Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Babu wani bawa daga cikin bayin Allah,da zai kwanta da tsarki[ alwala] Sannan ya tashi cikin dare, kuma ya roki Allah wani abu daga cikin al'amuran duniya ko na lahira,face Allah ya biya masa buqatarsa.).
# SAHEEHU IBN MAJAH, KUMA ALBANY YA INGANTASHI.
FADAKARWA
Wannan Hadisi yana bayyanama abubuwa kamar haka;
~Muhimmancin kwanciya da alwala,kamar yadda ya tabbata acikin hadisi Annabi s.a.w ya umarci daya daga cikin sahabbansa idan yaje kwanciya barci yayi alwala irinta sallah.......
~Allah yana amsa adduar bayinsa acikin dare,kamar yadda Annabi s.a.w ya kara tabbatar da haaka awani hadisin.
Allah kabamu ikon kiyaye wannan ibada mai tsada acikin dare.



0 Comments: