🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲
♻♻ *PWA* ♻♻
_08185819176_
••••••••••••••••••••••••••••••
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
*BIRNIN SAHARA*
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
••••••••••••••••••••••••••••••
________________________________________
_______________________
*ѕtσrч/wríttєn ву✍🏻:*
👉🏻© *_Haiman Khan Raees_*
(℘ᾰ❡ḙ 11)
Yayinda Sarauniya Diana ta ja Hannun Kuyanga Hameedah suka kadaice daga su sai su. Sai suka fara tattauna wani al'amari cikin rada. Bayan sun kammala Tattaunawar sai Sarauniya Diana ta dauko takarda da biro tayi wasu Rubuce-Rubuce sannan ta mikawa Kuyanga Hameedah. Kuyanga Hameedah kuwa ta rusuna har kasa sannan ta amsa, bayan ta amsa ne sai ta gyadawa Sarauniya Kai Yayinda ita ma Sarauniyar ta gyada mata kai. Daga nan sai Kuyanga Hameedah ta fice daga cikin turakar tana mai sauri.
Bayan fitar Hameedah sai SARAUNIYA Diana ta kasa zaune ta kasa tsaye, ba komai ne ya jawo hakan ba kuma face hukuncin da ta yanke, tabbas ta san cewa Haiman Mutum ne mai Wuyar Sha'ani kuma yana iya Tarwatsa mata shirin ta cikin abinda bai wuce dakika uku ba. To amma, ai masu iya magana sunce mai rai ba'a rasa shi da MOTSI, bari dai ta zuba ido taga abinda zai faru.
Tana cikin wannan hali ne sai ga wata baiwa tashigo tayi sujjada a gabanta sannan tace "Ya Kyakkyawar Sarauniyar Da babu Kamar ta, Boka Nuna'v ne Yazo Yake so ya gana da ke". "shikenan muje! Diana ta fada Yayinda ta Nunawa baiwar hanyar fita daga cikin turakar.
Boka Nuna'v na zaune akan Luntsumemiyar kujerar da aka tanada domin tarbar baki, ga ABABEN ci da sha nan Birjik kamar ba'a so akan wani dogon tebur, sai dai ko kadan wadannan abubuwa basu birge Boka Nuna'v ba, hasali ma dai shi kanshi a cikin tashin hankali da zancen zuci yake domin Binciken da ya gudanar jiya a Halwar tsafin sa ya tabbatar masa da cewa burinsa ba zai taba cika ba matukar Wannan Bakon Yaron Yana raye. Hakan ne ma yasa ya garzayo zuwa wajen SARAUNIYA Diana domin ya zugata ta kashe Bakon kawai kowa ya huta.
Yana cikin wannan hali ne sai ga Sarauniya Diana da wannan baiwa tata sun shigo cikin falon, cikin farinciki da Murnar Ganin Sa Sarauniya Diana ta ruga da gudu ta Rungume shi tana masa Lale da zuwa.
Bayan sun gama gaisawa, sai Sarauniya Diana ta zauna a kan kujerar da take kallon ta Boka Nuna'v sannan tace; "Yakai Sarkin Bokaye Kuma babban aminin Mahaifina, shin Me Ya Fito da kai daga gida cikin wannan Talatainin dare haka? Ina fatar dai ba wata MUSIBA ce ta tunkaro wannan gari namu ba ko?"
Boka Nuna'v Yayi Ajiyar Zuciya, sannan ya fara magana da cewa: yake 'yata zan so muyi wannan magana ne a kadaice idan babu matsala, ko da jin haka, sai Diana ta yiwa wannan baiwa alamar ta fita ta basu waje. Bayan baiwar ta fita ne sai Boka Nuna'v ya ci gaba da cewa "ki sani cewa Babbar Masifa Ta Tunkaro Wannnan Gari Namu Na BIRNIN Sahara, Masifa irin wacce bamu taba ganin irin ta ba, Masifa ce wacce idan ta zo hatta Jaririn dake goye a bayan Uwar sa ba Zata kyale shi ba, sai dai kuma akwai mafita, Mafitar kuma ke kadaice kike da damar yin amfani da ita a hannun ki".
KO da jin wannan furuci daga bakin Boka Nuna'v, sai hankalin Sarauniya Diana Ya tashi, cikin matukar damuwa ta dubi Boka Nuna'u tace da shi: "ya kai babban Boka, shin wannan wace irin Masifa ce haka? Kuma mecece Mafitar wacce ni kadaice zan iya samar da ita?"
Boka Nuna'u yayi ajiyar zuciya sannan yace: Ai wannan matsalar ba komai bace face wannan bakon yaro wato Haiman, Bincike na ya nuna min cewa matukar bamu kawar da wannan yaro daga Doron kasa ba, to lallai ne Watarana sai ya zo ya Murkushe mu, ya kashe na Kashewa ya kwace sarautar birnin sannan ya daura jama'ar mu akan tafarkin wani Addini can na daban. Ke ce sarauniyar wannan Birni, duk hukuncin da kika yanke a kanshi ya zauna, don haka shawara ta rage naki".
Koda Boka Nuna'u yazo nan a zancen sa, sai hankalin ta ya Dugunzuma, ta rasa me zata ce. Can bayan wani dan dogon lokaci sai ta dago kai cikin alamun damuwa tace da shi: "Ya kai babban Boka shin babu wata hanya da za'a iya Bi a magance wannan matsalar dole sai kisa ya shiga al'amarin?"
Ko da jin wannan tambaya, sai Boka Nuna'u yaji Tamkar an zuba masa ruwan sanyi a Zuciyar sa domin akwai alamar haqar sa ya kusa CIMMA ruwa, amma saboda tsabar Kwarewa a iya Munafunci sai yayi narai narai da idanuwa kamar wanda akayiwa Mutuwa sannan yace; "Yake Sarauniyar Duniya, Wannan itace kadai mafita, Amma idan akwai wata hanyar da kike ganin tafi dacewa, kina iya binta, amma dai ki sani, nauyin kowane Mutum dake wannan Birni namu ya rataya ne a Wuyar ki, kuma kowa zai zarge ki da yimasa rashin adalci Yayinda suka fahimci cewa kece SANADIN faruwar Bala'i a gare su, haka kuma zasu Kalle ki da Qima da girma ne kawai Yayinda suka fahimci irin kokarin da kika yi wajen samar musu da Dauwamammen zaman lafiya "
Yayinda Boka Nuna'u yazo nan a zancen sa, sai Sarauniya Diana tayi ajiyar zuciya sannan tace: "shikenan shugaban Bokaye, zanyi nazarin wannan batu naka zuwa gobe, in yaso sai in yanke hukunci a fada".
"Yauwa 'yata kuma sarauniyar duniya, bani da Kokwanto a Raina dangane da ke, na yi imani da cewa zakiyi abinda ya dace", ni zan Koma gida saboda in ci Gaba da nazarin wani magani da nake son in kammala hadawa ", Boka Nuna'u ne yayi wannan Furuci Yayinda ya Mike tsaye. Ganin haka yasa Sarauniya Diana ta Sallame shi ya tafi.
Shi dai Boka Nuna'u ya tafi gida ne ransa cike Makil da farinciki, domin kuwa yana da tabbacin cewa Burinsa na son ganin ya Jefi TSUNTSAYE biyu da DUTSE daya ya kusa tabbata. Amma ita Sarauniya Diana, gaba daya wannan batu da Boka Nuna'u yazo dashi ya Dagula mata tunani. NANFA ta fara SAFA da Marwa a falon tana tunanin wane hukunci ya kamata ta yanke dangane da wannan al'amari.
Tana cikin wannan hali ne sai ga Kuyanga Hameedah ta shigo falon cikin sauri, tana zuwa babu wata wata ta fada mata cewa anyi nasara, wannan labari yasa hankalin ta ya dan kwanta. Daga nan ta sallami Kuyanga Hameedah ta tafi, Yayinda ita kuma ta nufi cikin turakar ta. A wannan lokaci dare ya raba, amma Sarauniya Diana ko gezau bata jin bacci saboda abubuwa da suka taru suka yi mata yawa.
Muna zaune a cikin wannan Faffadan daki dake cikin Kurkukun Birnin Sahara nida Imran Muna ta Hirar mu. A cikin Hirar tamu ce na fahimci cewa Imran yana Tattare da wata irin baiwa ta ban Mamaki, duk abinda na fada masa sau daya shikenan ya riqe shi kamar dama can ya San shi. A cikin wannan dare sai da Imran ya haddace Surorin Alqur'ani Mai girma guda Ashirin Da shida. Sannan muka fada fagen Tambayoyi da Amsoshin su, inda ya dinga min tambaya ni kuma ina bashi amsa tare da yi masa bayani akan duk wani MUHIMMIN Abu da ya kamata ace sabon shiga Addinin Musulunci Ya sani gwargwadon sani na. Muna cikin haka ne sai muka ji Karar takun sawayen wani ya nufo dakin da muke ciki. Ba tare da wata Fargaba ba muka Mike tsaye dukkan mu tare da zuba ido akan kofar dakin don ganin waye shi kuwa da tsakar daren nan.
Bamu jima a cikin wannan hali ba sai muka ga wata wata Mace kyakkyawa sanye da kayan kuyangin gidan Sarautar birnin sahara biye da ita a baya kuma wasu Narka-Narkan Qarata ne guda uku suna ta Muzurai kamar Saci babu.
Koda wannan kuyanga ta zo dai dai bakin kofar da muke wacce aka yi ta da Zunzurutun Rodi, sai ta tsaya sannan ta yiwa dakarun dake biye da ita alamar su dan ja da Baya. Bayan dakarun nata sun ja da baya sai ta nuna ni da dan Yatsan ta sannan ta yafito ni da hannu alamar in zo. To ka sanni da zafin rai, sai naga kamar wannan ai Rainin wayo ne, don haka kawai sai na basar kamar ban ganta ba na Koma na zauna abina na juya mata baya.
Ganin wannan Abu da na aikata ne yasa Imran ya risina yana mai dafa kafada ta sannan yace; "Ya kai Haiman, kada ka dauki wannan al'amarin da zafi, Kaje gareta kaji mai ke tafe da ita". Jin yadda ya tausasa murya da kuma Mutuncinsa da nake gani sakamakon Shigowar sa Musulunci ne kadai suka sa na amince da batun sa ba don Raina yana so ba. A Sanyaye na Mike ina tafiya kamar ba zani ba har naje daf da bakin kofar, har ya zamana ina iya jin Numfashin ta, sannan na dubeta ido cikin ido da nufin in daka mata tsawa tare da tuhumar ta kan dalilin da yasa tazo gare ni cikin wannan dare.
Sai dai kafin in aiwatar da wannan nufi nawa, tuni wannan kuyanga ta matso gare ni cikin wani irin zafin Nama ta toshe min baki da hannun ta. Mamaki ya hanani cewa komai, bayan ta toshe min baki da hannun nata sai kuma tayi amfani da dayan hannun nata tayi min alamar inyi shiru sannan ta gyada kanta da alamar "Ka Gane?", nima sai na gyada mata kai da alamar "Eh Nagane!"
Daga nan sai ta saka hannun ta a cikin wani Boyayyen aljihu dake cikin rigarta ta zaro wata takarda ta Miko Min. Na amshi Takardar jikina a Sanyaye na Warware ta domin ganin ko Menene a Ciki, aikuwa ina Budewa sai naga rubutu kamar haka:
*_Ya Kai Haiman, Idan har Kana so Ka fita daga cikin wannan Birni a raye, to ya zama dole a Gareka ka Bi duk umurnin da zan baka a gobe kana mai nuna cikakkiyar biyayya a gareni, ta haka ne kawai zan iya tseratar da rayuwar ka data Masoyiyar ka. Ka Taimakeni Kada Ka Bani Kunya Haiman, Sako Daga SARAUNIYA DIANA_*
Koda na gama karanta abinda wannan Takarda ta Qunsa, sai nan da nan naji kaina ya fara ciwo, domin Miliyoyin Tunanuka ne suka antayo min cikin kwakwalwa ta. Mafi girma daga cikin su kuma tambayoyi ne wadanda Amsoshin su ba masu Samuwa bane.
Me Yasa Diana take so ta cece ni?
Kuma me yasa har take Roko na?
Menene sirri da kuma Ribar Biyayyar da Take so In yi mata a gobe? Wadannan da ma wasu Sambada Sambadan Tambayoyi Makamantan su ne suka taru sukayi min Kane-Kane a cikin kwakwalwa ta. Ina cikin juya zancen a cikin Zuciyata ne kawai sai naji an girgiza ni, NANFA na dawo cikin hayyaci na ba shiri, ashe wannan kuyanga ce ta girgiza ni sakamakon dadewa da nayi ban bata amsa ba.
KO da muka hada ido da ita sai ta Kada Kanta tana mai min alamar "Ka Amince?" cikin sanyin jiki na kada mata kai nima da alamar "Eh na Amince!". Daga nan sai wannan kuyanga ta fizge Takardar dake Hannu na ta jefa ta cikin bakinta ta Sankame ta kamar ta sabi Buredi, bayan ta lamushe Takardar sai kuma ta Risina kasa cikin Girmamawa tayi mana alamar godiya sannan ta juya ta tafi, dakarun da suka Rakota suka rufa mata baya, kafin kace kwabo har sun bace daga dakin.
Bayan sun tafi ne sai na Koma inda Imran yake na zauna jikina a Sanyaye ba tare da nace komai ba. Bayan wani dan lokaci sai Imran ya dafa Kafada da yace "Ya kai Dan Uwana me yake faruwa ne? Har na bude baki zan bashi amsa sai naji kamar wani abu na motsi a kusa da bakin kofar dakin da muke ciki don haka sai na Lallaba na je kusa da kofar na daka tsawa tare da cewa" Waye Ne Anan?" aikuwa fadin hakan ke da wuya sai naga wani sirrin mutum yayi fitar burtu ya ruga a guje kamar zai bar duniyar.
Daganan sai na Koma inda Imran yake na Labarta masa duk abinda ya faru, koda yaji wannan batu nawa sai shima jikinsa yayi sanyi. Bayan ya dade yana tunani sai yace dani: " yakai Haiman, ka sani cewa akwai wasu Maganganu da Kankana yake yawan fada Yayinda yake raye, a duk lokacin da ya fadawa mutum su yakan barshi ne dasu a matsayin Linzamai da zasu taimaka masa wajen yanke hukuncin da ya kamata da shi," ko da naji wannan batu nasa sai nace " Ya kai Imran su kuma wadannan wasu irin Maganganu ne haka?"
KO da jin wannan tambaya tawa sai Imran yace: "Maganganu ne guda biyu, na Farko a duk lokacin da kazo mishi da batun ka samu wani abu na ci gaba, to yakan ce dani " YA KAI JIKANA, KA SANI CEWA, A DUK LOKACIN DA KAGA WANI CI GABA YA TUNKARO KA, TO KA SANI CEWA CIKIN BIYU DOLE NE A SAMU DAYA, KO DAI LOKACIN CI GABAN NAKA NE YAZO, KO KUMA TARKO NE AKE SO KA FADA CIKI", magana ta biyu kuma yakan fade ta ne Yayinda duk yaga na shiga damuwa saboda neman mafita dangane da wani al'amari daya dame ni, yakan ce dani "YA KAI JIKA NA, KA SANI CEWA DUK AMSAR DA KAKE NEMA TANA CIKIN ZUCIYAR KA, MAI YIWUWA KAI BA ZAKA YARDA DA KANKA BA, AMMA AMSAR DUK DA KAKE NEMA TANA CIKIN ZUCIYAR KA".
Yayinda Imran Yazo nan a zancen sa, sai nayi shiru na rasa me zan ce, daga baya dai sai na tambaye shi da cewa "To amma in banda abin ka, ta yaya wadannan maganganun zasu taimaka min wurin yanke hukuncin abinda ke tunkaro ni? Da Imran yaji kalamaina sai yayi Murmushi sannan yace: " Kayi Tunani! Daga nan kawai sai ya kwanta abinsa ya barni nan ina zaman Kahon Dandi.
Wannnan Shi Ne Abinda ya faru Tsakanina da Imran a Kurkukun BIRNIN SAHARA.
Zan Ci Gaba In Shaa Allaah
_*Phone:*_
08185819176
_*Web:*_ www.haiman.com.ng
_*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees
_*Twitter:*_ @HaimanRaees
_*Instagram:*_ Haimanraees
_*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲
♻♻ *PWA* ♻♻
Sai ranar alhamis in shaa Allaah



0 Comments: