🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲
♻♻ *PWA* ♻♻
_08185819176_
••••••••••••••••••••••••••••••
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
*BIRNIN SAHARA*
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
••••••••••••••••••••••••••••••
________________________________________
_______________________
*ѕtσrч/wríttєn ву✍🏻:*
👉🏻© *_Haiman Raees_*
(℘ᾰ❡ḙ 13)
_______________
Bayan waɗannan dakaru sun buɗe min hanya, sai na bi hanyar kai tsaye na fito fili inda ina iya ganin kowa kuma nima kowa na iya gani na. A nan ne fa naga abun mamakin da ban taɓa gani ba a rayuwa ta. A ƙofar wata Jibgegiyar ƙasaitacciyar fada na tsinci kaina. Wato fada ce da ta ƙawatu matuƙa ta yadda idan har nace zan misalta muku ita, to tabbas sai kunce shara ta kawai nake yi.
A ƙalla tsayin fadar daga ƙasa zuwa sama zai kai kimanin tsawon falwayoyi biyu da rabi, ga wasu murtuka-murtukan dirkoki da suka tokare fadar waɗanda ƙarti biyar da wahala su iya ritsa guda ɗaya. Ƙasan fadar kuma an yi masa daɓe ne da wasu irin duwatsun wuta masu canja launi lokaci zuwa lokaci. Gaba ɗaya bangwayen fadar an yi musu wata irin kwalliya ne ɗanyen gwal, ga wasu fitulu ɗirka-ɗirka masu matuƙar haske suna lilo a sama. Fadar tana da zubi ne da yayi daidai da harafin turanci na V, daga can tsakiyar fadar wata ƙasaitacciyar karagar mulki ce wacce ko karagar sarki Lu'umanu na birnin Teheren albarka. Sai kuma wasu matsakaitan kujerun sarauta a dama da haunin karagar.
A zaune a kan wannan Yalwatacciya kuma ƙasaitacciyar karaga, Sarauniya Diana ce ta ci ado da wasu irin kaya
Masu ruwan ƙasa da ƙyalƙyali gami da ɗaukar ido, ga wani takalmi shima mai ruwan ƙasa ta sanya, sai dai irin mai tudun nan ne da Wayayyun mata ne kaɗai ke sawa. Sai kuma hular Sarauta dake bisa kanta wacce ita kuma kalar ruwan gwal ce da ita. Wato na daɗe da sanin cewa Diana kyakkyawar mace ce ta gaban kwatance, amma wannan kwalliya da tayi yau, na tabbatar da cewa in zanyi wata biyar ina tunanin a wane rukuni ya kamata in aje ta a sahun kyawawan mata, gajiya kawai zanyi, domin ko a matakin farko na ajiye ta nasan nayi laifi don ta wuce nan.
A tsai-tsaye a bayan ta kuma wasu Lafta-laftan ƙarti ne guda biyar kamar shanu. A dama da hagun ta kuma waɗan su kujeru ne masu kyawun gaske guda goma-sha-uku-uku. Zaune a kan kujerun farko dake dama da haunin Sarauniya Diana kuma wasu mutane ne guda biyu masu sanye da jajayen riguna. Dukkan su zasu kai kimanin shekaru saba'in saba'in a duniya. Kuma kujerun su suna kusa da na Sarauniya Diana ne. A hagu da mai jar rigar dake daman Sarauniya Diana kuma Dargazu ne zaune tare da 'Yar sa Dardira cikin shigar yaƙi, fuskokin su babu alamar fara'a ko kaɗan.
A dama da mai jar rigar da ke hagun Sarauniya Diana kuma Boka Nuna'u ne zaune a kan wata baƙar kujera wacce ita kaɗai ce mummunan abu da ido na ya kai kansa a fadar. Shima fuskar sa babu alamar fara'a. Ravowar kujerun kuma duk suna ɗauke ne da sauran masu muƙamai a fadar, sai dai akwai wata kujera guda ɗaya wacce take dab da ta boka Nuna'u, itace kaɗai ba kowa a kanta. Me ya sa waccan kujerar ita kuma na ganta empty? Na tambayi kaina a cikin zuciya ta? To kai kuma ina ruwan ka? Wani ɓangare na zuciyata ya faɗa. Nan dai na kori tunanin wannan kujera daga zuciya ta.
Gani na da sauran jama'ar fadar sukayi na fito fili ne yasa suka fara 'yan maganganu kowa na faɗin albarkacin bakin sa. A yayin da suke waɗannan' yan maganganu hankali na baya kansu. Ina can na hangame baki ina kallon wannan kyakkyawar fada wacce ko a mafarki ban taɓa ganin irin ta ba.
Wata ganga da aka buga ce ta sa hankali ni ya dawo jiki na. Ni dai ban ga wannan ganga ba amma dai somehow na san ganga ce. Ban ga wanda ya buga gangar ba kuma ban fahimci sautin daga ina yake fitowa ba. Lokaci guda kawai dai sautin ya bayyana a kunnuwana. Shiru ya biyo bayan wannan sauti Yayinda fadar tayi tsit kamar mutuwa ta gifta.
Can sai wani dan figigin mutum ya Mike tsaye daga kan ɗaya daga cikin kujerun dake hagu da Sarauniya Diana, hannun sa na ɗauke da wata 'yar Madaidaiciyar ganga wacce a ɗazu hankali na bai kai kanta ba. Yayinda yazo tsakiyar fadar, sai ya fara doka wannan ganga tasa cikin wani irin sauti mai daɗin gaske wanda yasa ni har na fara karkaɗa ƙafa gami da mamakin yadda akayi wannan' yar ƙaramar ganga ke bada sauti haka. A taƙaice dai gwani ne wannan.
Wani ɓangare na zuciyata yace "hmm wa yaga su jikan Dujal! Shiru ɗayan ɓangaren ya faɗa. Kafin in sake yin wani tunanin, sai kuma wani mutumin ya tashi ya fara rero wata waƙa mai dadin gaske yana jinjinawa Sarauniya Diana da kuma sauran jama'ar Ƙasar. Wani abin ban mamaki shi ne, Yayinda yazo daidai gaɓar da yake yabon Sarauniya Diana, sai naji haushin sa ya turnuƙe mun zuciya. Wani ɓangare na ƙwaƙwalwata sai yace "kai hamago ina ruwan ka da ita? Kana fa da budurwa, Sadiya hamago SADIYA! gaba ɗaya wannan fada da kayan alatun dake cikin ta sun sa har na manta ma da maganar Sadiya. Ni dai ban san me ke faruwa ba, amma ji nake yi kamar son Sadiya ya ragu a zuciya ta. Me ke faruwa ne? Na dai share kawai.
Ganin da na yiwa wannan fada yasa na fara shakkar anya kuwa zan fita wurin nan a raye? Ga shi ban ga Sadiya ba a cikin fadar, ko dai sun kashe ta ne? Wani ɓangare na zuciya ta yace 'ka daina wannan mugun tunanin! Daga nan sai na ƙudurta a raina cewa lallai zanyi duk yadda zanyi don in samu damar barin garin nan. Sai dai duk da wannan ƙuduri da na ɗauka, na san cewa in aka yi min wani Rainin wayon komai na iya faruwa, wataƙila ma abinda yasa Sarauniya Diana ta lallaɓe ni kenan, tunda ta san hali na sarai.
Bayan wannan mawaƙi ya gama rero waƙar sa, sai fadar ta sake yin tsit, daga nan kuma sai kowa da ke fadar ya risina bisa guiwar sa yayi gaisuwar ban girma ga Sarauniya Diana. Ya zamana ni kaɗai ne a tsaye cikin fadar. Bayan wani ɗan lokaci, sai Sarauniya Diana tayi gyaran murya. A sannan ne duk jama'ar fadar da suka duƙa ƙasa suka miƙe sannan suka koma izuwa kujerun su.
Bayan kowa ya zauna ne, sai wani Lafcecen Badakare ya daka min tsawa da cewa: "Kai don ƙaniyar baka iya gaisuwa bane?" a zahiri na tsorata da jin muryar Badakaren, amma sai na dake don bai kamata in zama matsoraci ba, ni ne fa HAIMAN! Sai dai kuma bana so in yi abin da zai ɓatawa Sarauniya Diana rai. It's now or never, ya zama dole in yi wani abu.
Maimakon in firgice ko inji tsoro in duƙa inyi gaisuwa a ruɗe, kawai sai na nayi Murmushi sannan na ɗanyi taku uku zuwa gaba Inda za'a fi gani na da kyau na fuskanci mai maganar na fara magana cikin raha ina cewa: "haba bijimi sai kace baka waye ba, ai a matsayina na baƙo kuma mutum mai sauƙin kamata yayi in yiwa Sarauniya gaisuwar ban girma irin wacce ba'a taɓa yi mata irin ta ba! Haba duba fa kaga irin kwalkiyar da tayi wacce nasan ko wata ma da taurari kishi suke yi da ita saboda anfi kallon ta a bisa su, duba fa kaga irin kyawun ta wanda ya zarce tunani, ta yaya kake tunanin zata ji daɗi in an gaishe ta da salo irin na mutanen da wanda an daina amfani da shi da daɗewa? Haba mana ka waye! Ka waye nawa", na ƙarasa maganar ina dariya ciki-ciki. Babu wanda yayi dariya ko murmushi daga cikin jama'ar fadar, hasali ma da yawan su mur suka sha. Sai a lokacin ne na fahimci shirmen da nayi, ta yaya zan zo Ƙasar mutane kuma in kushe musu al'adar da suka daɗe suna yi? Ƙila ma tun zamanin iyaye da Kakanni? Me ke damu na ne? Na dai kanne kawai.
Daga nan sai na nufi inda karagar Sarauniya Diana take kai tsaye, ko da ganin haka, sai wasu ɗirka-ɗirkan ƙarti suka nufo ni da nufin su dakatar da ni, amma sai Sarauniya Diana ta ɗaga musu hannu alamar su ƙyale ni.
Yayinda na iso dab da karagar, sai na tsaya cak, sannan na durƙusa bisa guiwa ta guda ɗaya, na duƙar da kaina ƙasa, sannan na fara magana cikin tausasa murya ina mai cewa: *-" gaisuwa ga Sarauniya Diana, Sarauniyar kyawawan matan duniya, Jarumar gaske, Cikakkiyar mace mai kamala da cikar zati, haƙiƙa na aikata babban kuskure da na yi miki magana cikin rashin ladabi, kuma na san na cancanci kowane irin hukunci kika yanke min, sai dai ya shugaba ta ki sani cewa ni ba komai bane face yaro ɗan mitsili wanda bai san abin da yake yi ba, kuma na jahilci matsayi da ƙimar da kike da su. Da haka ne nake neman afuwa a gare ki yake wannan kyakkyawar Sarauniyar mai cikar halitta- *
Yayinda na zo nan a zance na, sai fadar ta ƙara yin tsit tamkar maƙabarta, aka rasa wanda zai iya cewa komai. Bayan wani ɗan lokaci, sai na ɗago kaina da nufin in kalli Sarauniya Diana. Aikuwa abinda na gani ya bani mamaki matuƙa.
Zan Ci Gaba In Shaa Allaah
_*Phone:*_
08185819176
_*Web:*_ www.haiman.com.ng
_*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees
_*Twitter:*_ @HaimanRaees
_*Instagram:*_ Haimanraees
_*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲
♻♻ *PWA* ♻♻



0 Comments: