Tuesday, 13 November 2018




TUNA BAYA

TUNA BAYA...


Yau waka ce zana tsara
Don yan Shi'ah sai mu lura
Dole mu kalla don mu gyara
Cikin Yara Manya da Tsara
Babu fada ko aita Sara

Shi musulunci Adali ne
Gun mu Musulmi harda arne
Ku yan Shi'ah sai ku gane
A kauye harda cikin Birane
Kuzo ku zamo tamkar mutane.

Ku bar Shi'ah ku taho ga Sunnah
Ku koyi karatu harda Gunnah
Ku gyara zukata banda 'barna
Zakuyi girbi can a Gona
Nayi nasiha 'yan'uwana

Yanzu ku duba me ya faru
Yan mata shin zasu auru ?
Ba ilimi balle kwararru
Kuna ga hakan zaisa su gyaru
Ko kuma shi zaisa su tsaru ?

A Zaria an kashe rayuka kam
Cikin rafi har can cikin dam
Bazan taba yin Shi'ah ba sam sam
Sojojin da ake kira ARM
Sun kashe Shi'ah sunyi ki-kam.

Zaria ta zam dandalinsu
Yaransu maza har shugabansu
Zakzaky shine mai zigasu
Gashi fa sun rasa rayuwarsu
Rabbi ka taimaki jahilansu.

Basu da kunya kan Sahabbai
Tinaninsu kullun abai-bai
Wai kuma su nan sunyi dai-dai
Ina dai-dai acikin fadin wai
Babu karatu ba Hadisai.

Yanxu Hussainiyya ta rushe
Ba bishiya kuma babu Reshe
Gininta ya rushe babu tushe
Sojoji duk zasu kwashe
Gininta ananne zata washe.

Gani Madina Garin Habibi
Salati naima babu Carbi
Ba tsoro Balle fa Harbi
Da wannan ne zanyo Nasibi
Agunka Ilahi babu gi'bi

Zanyi Du'a'i gun Masoya
Sahabban manzo babu 'buya
A bayyane zanyo babu sanya
Ban shakkar mai yin kiyayya
Inaso in zama mai Biyayya.

Sunyi yawa acikin kasata
Mazansu da yara harfa mata
Suna mutu'a kullun da mata
Su lalata sannan su 'Bata
Sahabbai lallai sunci tuta.

An kashe rai lallai a Gyalle
Masu bakin kaya da kyalle
Sun ta gudu dai harda Tsalle
Zakzaky shine yau a kulle ?
Yaita gudu sannan ya fyalle.

Sufa Sahabbai sunci Riba
Halifofin Manzo ku duba
Ba 'keta kuma babu Giba
Saifa ku daina har ku Saba
Da son Manzo sannan Sahaba.

Baitocina zasu kare
Ban san Shi'ah zaana tsere
Zuwa Sunnah sannan na kere
Duk wani 'daki harda Zaure
Dan fa nazam tamkar kwararre
Dan naci nama har na kware🍗🍗

BY ABUL-KHAYR

Share this


Author: verified_user

0 Comments: