༄༄ *PWA* ༄༄
࿐❁✹✿༄✺༄✿✹❁࿐
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
*BIRNIN SAHARA*
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
࿐❁✹✿༄✺༄✿✹❁࿐
____________________________________
✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
*ѕtσrч/wríttєn ву✍🏻:*
👉🏻© *_Haiman Raees_* ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
(℘ᾰ❡ḙ 15)
Nan take Sarauniya Diana ta umurci wasu Jibga-Jibgan dakaru da su kawo mata wani abu da ban san ko menene ba. Dakarun basu daɗe ba sai gashi sun dawo niƙi-niƙi ɗauke da wani teburin baƙin ƙarfe, a kan wannan teburi kuwa, wani kasko ne shima na baƙin ƙarfe, Dakarun nan suka zo suka ajiye wannan teburi a gaban Sarauniya Diana.
Daga nan sai Sarauniya Diana ta yiwa Boka Nuna'u izinin Gabatowa gare ta, wato duk wannan abu da ke faruwa fa kada ku manta babu ko ɗaya daga cikin mutanen fadar da yace ƙala, sai dai kawai lokaci bayan lokaci wasun su kan nuna alamun jin daɗi ko rashin sa a fuskokin su. Yayin da Boka Nuna'u ya gabata a gaban Sarauniya Diana, sai ya maida duban sa zuwa ga wannan teburin baƙin ƙarfe yana mai karanto wasu ɗalasiman tsafi waɗanda shi kaɗai yasan abin da suke nufi. Bai jima da fara karanto waɗannan ɗalasiman tsafi ba sai ga wata shuɗiyar wutar ta bayyana a cikin wannan kasko da ke kan teburin, daga nan kuma sai Boka Nuna'u ya fara karanto wasu sabbin ɗalasiman tsafin da ƙarfi tare da ambaton wasu sunaye marasa kamar yaro na Gwalan-gwalan.
Bai daɗe a wannan hali ba sai ga wasu kyawawan fararen duwatsu sun bayyana a cikin wannan kaskon, ba tare da yace wannan wuta tayi musu komai ba. Bayan ya gama wannan surkulle nasa sai yace: "ka zaɓi ɗaya daga cikin waɗannan duwatsu, domin ƙaddararka tana jikin su ne!
Ashe? Na faɗa a fili ina mai ɗaga hannuwa na cikin alamun mamaki sannan na ci gaba da cewa; 'amma dai kana da matsala, idan har so kake yi na zaɓa mai zai hana ka fito da su waje tukun? Okay, kada ka damu wataƙila kaima ba zaka iya bane ko? No problem, I got it', ran Boka Nuna'u nasan in yayi dubu ya ɓaci domin fuskar sa har wani karkarwa take yi saboda tsabar fushi, sai dai kafin yayi wata magana tuni na matsa gaban wannan teburi ya zamana ina fuskantar wannan kaskon baƙin ƙarfe mai ci da wuta.
Bazan ɓoye muku ba a firgice nake, kawai juriya ce saboda all this things that are happening doesn't actually make sense, sai dai kuma babu yadda na iya face in bi al'amuran a yadda su ke. Don haka kawai sai nayi Bismillah sannan na tura hannu na dama cikin wannan kaskon baƙin ƙarfe mai ci da wuta. Bisa mamaki sai naji wannan wuta ko kaɗan bata da zafi, hasali ma wani irin sanyi ne take fitarwa tamkar AC, Oh oh har na tuna da AC, wai shin ma mutanen nan suna da AC kuwa? Bari dai wannan tambaya ce ta wani lokaci ba yanzu ba. Erm... A ina ma na tsaya? Yes! Wuta mai bada sanyin AC, correct. Yayinda na taɓa ɗaya daga cikin waɗannan duwatsun sai naji yana motsi kamar yana numfashi, don haka sai na kauda hannu na daga gare shi, haka nayi ta taɓa waɗannan duwatsu har na rasa wanda zan zaɓa, can sai wata zuciya ta ce min in ɗauki wannan mai motsin in yaso ayi wadda za'a yi ɓera ya ɓaras da garin Kyanwa.
Yayin da na fito da wannan dutse daga cikin wannan kasko sai naji ya daina motsin da yake yi, har da nayi tunanin maida shi sai Boka Nuna'u ya dakatar da ni ta hanyar fisge dutsen daga hannu na, bayan yayiwa dutsen kallon ƙurilla, sai ya fashe da wata irin Mahaukaciyar dariya, sannan ya ɗaga ɗan ƙaramin dutsen sama yana mai ci gaba da ƙyaƙyata dariyar sa. Ai kuwa ɗaga wannan dutse ke da wuya sai ga tambarin Takubba biyu da garkuwa sun bayyana a saman fadar suna ƙyalli, nan take mutanen fadar suka bushe da sowa suna murna kamar anyi musu wani babban albishir. Bayan sun ɗauki wasu ƴan daƙiƙu suna wannan aiki na dariya, sai Sarauniya Diana ta ɗaga hannun ta sama alamar ayi shiru, nan take kuwa fadar tayi Tsit! Kamar an ɗauke Nepa a wajen taron biki. Daga nan sai Sarauniya Diana ta miƙe daga Karagar Mulkin ta, bayan ta ɗan yi zarya na waɗansu ƴan daƙiƙu, sai ta fuskance ni tana mai cewa: "ya kai wannan Baƙo, dutsen da ka zaɓa yana ɗauke ne da ƙaddarar yaƙi, don haka za'a haɗa ka faɗa da ɗaya daga cikin mutanen wannan birni domin a tantance matsayin Jarumtar ka, amma ka sani cewa wannan faɗa da zaka yi yana da doka ƙwaya ɗaya ce tal! Ka kashe ko a kashe ka! A zahirin gaskiya wannan jawabi nata ba ƙaramin tsorata ni yayi ba domin ji nayi kamar in fece daga fadar, sai dai a yayinda take furta waɗannan kalamai, idanuwanta kuma wani labarin suke bani na daban. Labarin dai ya tafi ne kamar haka; "kai Haiman kai dai matsala ne! Kai kasan irin bala'in da ka jawowa kanka kanka kuwa? Yanzu ga shi babu yadda na iya dole in bari kayi wannan faɗa in ba haka ba kuwa jama'a ta zasu yi min bore.
Kada ku tambayeni yadda akayi na fahimci duk waɗannan abubuwa a cikin wannan ɗan lokaci haka, zan muku bayani a gaba, amma wannan yanayi da naga Sarauniya Diana a ciki ba ƙaramin Nishaɗi ya sakani ba, don haka ban san lokacin da na buɗe baki na fara sambaɗa dariya surutu ba ina cewa; 'haha ai Sam kada ki damu Sarauniya komai zai yi daidai, babu wani abin firgici a cikin wannan al'amari haha! Sai bayan da na gama Suburbuɗo waɗannan bayanai ne na fahimci cewa kowa dake fadar fa ni yake kallo cikin alamun rashin fahimtar inda batu na ya dosa, kafin kowa yace komai sai nayi gyaran murya tare da gyara tsayuwa ta nace; 'An gama yake wannan Sarauniya mai Mulkin duniya, tabbas na amince kuma zan kiyaye wannan doka",
Na tabbata Sarauniya Diana itama hankalin ta a tashe yake, amma jawabi na ya ɗan kwantar mata da hankali. Daga nan sai ta bai wa Sarkin Yaƙi Dargazu izinin Gabatowa gare ta. Da fari nayi zaton cewa da shi zata faɗa, don haka sai na fara tunanin cewa anya ma kuwa Sarauniya Diana so take in fita daga wurin nan lafiya? Musamman duba da yadda ya nufo inda Sarauniya Diana take yana wani irin Murmushin mugunta. Na dai kanne ban ce Komai ba.
Yayinda Dargazu yazo inda Sarauniya Diana take, sai ya yi mata gaisuwar ban girma, sannan ya juya zuwa ga sauran jama'ar dake fadar yana magana cikin muryar nan tasa mai kama da ƙarar tashin tifa da cewa; 'ya ku mutanen birnin Sahara, a karo na farko tun bayan hawan Sarauniya Diana karagar mulki yau za'a gwabza yaƙi, kuma a karo na farko tun bayan kafa wannan birni, yau za'a gwabza tsakanin jarumin wani gari can daban da kuma namu na nan kuma a cikin wannan fada ta ƙasarmu mai daraja, lallai wannan faɗa da za'a yi ya kamata ya zama ɗaya tamkar da dubu a cikin Tarihin wannan birni namu. Don haka a matsayina na sarkin yaƙin wannan birni kuma jarumin da babu kamar sa, na zaɓi ƴata Dardira a matsayin wacce zata gwabza da wannan baƙon turmi... Au Jarumi, domin a tantance Jarumtar sa". Ai ko da jin wannan batu na Dargazu sai naji hantata ta kaɗa, Sarauniya Diana kuwa komawa tayi kan karagarta kawai ta zauna cikin alamun karayar zuciya, su kuwa jama'ar fadar sai suka ɓarke da sowa suna murnar faruwar wannan al'amari, a taƙaice dai suna murnar mutuwa ta tun gabanin na mutu.
Ita kuwa Dardira sai ta fito filin fadar tana tafiya cikin rangwaɗa, izza da jiji dakai a lokaci guda, mutane na tafa mata da yi mata kirari. Yayin da ta fito filin fadar, sai Dargazu ya kalle ni cikin Murmushin mugun ta sannan ya kalli Dardira cikin Alfahari yace: 'shin ko akwai wata wasiyya da zaku bayar ko da ɗaya ku ya mutu a sanarwa da ƴan uwansa? Ko da jin haka, sai caraf Dardira ta karɓe da cewa:'bana buƙatar in bar wata wasiyya don nasan babu yadda za'a yi wannan ɗan tamatsitsin yayi nasara a kaina balle har ya kashe ni.
Ko da naji wannan zance sai raina ya ɓaci, zuciyata ta harzuƙa, tabbas ido ba mudu bane amma yasan ƙima, ko da ganin irin ƙirar jikin Dardira nasan ba sai an gaya maka Jaruma bace, amma du da haka bai kamata ace tana wannan cika bakin ba, don haka sai nan take zuciyata ta kwaɗaita min son ganin nayi nasara akanta ko don inga inda wannan jiji da kan nata zai kaita. To amma ta yaya zan iya yin nasara akan ta? A zahiri dai in tsagwaron ƙarfi ake magana to manta ma kawai, nasan ta wuce tunani na, sai dai sa'a da dubara. Yauwa Dabara! To amma wacce dabara zanyi mata?
A dai dai wannan lokaci ne wata shawara ta faɗo cikin raina, sai dai abu ne mai wahala inyi nasara da ita, amma in nayi sa'a, tana iya zamar min abin alfahari, in kuwa banyi sa'a ba, zata sa in zama Bahamage lamba ɗaya. Nan fa na fara tunanin inyi amfani da ita ne ko kuma in sake wata? Ina cikin wannan tunani ne kuma sai ga wata shawarar ta faɗo min daga inda ban taɓa tunanin zata zo ba. Wannan shawara kuwa ta fito ne daga babban jarumin Fina-Finan India wato Shah Rukh Khan, na sani cewa zaku yi makakin ace ina cikin wannan yanayi amma ina tunanin Shah Rukh khan? Well, kada ku damu da wannan, abu mafi muhimmanci shi ne, shawarar sa ta zo min a dai dai lokacin da nake buƙatar ta,
Ga abinda yace;
*take risk in life, if you win you will be happy, if you lose, you will learn*
Haƙiƙa taran aradu da ka shi yafi dacewa da ni a dai dai wannan lokaci tare da fawwalawa Allaah komai. Don haka yayin da Dargazu ya nemi jin ta bakina dangane da wasiyyar da zan bari sai kawai nayi wata dariyar takaici sannan na dube shi ido cikin ido nace;...
Zan Ci Gaba In Shaa Allaah
<><><><><><>>><><><><><><>
___________________________________
●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●
<••••••••••••••••••••••••••••>
👳🏻♂ *_Haiman Raees_* <••••••••••••••••••••••••••••>
*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐 _*Web:*_ www.haiman.com.ng
*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees
*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees
*_"""""""""""""""""""""""_*
🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*
Miyan Bhai Ki Daring...



0 Comments: