π
.
Alherin Allah Ya kai ga iyaye mata Hausawa, wato a kalolin mari da suke bamu muna yara a salonsu na tarbiya. Ciki akwai *TAU*, *TAS*, *RAAM*, *FAYAU*, *FAU* DA KUMA *TARAU*.
.
Wadannan marukan za su sa ka fara tinanin ko dai ba ita ta haifeka ba neππ
.
Shi dai *TARAU* zai sa ka gyara kura-kuranka nan take. π
.
Dadin *TAU* kuwa a take za ka yarda cewar ka yi laifi. π
.
*RAAM* kuwa zai sa ka fallasa duk wadanda kukayi laifin tareπ
.
Amma ka ga *FAU*, a take zai sa ka yi fitsari a wando. π€£
.
Ance *TAS* yafi muni, domin zaisa ka rasa halinda kake ciki, ka fara tinanin ko dai mafarki kake yi neπ
.
Shi kuwa *FAYAU*, lokacin da ka karbe shi za ka kasa tsayawa guri daya, kayinka zai fara yin gabar da yamma kudu da arewa kana neman me ya marekaπ
.
Ka ga idan ta baka daya daga cikin marukan nan, da zaran tace "mu tafi gida"! Za kace "mama gashi nan a aljihuna" π€
.
Allah Ya sakawa iyayenmu da alheri.
.
Don haka duk wanda yaga sakonnan dole ya fadi wane irin mari ya taba karba.............. Ina jiraππ»ππ»ππ»



0 Comments: