura k'ofan..... *TKU A KO DA YAUSHE* *UMMU BASHEER*✍đŸ» [10/9, 15:25] 80k: đŸŒč *ALK'AWARI*đŸŒč đŸŒč {The promise} *NA* *UMMU BASHEER* ® *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart of reader's)_ #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM *#IG PML WRITERS* #https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 #http://maryamsbello.blogspot.com *PAGE* *11*~ *12* *WANAN SHAFIN NA SADAUKAR DA SHINE GABA D'AYAN SHI GAREKU Y'AN PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* Mommy sultan Mommy musadiq MSB Mmn khadija Aunty Khady Mmn Shureim Sadnaf 4real Shukrah cute Sweery Jannart Lubabat Isma'il Sadnas Seemaluv Eshat Asym Samrah *Kai a gaskiya idan na tsaya lissafo sunayyen ku zamu k'arar da shafin anan Amm ko sani ina k'aunar ku,* *Allah ya k'ara muku basira da zak'in hanu Allah ya raba ku da sharin mak'iya da mahassada* *Ni ummu basheer mai k'aunar ku ce Allah ya bar zumunci Ameen* Kasan cewar week end ne hakan yasa shi fitowa waje gurin motoci ya zauna yana shan iska, Wasu kyawawan y'an mata na gani su biyu sunci kwaliya fuska tasha fente fente d'inkin nan d'an figil baza kuce y'ayan musulmai bane dan ko kyale basu saka ba,Ilham da Suhaila kenan,dai dai zasu wuce shi ya daka musu wata tsawa mai rikitarwa Suhaila sarkin tsoro tuni ta k'ame guri d'aya,kalon su yakeyi yace"are u stupid ba kwa gani nane zaku wuce ba gaisuwa wai ina ma zaku at this time da magriba ya kusa?" Ilham ce tayi k'arfin halin cewa"friend nane take birthday shine za muje" Cikin takaici yace"da wannan irin dress d'in sannan at this time zaku fita?" Ilham cikin rashin kunya tace"to ai naga mom ta sani ita ta ban izini" Mik'ewa yayi ya daka musu tsawaya yace"ba inda za kuje stupid kawai mara kunya" Ai ba shiri suka shige cikin gidan Ilham ta nufi gurin mom dake zaune ta haye jikinta cikin shagwab'a tace"mom wlh ya Sameer ya hana mu fita har yana zagin mu" Gyara zama tayi ta hau masifa tana zagin Sameer tace"wato shi issashe ko aiko zai had'u dani,dan haka tashi ki tafi abinki ,kuma mai ya had'a ki da yarinyan can ban ce ki fita harkan Suhaila ba kinsan dai ba shiri muke da Uwarta ba dan bata da mutunci" Tace"mom nifa jinina ya had'u da Suhaila ina sonta" Hararanta tayi tace"saboda kina son yayanta ba wlh ki kiyayeni gara ki cire shi a zuciyanki" Bata k'ara cewa komi ba ta fita ta had'u da Suhaila dake lab'e tana son shiga parlour su Amma tsoro take dan bata fad'i inda zata je ba,Ilham ce ta kira ta su tafi tace ita bazata ba, Tace"wai meyasa kin cika tsoro da Allah mu tafi" Ta ja hanunta suka fita suka shiga mota suka bar gidan kasancewar Sameer ya shiga masalaci, B'angaren su Nabila kuwa jarabawar su ya fito kuma sunci sunyi murna sosai inda Ya Khalil ya dage duk da bai da kud'i ya shirya musu y'ar walima a gida,Nabila taji dad'i ba kad'an ba, ****** ******** Aunty Jidda ce ta dage sai Ya Khalil yazo sun d'an fita shan iska,(ni kuwa nace wa yaga baturiya) Da yake yana da machine kawai sai ya goya ta suka tafi bayan sun fito daga wani gidan zoo ne machine d'in ya samu matsala gashi unguwan masu kud'i ne ba wurin gyara kusa suna bakin titi sun rasa yaza suyi sai Aunty Jidda tace bari taga ko zasu samu wani mai mota ya taimaka musu, Safwan dawowan shi daga Club kenan yasha giya ya bugu sai tuk'in ganganci yakeyi bai kalon gaban shi da kyau, Dai dai da Aunty Jidda ta hau gefen titi,aikuwa da gudu ya kwasheta da mota ji kuke kiiiiiyyyyyyyyy Ya Khalil cikin razana yayi kanta ganin an buge mishi mata,sai jijigata yakeyi yana kuka wiwi Amma ko motsi batayi, Safwan ne ya fito yana tangad'i yana bala'i yana cewa"ku wasu irin dabobi ne wai i...ina...ta...muku. ..horn ba kwaji...ne"ya k'are maganan cikin maye, Ya Khalil ne ya cakumo shi yace"wlh in mata ta wani abu ya sameta kotu ce zata raba mu" kan kuce me sai ga mutane sun cika gurin wani mutumi police yasa Safwan a mota tare da su Ya Khalil suka nufi Hospital. *muje zuwa masu karatu* *TAKU A KO DA YAUSHE* *UMMU BASHEER*✍đŸ» [10/9, 15:25] 80k: đŸŒč *ALK'AWARI*đŸŒč đŸŒč {The promise} *NA* *UMMU BASHEER* ® *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart of reader's)_ #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM *#IG PML WRITERS* #https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 #http://maryamsbello.blogspot.com *PAGE* *15*~ *16* Tura k'ofan tayi ta shiga yana zaune a kujera yana sana'an nashi wato game yana sanye da kayan doctors,jin an shigo ba tare da sanin shi ba yasa ya d'ago kai,ido biyu sukayi bai ce komi ba yaci gaba da abin daya keyi,kalon shi tayi aranta tace ashe dai doctor ne Amma ya cika miskilanci kaman bai san dazuwa na ba,k'arasawa tayi ta zauna kujeran dake fuskantar shi tace"drip d'in da akasa ya k'are" Bai d'ago ba haka kuma baiyi magana ahaka sai da suka d'auki 5 minute cikin haushi ta k'ara maimaita mai, Tsawa ya daka mata yace"get out from my office" Duk da taji tsoro sai da tace"to ina ma magana ka share ni" Yatsina fuska yayi yace"kin cika surutu please jeki zan zo" Sai da ta maka mai harara sanan ta fita, Sitti kusan wuni tayi a hospital d'in sanan ta tafi Sameer da kanshi ya mai data gida, Su Basma da mamanta sun zo,nan Nabila ke fad'a ma Basma abin daya faru tsakanin ta da Sameer,Basma tace"Amma yayanshi bai kyauta ba kuma ke ki rage tsokana dai dani babu ruwana" Hararanta tayi tace"sanu mama sai ki sa indaina" Suna zaune suna firan su a waje sai ga Sameer da Nasir zasu wuce,Nasir ne ya hangosu ya tab'o Sameer yace"friend ko ka hango wasu y'anmata?" ya nuna mishi su Nabila da hannu, Tsaki Sameer yaja yace"toh sai me,kai na lura y'anmata ke gaban ka" Dariya yayi yace"wallahi dole inso su dan ni yanzu aure nake so inyi" Zai je gurin Sameer ya jawo shi yana cewa"haba zaka zubar ma da kanka mutunci wancan cikakiyar mara kunya ce" Fuskan shi d'auke da mamaki yace"kasan su ne?" Nan ya fad'a mai ai itace wace ta fasa mai glass d'in mota,habawa mai Nasir zaiyi inba dariya ba yace"Amma fa ta burgeni yanda akasa mi wanda tayi maganin ka" Sameer bai kula shi ba dan yasan fad'a kawai za suyi inya kula, Washegari haka Sitti tace su mami sai sun shirya sunje hospital,ba yanda zasuyi haka nan suka tafi,Amma suna gaisheta suka tafi Sitti ce ta d'an zauna,Sameer ne ya shigo d'akin zaiyi ma jidda allura gashi bata so Nabila ce tace ta juya karta kala yanda za'ayi mata,ita ma Nabila bata so lokacin daya soka ma jidda allura sai da Nabila tayi d'an k'ara,wani dogon tsaki yaja ya fita, Jidda gabaki d'aya ta gama lura da cewa wanda suka bugeta masu kud'i ne ,habawa gata dama da son kud'i ai nan ta fara sak'e sak'en wani abu aranta,sannan ta lura su mama basu san bata da lafiya ba aiko nan ta d'auki wayan Nabila dake gurin,dayake d'akin ba kowa sai ta kira mama a waya ta gaya mata abin daya sameta,hankalin mama ya tashi sosai suna cikin wayan ne saiga Sitti ta shigo,tayi murmushi tace"kinji sauk'i kenan gashi kina waya" Tace"eh maman Nabila ce muke waya da ita" Nan Sitti tace ta bata waya su gaisa haka akayi kuwa sun gaisa cikin mutunci har Sitti ta k'ara bata hakuri,mama tace ai ba komi k'adara ne tace zata zo gobe,nan sukayi salama, Ta mik'a ma jidda wayan sanan ta fito driver ya mai data gida kasancewar Sameer aiki ya mai yawa, Sameer ne yana tafe yana waya yana duba patient dai dai zai shigo d'akin da aka kwantar da Jidda ,a wannan lokacin kuma Nabila ta dauko ruwa a bokiti ta watsa shi ta bakin k'ofa habawa ai sai a jikin Sameer ji kuke shaaaaa,k'arasa shigowa ciki yayi tsananin b'acin rai fuskar shi tayi jajawur abinku da farin mutum , Dago kan da Nabila zatayi wazata gani Sameer ne duk ya jik'e da ruwan data watsa.... *Toh fah ya kenan zata kasance a tsakanin su ku biyo ni dan jin mai zai faru* *TAKU A KO DA YAUSHE* *UMMU BASHEER*✍đŸ» [10/9, 15:25] 80k: đŸŒč *ALK'AWARI*đŸŒč đŸŒč {The promise} *NA* *UMMU BASHEER* ® *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart of reader's)_ #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM *#IG PML WRITERS* #https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 #http://maryamsbello.blogspot.com *PAGE* *17*~ *18* *DEDICATED TO SAMRA* *Ina taya ki murnan zagayowan ranar haihuwan ki ,wannan shafin naki ne* *HAPPY BIRTHDAY SAMRA*🎂 *Ina rok'on Allah ya bama jannart lafiya Ameen* K'arasawa yayi har gaban ta ya d'aga ya d'aga hannu ya sharara mata mari,ihu tayi saboda marin ya shigeta sai data ga gilmawar taurari, Jidda dake barci sai da ihun ya tasheta ta shiga tambayan ko lafiya, Ranshi ya b'aci sosai har fuskan shi yayi jajawur,kallonta yayi ya daka mata tsawa yace"wannan yazama last warning dazan miki akan k'ara yin min wani abu"azuciye ya fita daga d'akin, Tace"ban yafe mugu kawai" ni kuwa nace wannan shine ihu bayan hari, Shiga office d'in shi yayi sai yaga Dr Nasir na jiran shi,da sauri Nasir ya mik'e yana tambayan shi meya sameshi,ranshi ya b'aci ba kad'an ba ya fad'amai abin daya faru,Nasir k'unshi dariyan shi yayi a ciki ya fara ba shi hakuri ,Sameer dan bak'in ciki kamar yayi kuka, A ranar ne su mama suka zo Nabila sai murna take Amma data tuno da mari da Sameer yayi mata sai taji bak'in ciki, Sitti ce da Mama suna fira dan lokaci d'aya jinin su ya had'u,Sitti tace"ina son Nabila kamar abani ita" Mama tace"ai Nabila taki ce ni yanzu buri na d'aya inga ta sami miji nagari tayi aure karatun ya isa haka" Murmushi Sitti tayi sannan tace"Aure ai nufi ne na Allah zatayi in lokaci yayi Amma ni daza ki bani Nabila ai zanyi mata miji" Mama ta gyara zama tace"da gaske kike" Tace"kwarai kuwa nayi mata miji jikana ne in har kin amince sai iyayye maza su shigo cikin maganan" Cikin murna Mama tace"Agaskiya ban sa ko suwaye ba Amma ina ganin ku mutane ne nagari kuma har cikin rai na,na amince ni nabaki Nabila kuma nasan babanta bazai k'i ba" Sitti ta rik'o hannun Mama cikin murna tace"ban san da wani baki zan miki godiya ba Amma naji dad'i sosai kuma insha Allah Nabila ta samu miji" Nan sukayi ta fira cikin farin ciki,Jidda data barcin k'arya duk tana jinsu murna kamar ya kashe ta,tunda Nabila zata auri yaron masu kud'i ai su sun warke daga rashi dan duk wani abu na kud'i da ake kashewa duk dad ne ya d'auke musu komai ko sisi basu kashe ba , Lokacin da Sitti ta koma gida ta kira Dad da Daddyn Safwan ta gaya musu ta samo ma Safwan mata kuma tasan Nabila akwai tarbiya tayuwo ta dalilin Nabila ya shiryu ya bar halayyen daya keyi, Suma sunji dad'i dan auren shine mafita,Annan tace su shirya suje kauyensu Nabila su nemo aurenta,suka Amsa mata da za suje, ******** ******** Haka Rayuwa taci gaba Jidda taji sauk'i har ansalameta Nabila tun ranar data sha mari bata k'ara shiga harkan Sameer ba ,su Dad sunje sun nemarwa Safwan auren Nabila ,baban ta kuma yayi bincike ya gano daga gidan mutunci ne dan haka shi da yayyan shi sun amince har ansa rana wata d'aya ,sai lokacin Ya Khalil ya sani kwata kwata bai so ba Amma ba yanda zaiyi shiyafi son tayi karatu,duk budirin nan da akeyi ba wanda ya sani bayan su, Ya Khalil ya kai Nabila gida nan babanta ke fad'a mata aikuwa tayi kuka kamar ranta zai fita ita wallahi bata son aure karatu zatayi sai da Mama tayi mata fad'a sosai tace indai bata yarda tayi aure ba to bata ba ita,to shine fa ta hak'ura ta yarda,sannan ta koma gidan ya Khalil sai ana saura sati biyu biki zata dawo, ******* ******** Sitti ta tara meeting gaba d'aya kowa ya hallara a babban parlour na gidan, Sai da aka bude taro da addu'a sannan Sitti tace"na tara ku annan ne domin sanar da ku wani abin farin ciki,Safwan nayi maka mata kuma har ansa ranar aure kuma yarinyan nan ne wanda ka buge matar yayanta" A razane kowa ke kallonta maganar yazo musu wani iri,Safwan ya mik'e cikin zafi jikinshi har rawa yake tsabar bak'in cikin dayake ciki yace"Sitti kin san me kike cewa kuwa,aure fa sai kace k'aramin yaro ni za'ayi ma aure to wallahi ba'a isa ba" Daddyn shine ya daka mai tsawa yace"kai mahaifiyar namu kake fad'a ma haka ko yau ma a buge kake,gayamin giya kasha ko wiwi?"cikin fad'a yake magana dad ne ke bashi hak'uri, Sameer ko azuciyan shi cewa yake"hmm akwai matsala wanan yarinyan mara kunya ya Safwan zai aura" Ilham kamar ta kwala ihu takeji tsabar bak'in ciki zatayi magana kenan da sauri mom ta hana ta, Mami ko taji haushi meya Sitti ke musu haka ya za'ayi d'an ta ya auri talaka, Haka Safwan ya dage musu shi bai son auren sai da daddyn shi ya mare shi ya kore shi a parlour, *Toh fa akai cakwakiya a gaba muje zuwa zan warware muku komai* *TAKU A KODA YAUSHE* *UMMU BASHEER*✍đŸ» [10/9, 15:25] 80k: đŸŒč *ALK'AWARI*đŸŒč đŸŒč {The promise} *NA* *UMMU BASHEER* ® *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart of reader's)_ #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM *#IG PML WRITERS* #https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 #http://maryamsbello.blogspot.com *PAGE* *21*~ *22* *Wannan shafin gabaki d'ayan shi na sadaukar da shine gare ku masoyya litafin Alk'awari* *Nabila*gida ta shiga domin ta sanar da Aunty Jidda ko data fad'a mata cewa tayi ta shirya Amma tace ita bazata je ba da kyar ta yarda zata je ba dan ta so ba sai dan ba yanda ta iya da Aunty jidda,wani had'ad'an material orange colour doguwar riga ne tasa ta d'aura d'an kwalin tasa fashion d'in sark'a sannan ta d'auko gyale ta yafa, flat shoe tasa ,light make up tayi daga nan tayi ma Aunty jidda salama ta fita ,bayan mota ta shiga inda Safwan yake zaune shi kuma Sameer na driving suna tafe su d'an tab'a fira da Safwan ,inta had'a ido da Sameer ta madubi sai ya galla mata harara har suka isa wani had'adan Restaurant sun d'an ci abubuwa daga nan suka biya wani Park,kai ranar sun zaga gari inda Safwan yake ta shishige mata har sun d'an saba Sameer kamar ya kwarma ihu tsabar gajiya aran shi cewa yake wato shi yazama driver kenan bai cin dai yaya Safwan ne da waye ya isa yayi mai haka, Sun kawota gida Safwan yayi mata siyayya sosai sai nuna mata yake shi d'in ai mai kud'i ne ,Safwan yace Sameer ya kwashe kayan ya shiga mata da shi kamar zai gayama yayan magana sai kuma ya fasa ya kwashi kayan ya kai ciki, Dai dai zai fito ita kuma zata shiga wani hararan ya k'ara mata, Cikin takaici tace"Ka kula fa dan yanzu ni matar yayan kane dolle kace min Aunty" Murmushin rainin hankali yayi yace"akwai ki dasan girma waye zai ce miki Aunty" Gwalo tayi mai tace"hoo dole dai ka kira ni da Aunty Nabila" Kafin taxi magana ta ruga cikin gida aguje dan tasan zai iya marin ta, Juyawa yayi aran shi cewa yake ita yarinyan nan ga tsoro ga tsokana,yana zuwa yaja motar suka bar unguwan, Safwan yau yaje Clup sunyi caca shida wani mutum inda Safwan ya cinye cacar gashi kud'i mai yawa mutumin yasa haushi kamar zai kashe shi har fad'a sukayi da Safwan shifa bai yarda aci shi bane da kyar aka raba su Amma ya d'au *ALK'WARI* sai ya rama bazai bar Safwan haka ba dayake shima mai kud'i ne sosai,nace Allah ka shirya mana musulmai baki d'aya, Acikin sati biyu Safwan da Nabila suka saba,ita dai bata jin son shi aranta Amma yanzu ta hak'ura zata aure shi tayi mai biyayya, Ankai lefe akwati set biyu masu shegen kyau anzuba dukiya aciki harda kyautan mota aka bata ita kanta dataji irin dukiyan da aka zuba sai data tsorata, Ilham kamar zatai hauka dan bak'in ciki ,kasa zama tayi agidan ta tafi gidan k'anwar mom sai bayan biki zata dawo, Sitti kyautar wani Company ta bama Nabila da tana son ta har cikin ranta,da farko iyayyen Nabila sunk'i yarda da kyautan sai da Sitti tayi ta rok'ansu suka Amince sukayi mata godiya sosai, B'angaren surikan Sitti wato Mom da Mami sunyi bak'in cikin wannan kyautan Annan mom ta bama Mami shawaran in anyi auren tasa Safwan ya k'wace,Mami kam ta amince harsuka shirya da Mom tunda ta bata shawara, Nabila ita da Basma sukayi rabon kati inda Safwan ya aiko musu da driver ya kai su, Washegari su Aunty jidda tare da Basma suka tafi k'auye sai bayan biki zasu dawo, Tunda Nabila ta dawo k'auyensu kullum sai anbata magunguna tasha wanda bata san ma na mene ne ba mama ta dage sai gyara y'arta takeyi ,akoda yaushe suna waya da Safwan, Biki ya rage saura sati d'aya yanzu,nan aka farama amarya lalle akaje saloon mussaman aka d'auko wata make over ita zata dinga mata kwaliyya har agama bikin, Ranar thursday akayi Mothers Day acikin gari aka kama wani had'ad'an Hall Kar kuso kuga yanda amarya Nabila tayi kyau kamar asaceta agudu tsabar kyau, Ranar Friday akayi Arabian Night inda akasa kid'an larabawa sannan akayi shigansu,Amarya lemon green d'in abaya akasa mata aka nad'a mata gyalen,tayi kyau sosai kuma mutane sun taro ina gefe rik'e da litafina da biro sai na hango wata mota mai kyau guda biyu sun iso gurin ko kunsan suwaye? y'an *Pure Moment of Life Writers*ne sunyi kyau cikin shigansu na Arabian gown,da sauri na nufesu aka shiga gaisawa, Taro yayi anwatse lafiya. *Taku a ko da yaushe* *UMMU BASHEER*✍đŸ» [10/9, 15:25] 80k: đŸŒč *ALK'AWARI*đŸŒč đŸŒč {The promise} *NA* *UMMU BASHEER* ® *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart of reader's)_ #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM *#IG PML WRITERS* #https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 #http://maryamsbello.blogspot.com *PAGE* *19*~ *20* Safwan fita yayi daga gidan gaba daya ranshi ya gama b'aci kamar shi ace za'ayi mai aure aiko bazai yuwo ba,direct club ya nufa ya sha giya ya bugu sosai bai dawo gida ba sai cikin dare, Ilahm suna shiga d'aki tasa ma mom kuka ita wallahi ya Safwan take so da kyar mom ta shawo kanta ta hakura tace bayan auren zata san yanda za'ayi ta auri Safwan,mom ta yarda ne kawai saboda kud'i tunda tasan familyn akwai dukiya, Da safe Sameer yayi shirin tafiya office sai ya shiga ya gaida Sitti nan take cemai ya shawo kan Safwan yaje ya ga Nabila su fahimci juna, Yace zaiyi k'ok'ari yayi mai magana, Bayan ya dawo aiki da daddare yaje ya sami Safwan yayi mai magana da farko fad'a sukayi sai daga baya dayake yana d'an son Sameer d'in sai ya amince Amma da sharad'in zai dinga raka shi,duk da Sameer bai so baran ma dai basa shiri da ita hakanan ya amince ko dan Sitti taji dad'in Safwan yaje, Nabila na kwance kan gadon ta tayi zurfi a tunani,Basma data shigo d'akin sai magana take mata Amma shiru sai data tab'ata tayi firgigit ta dawo hayacinta, Basma tace"dan Allah ki cire damuwa aranki karki sama kanki wani ciwon na daban" Ta share hawayen daya zubo mata tace"baza ki fahimci meke damuna ba wallahi ni kad'ai nasani" Cike da tausayin k'awar nata tace"nasan abin da kike ji Amma kiyi hak'uri kiyi ma iyayyen ki biyayya dan baza su baki mijin daba nagari ba da yardan Allah zakiyi farin ciki a rayuwan auren ki" Nabila bata k'ara cewa komai ba,Bayan kamar minti goma wani yaro ya shigo gidan yace ance ana salama da Nabila nan da nan Jidda tace ta shirya bayan da zatayi haka ta canza kaya riga da siket tasa sannan ta d'auko hijab iya gwiwarta tasa Basma tace ta tsaya tayi mata make up tace bata so ta kyaleta, Fita waje tayi Sameer ne tagani cikin riga sky blue da wando jeans black yasa earpiece a kunnan shi ya jingina da mota,cikin mamaki tace shi kuma mai yakeyi Annan,karasawa tayi har gabanshi ta tsaya,Wow nace dan sunyi bala'in dacewa da juna,d'ago kai yayi ya kaleta ya yatsina fuska sannan ya bud'e k'ofan motan Safwan ne ya fito sai k'ara d'aure fuska yakeyi,Sameer ko gefe can nesa dasu yaje yatsaya yana aikin buga game, Cikin muryanta mai sanyi tace"ina yini" "Lafiya"ya amsa mata ciki ciki,kalonta yakeyi daga sama har k'asa aranshi yace yarinyan akwai kyau ga kuma shape dan haka zai aureta ko dan ya more ni'imar da Allah yayi mata,lashe lips d'inshi yayi yana imaging d'in gasu sunyi aure suna soyyewa,ni kam nace toh fa, Sun d'auki tsawon 20 minute a haka ba wanda yayi magana can yace"ni zan wuce zan dawo gobe" Kanta na k'asa tace"toh san anjima" Ta shiga gida,shi kuma Safwan ya kira Sameer suka tafi, Washegari yace Sameer ya shirya zasu gidan su Nabila,Sameer yayi mamaki sosai ganin da kyar ya yarda yaje gidan Amma yanzu da kanshi yake cewa zai je,nan suka shirya suka je gurin Sitti yace zasu gurin Nabila Sitti taji dad'i sosai ganin yanzu Safwan ya hak'ura,sanan suka tafi, Nabila ce ta fito yau ma Sameer ta fara gani sannan Safwan nan Safwan yace ta shirya zasu fita shan iska ne. *TAKU A KO DA YAUSHE* *UMMU BASHEER*✍đŸ» [10/9, 15:25] 80k: đŸŒč *ALK'AWARI*đŸŒč đŸŒč {The promise} *NA* *UMMU BASHEER* ® *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart of reader's)_ #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM *#IG PML WRITERS* #https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 #http://maryamsbello.blogspot.com *PAGE* *23*~ *24* *DEDICATED TO RAHMAT MUH'D RUFA'I NALELE* *Allah ya k'ara basira,kwarin ido da zak'in hannu,Allah ya kare ki aduk inda kike* Ranar d'aurin aure Amarya Nabila taci kwalliya da kun ganta kunga Amarya,kowa na cikin farin ciki, B'angaren Ango Safwan kam sai shirin tafiya d'aurin aure ake can k'auyen kura,Safwan ne acikin mota ya d'an fita kafin lokacin tafiya yayi,dai dai yazo check point ya tsaya wani police yace yq bud'e boot d'in mota,Safwan ranshi ya b'aci kamar shi d'an Familyn Bina acewai sai anbincike motar shi,da farko gardama yayi musu sai daga baya ya bud'e,wani d'an k'aramin akwati suka gani aciki,suka tambaye shi mene ne aciki,shi ma da mamaki yace bai sani ba su bud'e su gani,aikuwa suna bud'ewa mai zasu gani Cocaine ne cike da akwatin,cikin hanzari wani police ya sama Safwan ankwa tare da cewa"You are under Arrest" Iya rud'ewa Safwan ya rud'e sai zare ido yakeyi ya fara cewa wallahi bai san ya akayi aka samai a mota ba inna aiko sauraran shi basuyi ba suka saka shi a mota direct police station suka nufa da shi, Kowa da kowa sun hallara domin tafita d'aurin aure Amma sama da k'asa anrasa ina ango ya shiga gashi lokaci sai tafiya yakeyi,Sameer shima sai neman shi yake Amma ya rasa shi,can saiga kiran wani police dayake yasan su Dad nan yace suzo police station,ai ba b'ata lokaci sukaje police d'in yayi musu bayanin komai dake faruwa kuma zasu rik'e Safwan har sai sun gama bincike sun san gaskiya,hankalin su Dad ya tashi gashi yau ne ranar d'aurin aure yaza suyi kenan,haka suka koma gida bazasu b'oye ma Sitti meke faruwa ba yazama dole su sanar da ita,nan suka keb'e da ita suka gaya mata hankalinta ya tashi sosai kuma ranta ya b'aci harga Allah tana son jikokin ta Amma abin da Safwan yakeyi na damunta,yanzu babbar damuwan su yaza suyi da d'aurin auren nan tunda ankama Ango, Sitti tace suje zatayi shawaran abin daza suyi,sai zagaye parlourn take yi tana tunani can ta yanke shawaran akira mata Sameer, Lokacin da Sameer ya shigo yasameta sai share hawaye takeyi,Cikin rud'ewa ya karasa wajan ta yana tambayan ta meya sameta, Zama tayi kan kujera shi kuma ya zauna a k'asa yana fuskantar ta rik'o hannun ta yayi yace"Sitti na meyasa ki zubar da hawaye meyasa ki cikin damuwa da tashin hankali har kike hawaye wanda najima banga zubar su ba please ki taimake ni ki amsa min tambayoyina?" Gefen gyalen ta tasa ta k'ara share hawaye sannan tace"Safwan nacan police station ankule shi" Cikin rud'ewa yake tambayan ta meyafaru,nan ta fad'a mai komai,haka ya shiga bata hak'uri da kwantar mata da hankali, Kalon shi tayi tace"kayi min *ALK'AWARI* zakayi duk abin dana saka ka taimake ni,nida iyayyen ka" Da sauri ya k'ara rik'e hannun ta kamar wanda za'a k'wace mai ita yace"Sitti na zanyi komai kike so inhar zakiyi farin ciki ki fad'a min me kike so" Tace"kayi min *ALK'AWARI* zaka sani cikin farin ciki bayan Safwan daya sani cikin bak'in ciki,ka taimaka kar muji kunya mutane sun taru dan d'aurin aure Amma ango an kule shi ka taimaka kar musa iyayyen Nabila cikin tashin hankali,sannan ina so kayi min *ALK'AWARI* *Zaka auri NABILA*" Arazane ya d'ago kan shi atake nan idon shi yayi jajawur kalonta yake ya kasa magana yana cikin wani irin shock, K'ara cewa tayi"kayi min *ALK'AWARI*zaka aureta ta kuma zaka rayu da ita duk wuya duk runtsi" Da gyar ya bud'e baki yace"Shin idan namiki *ALK'AWARI*na aureta zakiyi farin ciki?" D'aga mai kai tayi,bai san lokacin daya rungumeta ba wani irin kuka ya kusa kufce mai da gyar ya had'iye sai hawaye ke zuba kamar anbud'e famfo,yace"Sitti kin kula dani tun ina d'an shekara d'aya mahaifiyata ta tafi ta barni,mahaifina ya kyale ni baya sona,ke kad'aice mai sona mai kula dani meyasa ni bazan saki farin ciki arayuwa ba,ni Sameer nayi *ALK'AWARI* zan auri Nabila domin samun farin cikin ki,na miki wannan *ALK'AWARIN*" Fad'an irin farin cikin da Sitti ta shiga b'ata lokaci ne,nan tace yaje ya k'ara shiryawa su tafi dan lokaci ya k'ure nan ta fad'ama su Dad hukuncin data yanke,Dad yace"meyasa zaki ce haka shi kuma Safwan fa?" Dadsyn Safwan ne ya katse shi ta hanyar cewa"abin da tayi shine dai dai domin dama can yarinyan bata dace da shi ba dan kamilalliyar yarinya ce dan haka nine waliyin Sameer" Dad yace"shi kuma Safwan yaza muyi da shi kenan anyi mai adalici kenan?" Daddyn Safwan yace"mun riga mun gama magana" Lokacin da Sameer ya fito kamar zai fad'i k'asa da dafa bango ya isa d'akin shi,Nasir na zaune dayake tare zasu tafi d'aurin auren,kalon shi yayi yaga yanayin shi yasan ba lafiya nan ya shiga tambayar shi da kyar ya fad'a mai?shi kan shi ya girgiza dajin haka,Amma sai ya fara kwantar mai da hankali, Sai da Nasir yayi da gaske sannan Sameer ya shirya cikin farar shada,duk da fuskar shi ba annuri Amma yayi kyau ba kad'an ba.... *muje zuwa masu karatu* *Shin ko Iyayyen Nabila za su yarda?* *Shin insun yarda ita zata yarda?* *Mai zai faru da Safwan?* *Amsoshin tambayan nan na page na gaba* *Taku a ko da yaushe* *UMMU BASHEER*✍đŸ» [10/9, 15:25] 80k: đŸŒč *ALK'AWARI*đŸŒč đŸŒč {The promise} *NA* *UMMU BASHEER* ® *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart of reader's)_ #WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM *#IG PML WRITERS* #https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 #http://maryamsbello.blogspot.com *PAGE* *25* ~ *26* *Ina mai baku hakurin jina shiru da kukayi kwana biyu* *DEDICATED TO MAIMOUNATH &BEAUTY QUEEN* *Sister da k'awas wanan shafin naku ne na gode da sadaukarwan ku gare ni Allah ya bar zumunci,Allah yasa ku gama book d'in ku lafiya* *K'arfe*2:30pm dai- dai suka iso k'auyen,mutane har sun gaji da jira kasancewar d'aurin auren 2:00 ne, Daddyn Safwan ne ya shiga basu hak'uri sannan yace yana son ganin baban Nabila,bai b'oye mai komai ba ya fad'a mai gaskiya,duk da cewan baiji dad'i ba shida yayan shi Amma sun yarda da a had'a auren da Sameer dan sun yaba da hankalin shi,nan yayan Baba yaje ya gaya ma liman halin da ake ciki, Nan aka *D'AURA AUREN SAMEER UMAR BINA DA NABILA USMAN IBRAHIM AKAN SADAKI MAFI DARAJA*mutane sai tunani wasu suke tunda sun san sunan Angon SAFWAN Ya Khalil dayaji yayi mamaki gashi mutane sunyi yawa bale yaje ya tambayi baban su,shi ko Sameer lokacin da aka d'aura sai da yaji wani iri ajikin shi bazai ce ga halin daya shiga ba,nan take kanshi ya fara mishi wani azababben ciwo da k'yar yake murmushin yak'i, B'angaren Amarya Nabila kuwa tana zaune gefe guda jikinta yayi sanyi gashi gaban ta sai fad'i yakeyi bata san mai yasa ba,kamar daga sama taji anacewa" *AN D'AURA AUREN SAMEER UMAR BINA DA AMARYAN SHI NABILA USMAN IBRAHIM* arikice ta mik'e tsaye tana tunanin shin abin dataji da gaske ne kuwa?,k'anwar baban ta ne ta shigo tace an d'aura aure da Sameer,ido jajawur Nabila tace"da gaske kike Mami?" Ganin yanda jiri ke shirin yar da Nabila yasa ta k'arasa da sauri ta rungumota kar ta fad'i nasiha ta shiga mata,Amma inna Nabila ba abin datake sai kuka,Basma ta rik'o hannunta ita ma tana bata hakuri,ranar Nabila taga tashin hankali sai ma lokacin da aka ce za'a tafi da ita ai bayi ta shiga ta kulle ta dinga rusa kuka sai da Jidda tazo shima da k'yar ta fito aka shirya ta cikin wata material purple and golden d'inkin riga da siket aka samata gold d'inta sai gyale shima purple,Amma fa da k'yar aka shirya ta,d'akin mama aka kaita tayi mata nasiha mai ratsa jiki kowa na gurin sai da jikin su yayi sanyi,sai da aka b'anb'are ta ajikin mama ita kanta mama sai da tayi hawaye,parlour'n Baba aka nufa da ita shima yayi mata nasiha sosai yace tayi hak'uri da k'addara haka Allah ya nufa cewan bazata auri *SAFWAN BA SAI SAMEER* ,aiko nan ta saki kuka wato dai da gaske *SAMEER TA AURA* lokacin da aka fito da ita k'ofar gida taga ya Khalil ai da sauri ta rungume shi tana kuka tace"Ya Khalil ka gayamin shin dagaske ne Sameer aka d'aura min aure da shi ba Safwan ba?" Girgiza mata kai yayi alaman kar tayi kuka dan shi kanshi jiyake kamar yayi ta dukan Sameer d'in dan ya tsane shi, Da kan shi ya saka ta a mota suka d'auki hanyar kaduna k'arfe 8:00 suka shigo garin Kaduna,b'angaren Sitti aka fara shiga da ita Sitti taji dad'i sosai tayi ta sama Nabila Albarka,a wurin Sitti suka zauna dayake anshirya INDIAN DAY aikam wasu make over suka shigo d'akin Sitti suka hau shirya Amarya nan da nan Amarya ta fito tayi kyau sosai,Basma ce ta fito da wayanta tana selfie da Nabila ita ko kamar ta shak'eta takeji dan haushi,dauriya kawai Nabila takeyi Amma jitake kamar zuciyan ta tafarfasa yakeyi, Wani guri agefen gidan aka yima decoration komi milk da golden hatta ankon colour d'in shi kenan Amarya kuma nata golden da black, sai Ango wanda yasa kayan indian shima irin colour na Amarya, wow sunyi kyau ba kad'an ba, Lokacin da Amarya aka fito da ita lokacin ne Sameer ma ya fito shida Abokan shi wanda duk aikin Nasir ne ya gayato su,haka Aunty Jidda ta rik'o Nabila har gaban Sameer tace ya rik'e ma Nabila hannu su shiga tare, ko kalansu bai yi ba bare yayi abin da Aunty Jidda tace sai Nasir ne yayi saurin rik'e hannun shi ya had'a dana Nabila aiko wani irin shock sukaji alokaci d'aya cikin mugunta Sameer ya matse mata hannu ahaka suka shiga gurin sai d'aukan su hotona akeyi har suka zauna akujera still bai saki hannun ta ba sai matse mata yake cikin salon mugunta, Anci ansha anyi rawa Amma su kam Ango da Amarya basu yi ba,kuma atare suka fita waje da aka tashi sannan ne ya sakin mata hannu aiko hannun yayi ja,sai alokacin ta fuskanci wani abu wato yan'uwanta za'a basu gurin kwana Amma ita zata shiga d'aki da Sameer,Sitti ce ta rik'e hannun su har dai dai k'ofar parlourn Sameer sannan ta had'a hannun su guri d'aya tayi musu addu'a tare da fatan alkhairi tace su shiga ita kuma ta juya ta tafi,ai suna shiga parlourn ya saki hannun Nabila tare da jan tsaki mai k'arfi ya shiga d'akin shi ya barta nan tsaye jiki asanyaye ta shiga d'ayan d'akin datake tunanin shine nata,data shiga duhu ta gani ahankali ta kai hannu ta kunna wutar d'akin nan da nan haske ya mamaye ko'ina,wow d'akin ya had'u komai pink and red ne ga wasu flowars masu kyau da akayi decoration d'insu d'akin sai zuba k'amshi yakeyi, Azuciye ta fara cicire flowars d'in ta fasa duk wani abu na glass dake d'akin hannun ta duk jini Amma bata damu ba duk ta Hargitsa d'akin sannan ta fad'a kan gado ta saki wani irin kuka tare da cewa"na tsane ka Sameer nayi *ALK'AWAI* baza ka tab'a samun farin ciki da niba sannan nayi *ALK'AWARI*ba zan tab'a sonka ba" *Taku a ko da yaushe* *UMMU BASHEER*✍đŸ»

Share this


Author: verified_user

0 Comments: