Wednesday, 21 November 2018




BIRNIN SAHARA 16

Home BIRNIN SAHARA 16

࿐​ *_​PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_* ࿐​

༄༄ *PWA* ༄༄



࿐​❁✹✿​༄✺༄✿​✹❁࿐​
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
     *BIRNIN SAHARA*
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
࿐​❁✹✿​༄✺༄✿​✹❁࿐​          

____________________________________

   ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
         *ѕtσrч/wríttєn ву✍🏻:*
👉🏻© *_Haiman Raees_* ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹

            (℘ᾰ❡ḙ 16)

Don haka yayin da Dargazu ya nemi jin ta bakina dangane da wasiyyar da zan bari sai kawai nayi wata dariyar takaici sannan na dube shi ido cikin ido nace; "amma kai dai kam Dargazu kana da ban mamaki, a cikin mutane biyu na kasa tantance wanne ne kai, tabbas ko dai kaine jarumin da ban taɓa ganin irin sa ba, ko kuma hamagon da ban taɓa ganin sa ba".

" Me kake nufi da kalmar Hamago ne? Dargazu ya tambaya cikin alamun rashin fahimta.

'Kada ka damu da wannan, ah.. Abinda nake so in tamba a nan shi ne, shin wane irin uba ne zai tura ƴar sa cikin Gasar rai ko mutuwa? Idan har Jarumtakar ka ta gaskiya ce mai zai hana ka gwabza da ni? Amma ai cin zarafi ne a gare ni ka haɗa ni faɗa da mace, su mata ababen so ne, ababen sha'awa kuma ababen Killacewa tare da nunawa kulawa, ba wai ababen turawa inda zasu iya rasa rayukansu ba, ko ka gaji da ita ne kake so ka share ta daga doron ƙasa ta hanyar haɗa ta faɗa da ni? Shin wai ma kasan ko ni wanene kuwa? Waɗannan kalamai nawa sun sa fadar ta ƙara yin Tsit kamar anyi mutuwa, shi kam Dargazu kasa cewa komai yayi saboda rikicewa, ƴar dariyar da yake yi ma a ɗazu yanzu bata, ita kuwa Dardira ranta ƙara ɓaci yayi idanuwanta sun kaɗa sunyi jawur kamar an saka ƙarfe a wutar maƙera, Boka Nuna'u da ke kusa da ni sai yamin raɗa a kunne da cewa: "taka ta ƙare yaro! Ha'a? Seriously wai me nayi wa mutanen garin nan ne ya zamana kusan kowa na son ganin mutuwa ta? Maimakon wannan magana da Boka Nuna'u ya gaya min ta sa na karaya, sai ma ta ƙara min caji, don haka sai na tafi zuwa ga Sarauniya Diana, na ce mata: 'ran ki shi daɗe, this is madness kin san dai irin yadda nake mutunta mata, bai kamata ace wai an rasa namijin da za'a haɗa ni faɗa da shi ba a duk faɗin birnin nan sai mace, please Yallaɓiya ki ce wani abu mana.

Yayinda nazo nan a zance na sai fadar ta sake yin tsit, Yayinda kowa ya zubawa sarauniya Diana Idanu don jin me zata ce, ni kuma a zuciya ta sai nace (yes! Perfect!) so far dai komai na tafiya yadda nake so. Bayan shiru ya ɗan gudana sai Sarauniya Diana ta tace: 'Sarkin yaƙi Dargazu shi ke da alhakin zaɓen wanda zaku kara da shi, idan har ya zaɓi Dardira a matsayin wacce zaku kara da ita, bani da wani ƙorafi, fatar nasara wa mai sa'a! Dakyau, na faɗi a raina, su kuwa jama'ar fadar ba ƙaramin jin daɗin wannan hukunci da Sarauniya Diana ta yanke suka ji ba, don haka sai suka sake ɓarkewa da sowa gami da murna, nima a wannan lokaci murnar nake yi duk kuwa da cewa a zahiri kowa na ganin cewa mutuwata ta ƙarato.

Daga nan sai Dargazu yace in zaɓi irin makamin da nake so inyi faɗa da shi. Kasancewar Mahaifina Sam baya bari na inyi amfani da duk wani abu da aka ce ƙarfe ne saboda wasu dalilai da shi kaɗai ya sani, babu wani makami da na iya Sarrafawa a rayuwa ta face sanda, sandar ma a duk lokacin da zai koya min kari ko duka sai ya bani sandar da tayi min girma sosai ko kuma wacce tayi min kaɗan, a duk lokacin da nayi masa ƙorafi sai yace in yi haƙuri, lokaci zai zo da zan fahimci komai, amma har yanzu lokacin bai yiba. Don haka sai na cewa Dargazu sanda nake so a bani a matsayin makamin da zan yi faɗa da shi. Ko da faɗin hakan sai gaba ɗaya mutanen fadar suka sake fashewa da dariya saboda ganin sokanci na, Dardira da Dargazu da Boka Nuna'u kuwa har suna kifewa saboda tsabar mugunta, ita kuwa Sarauniya Diana Yayinda muka haɗa ido sai tayi min wani irin kallo mai kama da "Kayi Hauka ne?" ni kuwa a wannan lokaci babu abinda nake faɗa a zuciya ta face "He who laugh last, laugh longest"

Nan dai aka sa wasu bayi su ka kawo min wata dogon akwatu cike da sanduna dogaye, Gajeru da kuma Matsakaita don in zaɓi irin wacce nake so. Ko da na nufi inda wannan akwatu take, sai naji wasu kalamai da Mahaifina ya daɗe yana faɗa min su suna zuwa cikin ƙwaƙwalwa ta,

*Kada ka taɓa raina Maƙiyin ka komai ƙanƙantar sa, domin zai iya baka mamaki, kada ka taɓa nunawa Maƙiyinka ƙiyayya a Fili hakan zai sa ya kasa fahimtar ka, kada ka gaza taimakawa Maƙiyin ka a duk lokacin da ya buƙaci hakan, matuƙar ka taimaka masa daga ranar ka zama surikin sa *

Haka dai na ci gaba da tafiya a hankali har naje gaban wannan akwatu, da zuwa sai nayi Bismillah sannan na kai hannu da nufin na ɗauki sandar da ke layin farko, kwatsam sai naji kamar an janyo ni izuwa cikin wannan akwatu, nan take na faɗa kan akwatun Yayinda hannuna kuma ya riƙe wata sanda ram! Mutanen fadar suka ƙara fashewa da dariya, ina jin Dardira tana cewa 'ji yadda yake wani abu sai kace akuya mai ciki', aka ƙara fashewa da dariya. Har ga Allaah naji kunya, to amma sai na wayince kawai na ɗago daga kan wannan akwatu cike da ƙwarin guiwa, hannu na kuma riƙe da wannan sanda.

Bisa mamaki sai naji wannan sanda tayi daidai da ni, ban taɓa riƙe wata sanda da tayi daidai da ni ba sai wannan, in maka ta Thanos yace "Perfectly Balanced". Wani ƙarin abin mamaki shi ne, gashi dai ga dukkan alamu ba da ice aka haɗa sandar ba amma bata da wani nauyin kirki, daidai ni ɗin dai. Nan fa na tsaya ina kallon wannan sanda cikin mamaki domin ban taɓa tsammanin za'a samu wata sanda wacce zata min daidai kamarta ba. Ita dai wannan sanda ba wani tsawo gare ta ba, kuma bata da kauri sosai kuma kamar yadda na faɗa, bata da nauyi. A hankali kuma sai na fara fahimtar cewa akwai wasu ƙananun rubutu a jikin ta. Kafin in tantance zan iya karanta wannan wannan rubutu ko bazan iya ba, sai naji an sake buga wannan ganga mai ƙarfin sauti, take fadar ta ƙara yin tsit, daga nan sai Dargazu ya bada damar a fara wannan faɗa a tsakanina da Dardira.

Dardira ta ja tunga ta yi tsayuwa irin ta manyan jarumai riƙe da wata Sharɓeɓiyar Takobi wanda saboda tsabar ƙyallin ta har kashe min ido take yi. A nawa ɓangaren kuwa, kasantuwar wannan sandar a hannuna ba ƙaramin ƙwarin guiwa ya bani ba, amma saboda in ci gaba da kafcen da na Fara, sai na yiwa sandar riƙon SAKARKARI kuma nayi wata tsayuwa irin ta cikakkun Falalai. Hakan yasa Dardira tayi min wani murmushin mugunta sannan tace: 'sai kayi bankwana da masoyiyar taka kafin ka mutu', na kai duba na inda Sadiya take tsugunne a ɗaure, har yanzu ban daina mamakin yadda naji son ta ya fice min a rai ba saɓanin da da farko yadda nake jinta tamkar ita ce rayuwa ta. Maimakon in ce mata wani abu kawai sai nayi mata murmushi, sannan na juya zuwa ga Dardira nace da ita: 'ina matuƙar tausayin wannan Kyakkyawar fuskar taki, domin zata tafi lahira ba tare da ta shirya ba! Haba! Ashe wannan kalami nawa ya ɓata mata rai fiye da yadda nayi tsammani, don haka kawai sai ta nufo ni da wani irin azababben gudu cike da fushi ta fara kaimin muggan hare-hare ta ko'ina. 


Maganar gaskiya duk inda ake neman mace Jaruma mai ƙarfin damtse da zafin Nama Dardira ta kai, domin kaimin sara da duka take yi ta ko ina, ni kuwa a nawa ɓangaren babu abinda nake yi face gocewa da kuma kare muggan hare-haren da take kawo min. Dardira tana da matsala guda ɗaya wacce ga dukkan alamu bata san da ita ba, matsalar ta ita ce bata da dabarar yaƙi, tsabar ƙarfin damtse da kuma zafin Nama kawai take taƙama da shi, na fahimci hakan ne ta hanyar irin hare-haren da take kawo min ina gocewa gami da kare kaina ba tare da ni na kai mata hari ko sau ɗaya ba, a taƙaice dai ita Attacker ce.

Nan take wasu Kalaman mahaifina suka ƙara kawo min ziyara:

*Cikakken Jarumi shi ne wanda ya ƙware a kowane irin salon yaƙi, kai hari, kare kai ko taimakawa abokan yaƙin sa. Wanda duk ya ƙware a kai hari kawai, to ba zai iya kare kansa ba idan abokin karawar sa ya fishi ƙarfi. Shi kuwa wanda ya saba da kaiwa abokan faɗan sa ɗauki, abu ne mai wahala yayi nasara a faɗan ɗaya da ɗaya. Shi kuwa wanda ya ƙware a kare kai kawai abu ne mawuyaci ya mutu a yaƙi, kuma da wahala yayi nasara, don haka kana buƙatar ka haɗa Dukka ukun, kuma kada ka sake maƙiyinka ya gane ka ƙware a fannonin duka, ya zama Yayinda zai gane hakan, tuni har kayi nasara a kansa*

Hmmmmm nayi murmushi "Allaah Ya jiƙan ka Mahaifina, kana kabari amma kana ci gaba da koya min sabbin Darussa, na faɗi haka a zuciya ta. A dai dai wannan lokaci ne kuma Dardira ta kawo min wani mummunan sara a saitin wuya ta nayi maza na kare, kafin in ankara ta kawo min wani wawan hamɓari da ƙafarta a ƙirji na, nan take naji kamar an buga min gudumar THOR a ƙirji. Ƙarfin dukan ne yasa nayi wata ƴar ƙaramar tafiya daga inda nake naje na bugu da dirkar ginin fadar, nan take kaina ya fashe jini ya fara malala.

Zan Ci Gaba In Shaa Allaah.

<><><><><><>>><><><><><><>
___________________________________

●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Haiman Raees_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐 _*Web:*_ www.haiman.com.ng

*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees 

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees 

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees 
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*
Miyan Bhai Ki Daring...

Share this


Author: verified_user

0 Comments: