Wednesday, 17 October 2018




MIYAR SHUWAKA

Home MIYAR SHUWAKA
MUKOMA KITCHEN 
๐Ÿน๐Ÿ๐Ÿน๐Ÿ๐Ÿน๐Ÿ๐Ÿน๐Ÿ

*MIYAR SHUWAKA*
Ingredients:
* Nama
* Shuwaka 
* Busasshen kifi 
* Albasa
* Tafarnuwa 
* Kayan miya
* Thyme da curry 
* Maggi da gishiri 
* Man ja 

Preparation:
Ki wanke shuwakarki idan ba kya son dacin da yawa, sai ki dinga murje ta kina mutsittsike ta kina tace ruwan da rariya, sai kinyi kamar sau biyar ko sau shida, in kuma kina son dacin sosai sai ki wanke sau biyu ki tafasa namarki da thyme, da albasa da tafarnuwa da gishiri, ki zuba markadadden kayan miyarki da soyayyen man janki a kan tafasasshen namanki, idan ya dahu kamar minti bakwai, sai ki zuba shuwakarki, da gyararren busasshen kifinki, da yankakkiyar albasarki, da maggi, gishiri da curry, ki rufe tayi ta dahuwa, ba'a so ta yi ruwa kamar miyar eto za ki yi ta, amma ki zuba shuwakarki ta ji sosai.

By Ammaterh๐Ÿ’•
MUKOMA KITCHEN 
๐Ÿน๐Ÿ๐Ÿน๐Ÿ๐Ÿน๐Ÿ๐Ÿน๐Ÿ


Share this


Author: verified_user

0 Comments: