_Ke Gabatar Muku Da Shirin_
👇🏻
*📖DUNIYAR MAKARANTA DA MARUBUTA📝*
📚✍🏻📚✍🏻📚✍🏻📚
📚✍🏻📚✍🏻📚
📚✍🏻📚
📚
TARE DA::::::::::::::::::::_________✍🏻
*Muhievert India Er India/Er Luv*
```Kamar koda yaushe Shiri ne da yake zak'ulo muku makaranta littattafan Hausa (Hausa Novels) har ma da marubuta litattafan Hausan kansu dan jin ta bakinsu game da abinda ya shafi karatun ko kuma rubutun, A yau ma wannan gida ya zak'ulo muku wani shahararran marubucin dan jin ta bakinsa ga kuma yadda hirar ta kasance:```
*BAK'UWAR TAMU AYAU👉🏻MARUBUCIYAR LITTAFIN FARAR TAFIYA*
_______________________________
*Ya sunan Malamar?*
_Tohm da farko dai, Assalamu alaikum,Ni sunana Murja Salisu Na'ikke, Haifaffiyar garin jibia ta jihar katsina, Nayi karatu na addini a gidanmu tun daga alkur'ani har zuwa sauran manyan littatafan addini,Nayi karatun boko tun daga nursery har secondary duk anan jibia, Iyakar secondary karatuna ya tsaya saidai muna sa ran cigaba idan ansamu gyaran da aka bukata zuwa next year._
*Allah ya taimaka, mu koma kan abinda ya had'a mu anan wato rubutu, shin taya kika tsinci kanki cikin harkar rubuce-rubuce, me yaja hankalinki har kika fad'a ciki??*
_To alhamdulillahi abinda ya ja hankalina zuwaga rubutu shine: Yawaitar barna ta kowace fuska a zamanin nan ya taka muhimmiyar rawa wajan fara rubuce²na Wanda dama na kasance makaranciya tun ina yarinya daga bayan na fara hankali kuma sai sha'awar rubutun ta fara bijiromin a zuciyata. Ina js3 na fara koyon rubutu ni da kawata so sai muka watsar muka dukufa karatu. Bayan na gama karatun kuma sai na fara gwada sa'ata akan yin rubutun sai kuma Sai kuma naga ya samu kar6uwa_
*Lokacin da kika fara rubutu shin kin nemi taimakon wani ko wata wajen nuna miki hanyoyin da zaki bi??*
_No Kawai kai tsaye na fara abina duk kuwa da cewa abin baqo ne a gareni.So daga baya kuma sai na fara kar6ar gyara daga marubutan da idonsu yake kaiwa ga duk wani motsina._
*Me yafi baki whala a lokacin da kina rubutawa??*
_Toh nikam k'a'idojin rubutu sun fi wahalar da ni domin kuwa alokacin banida kyebord na hausa saidai inyi amfani da hannuna in saka su comma da sauransu a matsayin wadancan._
*Zaki kamar shekara nawa kina rubutu??*
_Cikin shekara ta uku nake_
*Wanne littafi kika fara rubutawa, kuma wanne saqo yake d'auke da shi??*
_Littafin *AMANA* shine na fara rubutawa kuma yana k'unshe da sak'o zuwa ga masu cin dukiyar marayu da kuma tozarta amanar da ake barmusu._
*Da kyau! Bayan kin kammala littafin shin bugawa kika yi ko kuwa a rubuce cikin littafi kawai kika barshi ko a online kika sake shi??*
_Ban buga ba, Na sake shi ne a online kyauta zuwa ga readers_
*Bayan da kika saki book d'in ya karb'uwarsa ta kasnace??*
_Alhamdulillahi, Ya samu kar6uwa sosai_
*Masha'Allah, a shekaru ukun da kikai kina rubutu kamar littafi nawa kika rubuta??*
_Littafin Amana shine na kammala..So sai na dakata da rubutun saboda wasu dalilai ,sai cikin last yamear na dawo aiki wanda shima na biyun ban qarasa ba saboda dalilin da yafi wancan karfi._
*Wanne irin qalubale kika tab'a fuskanta a sha'anin rubutu wanda ba zaki tab'a mantawa da shi ba, walau daga su masu karatun ko kuma 'yan uwanki marubuta???*
_Gaskiya ban fuskanci k'aubale daga kowane 6angare ba, komai ya tafimin yadda ya kamata._
*Idan muka koma baya kaxan naji kince bayan kin gama littafin farko sai kika ajjiye daga baya kika fara wani, in na fahimce ki kina so kice littatafan da kika rubuta guda biyu ne kenan?*
_Yes Biyu ne saboda ni banida ra'ayin saurin rubutu,a ra'ayina inason duk idan na d'ora alk'alamina akan takadda to ya kasance na zazzago ababe masu ma'ana da daukar hankali ba wai inyi saurin kammalawa ba in fara wani._
*Kamar wanne lokaci ne kika samun damar yin rubutu? Kinsan wasu sukance da rana ko da safe ko cikin dare.*
_To Alhamdulillahi.Kinsan abu ga mai iyali,Ina samun nutsuwar yin rubutuna ne bayan sallahr isha'i wato *A cikin dare*😂 kafin bacci alokacin babu aikin komai._
*Hhh lallai kuwa sai kika tunan da A CIKIN DAREE na lol.. Da kyau! shi littafin da kike rubutawa na gaba ko zaki iya fad'awa masu karatu sunansa da kuma abinda yake qunshe da shi??*
_Hhhh.Eh sunansa *FARAR TAFIYA* labari ne da ya k'unshi illolin fyaďe da kuma makomar mai aikatawa,sannan da kuma illarsa ga wanda akayiwa._
*Gaskiya ne, duk da naji kince baki kammala shi ba, shin zaki kammala shi ne nan gaba ko kuwa zaki ajjiye shi ne ki fara wani??*
_Bana fatan ajiyewa,. Idan dama ta samu ko yanzu zan iya cigaba cikin daren nan kafin gari ya waye. Sannan dalilin dakatawar bawai yana nufin dakatawa ba ne,No! Dakatawa ne na wucin gadi inshaallah ku tsumayeni ma cikin satin nan za ku ji ni._
*Allah toh ya taimaka, a cikin littattafanki wanne littafi kika fi so kuma me yasa kike sonsa?*
_*FARAR TAFIYA* Domin kuwa a dalilinsa ne sunana ya shahara a duniyar gizo, a dalilinsa ne nasan ababe da dama wanda bansansu ba. A dalilin farar tafiya nasan meye rubutun shi kansa,wanda a baya yi nayi da ka kamar ina lalube a duhu._
*Gaskiya ne, shin kina da uaban gida ko uwar gida a fannin da ya shafi rubutu??*
_No Ni nake yin abina. Saidai nakan kar6i gyara da shwara daga bakunan sauran manya da k'ananun marubuta._
*Da kyau! Wanne marubuci ne ko marubuciya take burgeki kuma me yasa take burgeki??*
_Fiddausi muh'd Feedohm💧Da Aunty Maimuna Idris sani beli.Salon rubutunsu da kuma irin jigon da suke dauka don yin rubutu akansa yasa bana ganin kowa a duniyar rubutu sai su._
*Menene burunki na gaba kan rubutunki??*
_Burina anan gaba shine Naga na taka matsayin da magabata suka taka sannan rubutuna ya zama fitila wa al'uma wadda zata haska musu rayuwarsu a yau._
*Allah ya yarda, shin zaki ci gaba ne da rubutu iya online ko kuwa zaki runqa fudda shi har kasuwa ne??*
_Inshaallahu ina da burin buga littafi idan Allah ya so._
*Toh! Ya batun da ake fad'a kan marubuta, Wasu makarantan sukance marubuta na da wulaqanci yayin da suke musu magana a online shin mene gaskiyar al'amarin??*
_To a iya sanina da kuma kasancewata acikin marubuta tsawon shekaru ban taba cin karo da wulaqanci ko mai yinsa ba..saidai kinsan ance fahimta fuska.Amma gaskiya marubuta mutanene masu karamci da mutumci da sin farantawa makaranta._
*Masha'Allah! Wanne kalar abinci kika fi so?*
_Tuwon dawa da miyan kuka😁_
*Hhh Da kyau! Toh bangaren abin sha fa??*
_Fura ko farau²😁😁_
*Toh batun kayan sawa fa wanne irin kika fi so da kuma colour??*
_Atampa riga da zani single..inason pink anda pitch colour_
*Wacce shawara zaki bawa makaranta har ma da marubuta??*
_Marubuta muji tsoron Allah mu kyautata alkalaminmu.Mu sani duk abinda muka rubuta fa za'a tuhumemu akansa ranar tsayuwa,Muyi rubutun da zai amfanemu duniya da lahira bawai wanda zamu birge mutane ba a lahira kuma yayimana jagora zuwa wuta.Makaranta ku dinga yimana uzuri sannan ku cire k'azamin tunani daga rayukanku ku fuskancemu ,mu masoyanku ne masu son farinikinku a koda yaushe.Zagi da cin mutumci da post din k'arya har ma da k'irk'irar mutuwar bogi garemu bai kamaceku ba.Ku faranta mana muma mu faranta muku._
*Allah sa sunji, Me zaki ce game da wannan shiri na Duniyar Makaranta da Marubuta??*
_A cigaba da faďaďashi domin shiri ne da ya dauki salon wayarwa al'uma kai gameda abinda ya shafi marubuta da rubutu,Sannan a cigaba da aikashi zuwa lungu da sak'o don marubuta da makaranta su farka su fuskance mu yadda ya kamata._
*Muna godia, ko kina da wa 'yanda zaki gaisar? Dan naga lokaci tun dazu yana ta hararar mu*
Ni kuwa nake da wadanda zan gaisar
Ina gaisheki Ma Muhievert Abdullahi.
Kamala Minna
Jaahid
Khadija Bee²
Kawu Bamai
Fulani Hafsat.
Real ummie xieey
Real Smasher
Habiba Idrees
Rufaida Umar
Fulani Bingel sudan. E.t.c
*_Muna Godia😍, Wannan ita ce k'arshen tattaunawar mu da Malama Murjanatu Na'ikke duk da lokaci ya k'ure bamu gama jin ta bakinta ba, sai nace kuci gaba da kasancewa tare da ni Muhievert india Er india/Er luv/Er Mumcy/Dad/Er gata.lol duk wanda kuka kira ni da shi zan amsa.......... ku tara wani lokacin dan jin bak'uwar mu ko bak'on mu na gaba cikin dhirin.🙋🏻♀🙋🏻♀🙋🏻♀🙋🏻♀BIIIIIIIIIIIIIIIIIIIISLAM MAKARANTAAAA😘❤_*
{ 8 November 2018 }
{ 10: 28pm to 11:58pm }
*Er India Novels Grp📚✍🏻*



0 Comments: