Wednesday, 7 November 2018




BIRNIN SAHARA 14

Home BIRNIN SAHARA 14

࿐​ *_​PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_* ࿐​

༄༄ *PWA* ༄༄



࿐​❁✹✿​༄✺༄✿​✹❁࿐​
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
     *BIRNIN SAHARA*
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
࿐​❁✹✿​༄✺༄✿​✹❁࿐​          

____________________________________

   ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
         *ѕtσrч/wríttєn ву✍🏻:*
👉🏻© *_Haiman Raees_* ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹

            (℘ᾰ❡ḙ 14)

Ba komai na gani a tattare da Sarauniya Diana ba face abubuwa guda biyu, na farko dai mamaki ne ya bayyana ƙarara a fuskar ta, farinciki da jin daɗi kuma suka bayyana a cikin idanuwan ta. Kada ku tambaye ni ta yaya na gane hakan a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci haka domin bani da amsar da zan baku face in ce muku hakanan dai kawai na gane. Ita kuwa Sarauniya Diana dama can ta ƙware a irin wannan al'amari, domin kuwa ita mace ce mai tarin baiwa da karama. 

Sai dai abinda yafi tayar min da hankali a daidai wannan lokaci shi ne, me ya sa kuma take mamaki bayan ita ta roƙe ni da in kwantar da kaina matuƙar ina so ta cece ni? Ina cikin wannan tunani ne kwatsam sai naji an yi gyaran murya. Hakan ne yasa na fahimci cewa ashe fa tun ɗazu na saki baki ne sakaka ina ta kallon sarauniya Diana. 

Ko da na fahimci haka sai nayi sauri na sake duƙar da kaina ƙasa tare da bada haƙuri. Bayan wani ɗan lokaci sai Sarauniya Diana ta sake yin gyaran Murya sannan ta fara magana cikin wata irin siga wacce babu tausayi kuma babu tursasawa a cikin ta tana mai cewa: "An karɓi tubanka yakai wannan baƙo, sai dai ka da hakan yasa ka fara jin daɗi, domin kuwa laifin da ka aikata ya wuce inda kake tunani. Sai dai da fari, zan so inji ta yadda akayi har ka samu damar shigowa wannan birni namu." 

A yayinda Sarauniya Diana tazo nan a zancen ta, sai na rasa me ma ya kamata inji ne? Farin ciki ko baƙin ciki? Hakanan dai nayi ta maza na sake ɗago kaina ina mai kallon ta ido cikin ido sannan na ce da ita:" ya ke wannan Sarauniya mai karamci, ni kaina ban san yadda aka yi na zo nan ba, ni dai abin da zan iya tunawa kawai shi ne kasancewa ta a gidan biredin da nake aiki Yayinda nake ƙulla biredi a Leda, kwatsam sai naji anyi sama dani an buga da bango daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba sai farkawa nayi na ganni a nan! 

Ina rufe baki kuwa sai boka Nuna'u yayi caraf ya fara magana da cewa; "kai yaro, kada ka raina mana hankali, ko gashin gemu na na san ya haife ka ballantana ni kaina, shin kai a tunanin ka zamu yarda da wannan Tatsuniyar taka ne? Shin me zai hana kawai ka faɗa mana Gaskiyar cewa kai ɗan leƙen asiri ne da aka aiko ka domin ka kwashi sirrin mu ka miƙa shi ga maƙiyan mu domin su zo suga bayan mu?"

Jin wannan magana ba ƙaramin ɓata min rai yayi ba domin idan akwai abin da na fi tsana a duniya, to bai wuce kace nayi abinda ban yi ba. Amma saboda bana son in ɓwtawa Sarauniya Diana rai, sai nayi banza dashi kawai bance masa komai ba, sannan na ci gaba da magana ina mai cewa: 'Wannan shi ne iya abinda zan iya tunawa yake sarauniya mai duniya.' 

Yayin da Sarauniya Diana taji wannan wannan batu nawa sai tayi shiru na tsawon wani lokaci ba tare da ta ce komai ba. Bayan wani ɗan lokaci, sai Sarauniya Diana ta ci gaba da magana ta na mai cewa: "ya kai wannan baƙo, ka sani cewa abu ne mai wahala a samu mutum ɗaya da zai iya yarda da zancenka a duk faɗin birnin Sahara, saboda yau sama da shekaru ɗari da arba'in kenan da kafuwar wannan birni, amma ba'a taɓa samun mahaluƙin da ya shigo cikin sa ba sai kai", ta yaya kake tunanin zamu iya yarda da kai? 

Yayin da Sarauniya Diana tazo nan a zancen ta, sai naji kamar an ɗaura min dutsen Zuma a kaina. Haƙiƙa in dai har sama da shekaru ɗari da arba'in babu wanda ya taɓa shigowa cikin birnin Sahara, to tabbas Sarauniya Diana da mutanen ta suna da duk wata hujja ta tuhuma ta a matsayin ɗan leƙen asiri, to amma ni na san cewa bani da laifi, tunda ko yanka ni za'a yi ban san ta yadda aka yi na shigo birnin nan ba. A dai-dai wannan lokaci ne kwatsam sai wani tunani yazo min, don haka banyi wata-wata ba wurin yin amfani da shi. "Yake wannan Sarauniya mai ƙima, idan har a tsawon wannan lokaci babu wanda ya taɓa shigowa cikin wannan birni, shin kuna da tabbacin in ku kun fita wani ba zai biyo ku a baya ba shima ya shigo? Ina nufin ah... Tun da dai ba za'a rasa ƙofa ba, kenan ai kowa na iya shigowa, menene banbancin nan da sauran garuruwa? Na tambaye ta Yayinda zuciya ta ke riya min "yauwa na kama su". 



Yayinda Sarauniya Diana taji wannan tambaya tawa, sai tayi wani tattausan murmushi wanda yasa har haƙoranta suka bayyana, sannan tace dani; "tabbas akwai banbanci mai girma a tsakanin Birnin Sahara da sauran birane, domin kuwa babu mahaluƙin da ke iya gani ko shigowa cikin wannan birni face sai ya kasance ahalin wannan birni", dangane da shiga ko fita kuwa, ahalin masarautar ce kawai ake barin su suna fita izuwa wasu ƙasashen domin su koyo sabbin ilmomi a fannoni da dama su dawo su koyar da mutanen gari. Don haka babu damar shigowar wani cikin wannan birni. 

Ko da naji wannan batu, sai nan take naji guiwa ta tayi sanyi, domin kuwa bani da wani uzuri da zan iya baiwa mutanen nan har su amince da ni. Don haka, kawai sai na yanke shawarar rungumar ƙaddara tare da miƙawa Allaah komai. Kawai sai na kalli sarauniya Diana na ce da ita: "shin yanzu babu wata hanya da za'a iya bi domin a gano gaskiya ta? 

Ko da gama faɗin hakan, sai mutanen fadar suka fara yi min dariya, wasu ma harda tuntsirowa daga kan kujerun su. Bayan sun ɗau tsawon lokaci suna wannan dariya, sai Sarauniya Diana ta ɗaga hannu sama alamar ayi shiru, bayan kowa yayi shiru sai ta dube ni cikin alamun damuwa tana mai cewa; "Ya kai wannan baƙo, ka sani cewa muna da wata doka mai tsawon Tarihi da muka kafa a wannan birni, wannan doka kuwa itace, duk Mutumin da ya shigo Ƙasar nan da nufin cutar da ko da ƙadangaren da ke cikin ta ne, to nan take zamu yanka shi, duk kuwa wanda ya shigo bisa ɓatan kai ko tsautsayi, to zamu ajiye shi a ƙarƙashin kulawar wani ɗan Ƙasar har na tsawon wata guda kafin mu yanke hukuncin yadda zamu yi da shi", sai dai kuma ba a nan gizo ke saƙar ba, Wajibi ne ga duk wanda zamu aje a cikin wannan birni namu na tsawon waɗannan Kwanaki ya zama ya Ƙware a cikin ɗayan abubuwa uku, Jarumta, Ilimi Ko Kuma Fasaha, idan kuwa har bai yi nasara a ɗayan waɗannan abubuwa ba, to kai tsaye mu a wajen mu bashi da amfani, duk kuwa wanda bashi da amfani a gare mu, to bamu ga amfanin da zai iya yiwa sauran mutanen duniya ba, don haka nan take shima za'a kashe shi. Bisa rashin sa'a sai gashi kun zama mutane na farko da kuka fara shigowa wannan ƙasa tamu don haka kaji abinda zaka fuskanta matuƙar kana so Burin ka ya cika. 

Ko da naji wannan batu sai nayi shiru ina tunanin abinda ya kamata inyi ni dai ban jin kaina, to amma Sadiya fa? Du da cewa babu soyayyar ta a zuciya ta, babu wani mukusanci nawa da ya wuce ta, haka itama bata da wani makusanci da ya wuce ni, lallai ya zama dole a gare ni in san hanyar da zan kuɓutar da mu daga wannan hali da muke ciki, in kuma abin ya ƙi yiwuwa, to ko ba komai dai ita ta kuɓuta. Don haka kawai sai na cewa Sarauniya Diana na amince, 'amma ina neman alfarma guda ɗaya, ina so idan har nayi nasara a Jarabawar da za'a yi min, to ya zamana Nasarar tamu ce nida Sadiya, ita ba sai an jaraba ta ba! 

Yayinda Sarauniya Diana taji wannan kalami nawa, sai ta cika da mamaki, domin su ƴan wannan birni a mafi yawancin lokutta kowa ta kansa kawai yake yi. "Haƙiƙa kana da ban mamaki", Sarauniya Diana ta faɗa fuskarta cike da mamaki, sannan ta ci gaba da cewa; "abinda ka roƙa ba zai yiwu ba, sai dai nayi maka alƙawarin idan har kayi nasara a Jarabawar da za'a yi maka, to zan baka damar sake shiga wata Jarabawar a madadin ta". 

Wannan magana da Sarauniya Diana tayi ba ƙaramin faranta min rai tayi ba, nan take na duƙa bisa guiwa ɗaya nayi godiya, sannan na miƙe cikin izza nace: "Na shirya domin fuskantar wannan jarabawa! 


Zan Ci Gaba In Shaa Allaah 

<><><><><><>>><><><><><><>
___________________________________

●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Haiman Raees_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐 _*Web:*_ www.haiman.com.ng

*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees 

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees 

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees 
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*
Miyan Bhai Ki Daring...

Share this


Author: verified_user

0 Comments: