_Ke Gabatar Muku Da Shirin_
๐๐ป
*๐DUNIYAR MAKARANTA DA MARUBUTA๐*
๐✍๐ป๐✍๐ป๐✍๐ป๐
๐✍๐ป๐✍๐ป๐
๐✍๐ป๐
๐
TARE DA::::::::::::::::::::_________✍๐ป
*Muhievert India Er India/Er Luv*
```Kamar koda yaushe Shiri ne da yake zak'ulo muku makaranta littattafan Hausa (Hausa Novels) har ma da marubuta litattafan Hausan kansu dan jin ta bakinsu game da abinda ya shafi karatun ko kuma rubutun, A yau ma wannan gida ya zak'ulo muku wani makaranci dan jin ta bakinsa ga kuma yadda hirar ta kasance:```
*BAK'ON AYAU๐๐ปMAKARANCIN LITTATTAFAN HAUSA*
_______________________________
*Ya sunan Malamin?*
_Alhamdulillah Ni dai sunan Abubakar Adam amma anfi kirana da Sadeeq Fulani_
*Masha'Allah malam Abubakar masu karatu zasu so suji d'an taqaitaccen tarihinka*
_Uhmmm Nidai Hafaffen garin kano ne a unguwar DAKATA KAWAJI dake qaramar hukumar NASSARAWA.Nayi karatun firare SAUNA SPS, nayi secondary a GSS KAWAJI yanzu haka ina BUK ina karanta ZOOLOGY wannan shine a takaice._
*Da kyau! Mu shiga cikin shirin kai tsaye, Shin Malam Abubakar Makaranci ne ko marubuci ? Kasan ance magana bakin me ita tafi dad'i*
_Ehh to duka biyun....amma dai yanzu ina kan yin daya daga ciki saboda yanayi na rashin samun isasshen lokaci._
*In na fahimce ka kana so kace kana rubutu kuma kana karatu?*
_Ehh to gaskiya yanzu bana rubutu kamar yanda na fada miki karatu kawai nake amma da na dan ta6a rubutu kafin na watsar_
*Da kyau! Kamar wanne littafi ka tab'a rubutawa?*
_Na rubutu wani dadadden littafi dana sa suna "HABULE" sai "INA MATSALAR TAKE'_
*Su wa 'yan nan littattafai daka rubuta guda biyu shin me suke k'unshe da shi wanne sak'o suke isarwa?*
_"HABULE" littafine na ban dariya da nishadantarwa saboda rayuwa ce wani saurayi dan me son gayu da qarya da son ace ya iya komai.Dayan ko Littafin *"Ina matsalar take"* a tsakanin mahaifansu take kowa baiso dansa ya auri wani iyayenshi suna tsorace masa auren 'yar mai kudi itama iyayenta haka....insha Allah idan na dawo rubutu zan kawo muku saboda yaran sunsha wahala ta ban mammaki a ciki Wannna kenan ya kunshi rayuwar soyayar dan talaka da 'yar mai kudi....shine a cikin littafin rabo ne ya hadasu suna tafiya zasu ABUJA motar ABBAN yarinyar ya samu matsala a cikin daji shine yazo ya taimaka musu shine silar haduwarshi da yarinyar._
*Shin su wa 'yannan littattafai lokacin daka rubuta su a online ka fitar da su ko kuwa bugawa kayi ka shigar da su kasuwa, ko kuma a littafi kayi ka ajjiye ya abin yake?*
_Ehh to gaskiya da yake da jumawa na rubutasu tun ina secondary na rubutasu da biro ne.....ba bugawa nayi ba._
*Za kayi kamar shekara nawa da rubuta su?*
_Zasu kai shekara 15, Amma dayan wajen 2009 na rubutashi_
*Da kyau! daga nan kuma baka sake sha'awar yin rubutu ba ko kuwa ya abin yake?*
_Gaskiya tun daga lokacin na dakatar na koma karatu......amma ba sha'awa na daina ba har yanzu idan da lokaci zan dakko biro na datakarka da shata layi nima._
*Da kyau! Naji kace kana karatun Litttattafai ga kuma karatun boko ta ya kake samun lokaci kake karanta littattafan sauran marubutan?*
_Hahhh ehh to dukda ina cikin yanayi na karutu hakan baya hanani yin karatun saboda tausaya ma masu rubutun bisa namijin qoqarinsu saboda aiki ne bana wasa ba wallahi.....ina karatun ne amma tsakiyar dare daga 12am zuwa abinda ya sauwaqa_
*Toh! Baka ganin a wannan lokacin zaka iya samun damar rubuta naka??*
_Gaakiya ne! Amma dakatar da rubutun dai bisa qashin kaina kamar yanda na fada miki na koma karatu.....amma ina saran insha Allah zan dawo dawowa ta ban mamaki idan na kammala karatuna._
*Zakai kamar shekara nawa kana karatun littafin hausa??*
_kusan 19yrs kenan_
*Lallai ka dad'e kana karatu, Ko zaka iya tuna littafin daka fara karantawa?*
_Bazan iya tuna guda daya ba sai dai wasu da na dan iya riqewa, Kowa rai yaiwa dadi, Izzatu, Inda so da Qauna, Matar Mutum, Sai litatafansu Maqotana kuma Yayuna irin su ,Nazir Adam Salih, Bala Ahmad Maje El Hajij Habib Ibn Hud, dadai sauransu.Amma asali da litatafan yaqe yaqe na kafin daga baya na canja zuwa wannan sashen._
*Da kyau! Cikin littattafan daka karanta wanne littafi ne yafi qayatar da kai, kake ji ina ma kar ya qare,ma'ana wanda yafi yi maka dad'i sosai?*
_wallahi duka litatafan dana karanta sai naji sun qayatar dani....saboda dukkanin wanda zai dau biro da takarda yace zai rubuta littafi to akoi saqon da yake son isarwa al'umma.....shiyasa duk littafin da na dauka da zummar karantawa ina karantawa ne ina nazartar saqon da maruciyar keson isarwa._
*ko akwai wani littafi wanda ka karanta kake ganin akwai kurakuran gyara cikinsa??*
_Ehh to akoi amma basu da yawa sosai.....amma fa anfi samun kura-kuran a litattafanmu na yanzu._
*Kamar wa 'yanne irin kura-kurai kenan?*
_Akoi kura-kurai da dama da nake gani cikin litattafanmu na yanzu musamman na magance matsala a qarshen littafi....wasu marubutan suna qoqarin fito da matsala amma a qarshen wajen maganceta saisu rasa ta yadda zasuyi ma mai karatu yanda zai gamsu sosai. Itace daya daga ciki.....amma mafi akasari idan naga irin wannan matsalar nakam turama marubuci saqo ta waya a matsayina na makaranci don su gyara._
*Da kyau! ya zaka banbancewa sauran makaranta tsarin littattafan baya dana yanzu wanne ne yafi saurin isar da saqo kuma wannene yafi dadi???*
_Litattafan da sunfi saurin isar da saqo amma litattafan yanzu sunfi dadi._
*Mu koma baya kad'an, nasan masu karatu suna nan suna tunanin shin malam Abubakar yana da aure ko kuwa babu, Kuma shekararsa nawa?*
_Hahh! Ehh to babu sai dai niyya, Ban wuce shekara 31 ba._
*Masha'Allah! Naji dazu kana cewa kana karanta littafan yak'i shin tsakanin littafin yaqi dana soyayya wanne yafi dad'i yafi kuma jan hankali??*
_Kowanne da irin nishadantarwarshi amma na soyayya yafi saboda yanzu ba wancan zamanin muke ba......saboda da na yaqin nake karantawa kafin daga bisani na koma na gwagwarmayar rayuwa ta wannan zamanin da kuma hanyoyin magancesu._
*Da kyau! Wanne marubuci ko marubuciya ce tafi burgeka ko yafi burgeka, kuma me yasa suke burgeka??*
_Ba wanda/wadda bata burgeni wallahi kamar yanda na fada muku a baya....kowa ina son tsarin littafansa musamman sabbin marubuta._
*Wacce shawara kake da shi ga marubuta har ma da makaranta??*
_Alhamdulillah bari na fara ta kanmu makaranta saboda sai damu za'a samu marubutan.Garemu shawara shine dan Allah duk mutumin da har ya iya daukar biro da takarka da zummar rubutu mu dinga yi masa kyakkyawan kallo in son samu ne ma mu kallesu a matsayin Malamanmu saboda wata baiwa ce Allah Ya basu ta isar da saqo ga al'umma ta musamman......idan a wajen isar mana da saqon sukai kuskure mubisu da hanyar da suka isar mana da saqon mu tunasar dasu su gyara.....ta haka nake ganin komai zai daidaita a tsakaninmu dasu.Su kuma shawarata garesu shine su dinsa fifita Addininmu da Al'adarmu ta Mal bahaushe fiye da komai......idan wani abu yaci karo da wadannan su daina shigo mana dashi mafi akasari hakan ne ke samar da sa6ani a tsakanin Makaranta da Marubuta.Da fatan idan munji zamu gyara baki daya._
*Me zaka ce game da wannan shiri na Duniyar makaranta da Marubuta?*
_Wallahi abinda zance bashi da iya ka....saboda wannan shiri shine daya tilo da tun lokacin dana soma karance-karance da yake baiwa kowa damar amayarda abinda yake ajiye cikin zuciyarsa shekara da shekaru musamman mu makaranta. Alhamdulillah muna miqa godiya ta musamman ga wadanda suka shigo mana da wannan shirin Allah Ya saka musu da alkhairi.....muna godiya maras adadi_
*Amin. A gurguje ko kana da wa 'yanda zaka gaisar?*
_Gaisuwa maras iyaka ga Mahaifana wadanda silar kyakkyawar tarbiyyar dana samu wajensu ne yasa har wannan shiri ya tsamoni cikin dubban mutane makaranta domin tattaunawa dani Allah Ya saka musu da godan Aljanna.....sai 'yan uwana da masoyana da abokaina na ko'ina musamman 'yan majalisarmu ta "Arab Tea" Ghaza, Mansur, Reenas da irinsu Dini, Auwal fari Mai tarewa dadai sauransu....Allah Yabar zumunci._
《 SAQONNIN MASU KARATU 》
*☎Zainab Zeey Colour:* ```Tambayata ga bakon mu meyasa kace littafin da yafisaurin isar da sako amma na yanzu yafi dadi? Kana nufin na da bekai dadin nayanzuba kuma na yanzu baya saurin isar da sako ๐ค๐ค๐ค```
*๐Abubakar:* _Hahhh! Kusan hakan ne amma bisa fahimtata ta mai nazari akan harkar littafi.....abinda nake nufi kuwa shine da yawan litatafan da marubutansu bayan sun kammala sukan baiwa na gaba dasu ko Malamai su suba musu kafin su fitar dashi to ta haka idan akoi matsala tun kafin ya fita kasuwa suke cireta......amma da yawan litattafan yanzu marubuci shi kadai ne kidansa yayi kuma rawarsa.....amma dukda haka bance babu ba ana yi amma gaskiya ba sosai ba._
*☎Al'amin Japaniz:* ```To Alhamdulillah. Bakonmu kuma dan uwa abokin aiki. Ni tambayata anan. Tunda kafara wannan aiki. Wane littafine akafi tambayarki cigabansa. Ma'ana yafi farin jini.?```
*๐Abubakar:* _in ka koma baya zaka samu amsarka_
*_Muna Godia Malam Abubakar, Wannan ita ce k'arshen tattaunawar mu da Malam Sadiq duk da lokaci ya k'ure bamu gama jin ta bakinsa ba, sai nace kuci gaba da kasancewa tare da ni Muhievert india Er india/Er luv/Er Mumcy/Dad/Er gata.lol duk wanda kuka kira ni da shi zan amsa.......... ku tara wani lokacin dan jin bak'uwar mu ko bak'on mu na gaba cikin dhirin.๐๐ป♀๐๐ป♀๐๐ป♀๐๐ป♀BIIIIIIIIIIIIIIIIIIIISLAM MAKARANTAAAA๐❤_*
{ 18 November 2018 }
{ 10: 31pm to 12:00pm }
*Er India Novels Grp๐✍๐ป*



0 Comments: