🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲
♻♻ *PWA* ♻♻
_08185819176_
••••••••••••••••••••••••••••••
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
*BIRNIN SAHARA*
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
••••••••••••••••••••••••••••••
________________________________________
_______________________
*ѕtσrч/wríttєn ву✍🏻:*
👉🏻© *_Haiman Khan Raees_*
(℘ᾰ❡ḙ 12)
_______________
Dargazu Na Zaune akan wata Bakar Kujerar Bakin Karfe dake Cikin Tafkeken Falon Sa yayi shiru Fuskar sa a Murtuke, sai ga wani Siririn Bawa Ya shigo yana haki kamar ransa zai fita. Ko da ganin sa a cikin wannan hali, sai nan take Dargazu ya Mike Tsaye yace: "Ya kai Talyus, me ya faru gareka na ganka a wannan hali? Ko da jin wannan tambaya sai Talyus ya nutsu sannan ya kwashe duk abinda yaji kuma ya gani tun daga Lokacin da Imran ya Musulunta Har Izuwa Lokacin Da Haiman Ya Daka Masa Tsawa Ya Firgita ya gudu.
Yayinda Dargazu yaji wannan labari sai Kansa ya Kulle, nan fa ya fara Zarya a cikin dakin yana tunani. Bayan wani lokaci mai tsawo sai ya juyo ya kalli Talyus yace: "Ya kai Talyus, shin Ka tabbata cewa Kuyanga Hameedah ka gani Taje wajen Haiman?" "Eh Yallabai na tabbata, Talyus ya bada amsa." Kuma Ka tabbatar Da Cewa ta bashi wani abu?" "Eh Yallabai, amma na Rantse da uwata ban san ko menene ba, kuma babu wanda yayi magana daga cikin su, ni Yallabai ina ganin kamar dama shi Haiman din yasan da zuwan Sakon!" Talyus ne yayi wani jawabi. Bayan wani dan lokaci sai Dargazu ya dauko wata Matashiyar Jaka cike da Lu'ulu'u ya jefa ma Talyus sannan ya sallame shi ya tafi.
Bayan Fitar Talyus ne sai Dargazu ya ci gaba da tunanin sa cikin damuwa. Ba komai ne ya sashi cikin wannan damuwa ba face wannan Bakon Yaro, tun daga Lokacin da yazo wannan Birni nasu al'amura duk suka Bi suka Lalace. Yanzu kuma gashi har SARAUNIYA da kanta take aiko babbar Kuyangarta gare shi, ga kuma wani Bakon Addini Da yake kokarin Yadawa, Lallai ya zama dole ayiwa Tufkar Hanci in ba haka ba komai zai iya lalacewa. Haka dai Dargazu yayi ta tunanin sa har hasken alfijir ya keto ba tare da ya Ankara ba.
×××××××××××××××××××××××××××
Ina nan zaune ina tunanin wadannan maganganun da Imran ya fada min har barci ya kwashe ni. Ban tashi ba har sai da sanyin alfijir ya keto ya tashe ni, daga nan na tashi Imran mukayi Taimama mukayi Sallah. Da gari ya waye sosai, sai muka ga an kawo mana abinci mai rai da lafiya harda abubuwan sha. Da Imran kamar ba zai shaba wai saboda kada ya zamana an zuba guba muci mu mutu, ai da naga haka sai nace ina zuwa kawai nayi Bismillah na hau cin abinci ba tare da wata Fargaba ba, da dai yaga haka shima sai ya biyo bayana. Nan dai muka ci muka sha muka godewa Allaah.
Ba muyi Minti Talatin Da gama cin abinci ba sai ga Dakaru sun zo kofar Dakin Da muke Ciki, Babba daga cikin su ya nuna ni da Yatsan sa yace "Sarauniya Diana Tana bukatar ganinka yanzu, daga nan sai ya sa Makulli ya bude kwadon dakin yayi min alamar in fito. Har na kama hanya zan fita sai na Waiga na Kalli Imran wanda tuni alamun damuwa sunyi masa Sambadebade a fuska nace: " Kada ka damu dan uwa, babu abinda zai same ni in shaa Allaah!". Ko da Imran yaji haka, sai ya saki fuskar sa, amma duk da haka sai ya ce dani: "Amma dai ina fatar Ka na da mafita dangane da batun nan ko?", ko da naji wannan tambayar sai nayi wani irin murmushi ta gefe daya, wato irin Murmushin nan da ake kira na Mugunta, sannan nace da Imran, "Kada Ka Damu Abokina, Ina da mafita! Daga nan mukayi sallama Na fita daga dakin. Ina fita kuwa suka maida Makulli suka Garqame kofar dakin sannan suka sani a Tsakiya.
Dakaru kimanin Ashirin ne suke bayana, sannan sai wasu kamar su a dama da hauni na, sai kuma biyar a gabana suna mana jagora. Haka muka ci gaba da tafiya ba tare da nasan ina muka nufa ba. Wani abu da ya bani Mamaki shi ne, Sam babu wanda ya damu da cewa ba a daure nake ba. Haka dai muka ci gaba da tafiya muna wuce Wurare iri daban daban. Ga dukkan alamu dai a karkashin kasa muke domin bana iya ganin komai face inda nake takawa da kuma saman Kaina, kuma ina iya jin kururuwar da sauran Fursinonin gidan yarin suke yi.
A haka dai muka ci gaba da tafiya har muka fito fili inda ina iya ganin sararin samaniya. Daganan sai aka daura ni akan wani katon keken Doki mukaci gaba da tafiya. Tsawon lokaci muna wannan tafiya babu wanda ya ce da wani kala. Can sai na dubi wani dan Siriri daga cikin Dakarun dake tare dani nace "Amma Kai ya naga kayi rama da yawa ne? Ko baka samun abinci sosai ne?" Maimakon ya bani amsa, sai kawai yayi banza dani kamar ma bai ji ni ba. Da Dai naga haka sai na taba Kafadar sa domin in sake Maimaita tambaya ta. Haba ai kuwa sai gani nayi ya kawo min wani wawan naushi, ba don na Ankara da wuri na goce ba da tuni na zama dameji. Wannan Abu sai ya bata min rai don haka sai na matso da karfina nace "wai ku wasu irin Falalai ne da Baku san wasa ba? Ku shikenan komai mutum yayi sai Ku kai duka da kokarin sheke shi... Ban gama fadar abinda ke Raina ba sai kawai naga kowanen su ya juyo kaina ya saita ni da Makamin dake hannun sa. Aikuwa banyi wata wata ba na Sankame Bakina, don naga alama wadannan ba wasan suke so ba.
Haka dai muka ci gaba da tafiya akan wannan keken doki muna ratsa Sahara. Sai dai bana iya ganin komai sakamakon zagaye ni da wadannan Samudawan suka yi. Tafiya muke yi zamu ba zamu ba dai har muka shigo cikin gari, na fahimci hakane ta hanyar Hayaniyar jama'a da na fara ji. Bayan mun taba 'yar Doguwar tafiya a cikin garin sai naji keken dokin da nake ciki ya tsaya. Daganan kuma sai wadannan Samudawan dakarun suka Sassauko sannan suka bani umurnin nima in sauko. Bayan na sauko sai suka sake yi min Rumfa kamar yadda sukayi da farko, sannan suka iza keya ta a gaba muka fara tafiya.
SARAUNIYA Diana tana zaune akan Karagar Mulkin Ta Tana karbar gaisuwa daga Mabiyanta. Fada ce Kasaitacciyar gaske ta gani ta fada. Ga mutane nan sun cika Makil, dakaru kuwa kai ka ce yaki za'a je. Gabaki dayan 'yan Majalisun kasar Sun Hallara a fadar. Dargazu da Mukarrabansa duk sun Hallara, ga kuma Boka Nuna'u nan shima ya samu Kujerar sa ta sarkin Bokaye ya Kame.
A wannan lokaci gaba daya hankalin Sarauniya Diana a tashe yake, domin bata san yaya wannan zama da za'a yi yau zai kasance ba, babban abinda yafi tayar mata da hankali shi ne yadda za'a yi ta iya fitar da Su Haiman daga BIRNIN SAHARA lafiya. Haka dai ta wanzu cikin wannan hali, duk wanda yazo Gaishe ta sai dai ta amsa masa kawai tana yaqe, amma ba gaisuwar bace a gabanta. Tana cikin wannan hali ne sai taji an buga Ganga alamar akwai wani mai son shigowa fadar. Nan take da bata umurnin a baiwa mai son shigowa fadar izinin ya shigo.
Ai kuwa ba'a jima ba sai ga wadannan Dakaru sun shigo cikin fadar a Jere. Yayinda suka zo tsakiyar fadar sai suka tsaya cak! Sannan suka Rabe biyu suka samar da hanya a tsakiya. Ta cikin wannan hanyar ne bakon da ake ta magana Akansa ya fito.
Zan Ci Gaba In Shaa Allaah
_*Phone:*_
08185819176
_*Web:*_ www.haiman.com.ng
_*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees
_*Twitter:*_ @HaimanRaees
_*Instagram:*_ Haimanraees
_*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲
♻♻ *PWA* ♻♻



0 Comments: