Sunday, 9 December 2018




TATTAUNAWA TSAKANIN MUHIVERT INDIA TARE DA MARUBUCIYAR LITTAFIN GADAR ZARE

Home TATTAUNAWA TSAKANIN MUHIVERT INDIA TARE DA MARUBUCIYAR LITTAFIN GADAR ZARE


*🥀📚ER INDIA NOVELS GRP📚✍🏻🥀*

           _Ke Gabatar Muku Da Shirin_
                                   👇🏻
  *📖DUNIYAR MAKARANTA DA MARUBUTA📝*
                             📚✍🏻📚✍🏻📚✍🏻📚
                                    📚✍🏻📚✍🏻📚
                                            📚✍🏻📚
                                                 📚



TARE DA::::::::::::::::::::_________✍🏻
*Muhievert India Er India/Er Luv*

```Shiri ne da yake zak'ulo muku makaranta littattafan Hausa (Hausa Novels) har ma da marubuta litattafan Hausan kansu dan jin ta bakinsu game da abinda ya shafi karatun ko kuma rubutun, A yau ma wannan gida ya zak'ulo muku wata shahararriyar marubuciyar inda ya gana da ita dan jin ta bakinta ga kuma yadda hirar ta kasance:```
*BAK'UWAR MU TA YAU MARUBUCIYAR LITTAFIN👉🏻GADAR ZARE*
_______________________________


         *Da farko masu karatu zasu so suji sunanki da d'an taqaitaccen tarihinki*
_Assalamu Alaikum ina yiwa masu karatu barka da wannan lokacin, Na farko dai sunana 💥HAUWA A USMAN JIDDARH💥 ('YARBAIWA) 💫_
    _Ni haifaffiyar garin kano ce, a sabuwar k'ofa cikin Kwalli Police Barracks, nayi primary school dina a nan kano stat Momy speed na rik'e labour prefect, sannan na tafi Computer Girls Science Secondary school nayi Candy a 2012 a nan ma labour prefect, sannan na wuce poly katsina na karanci science education, nayi Aure a Katsina state on 04/04/2015 amma Allah bai bani haihuwa ba_

          *Da kyau! Bari mu koma kan abinda ya shafi shi wannan shafi, Shin Malama Hauwa me ya ja hankalinki har kika tsunduma cikin harkar rubuce-rubuce?*
_Eh to ni dai Allah ya sani tun ina JSS2 muka fara ni da k'awaye na amma irin na wasan nan ne, kinga kenan tun ina yarinya nake da sha'awar rubuce-rubuce, kasancewar tun ina yarinya Allah yayi ni mai son karance-karance ce ni amma ba novels ba irin su JIKI MAGAYI, NA GARI NA KOWA, RUWAN BAGAJA, MAGANA JARI CE, DAJI BAKWAI, DARE DUBU DA D'AYA, ILIYA D'AN MAI K'ARFI, KULB'A NA B'ARNA, GANDUN DABBOBI E.T.C Tun ina JSS3 na gama karance su tsaf kuma har yau ina karanta su dan dawuya ki same ni a waje ba 1 daga cikin su, kuma yawancin labaran sunanan a kaima, So bayan nayi Candy na dawo gidan kasancewar bani da wani abunyi ne yasa na fara rubutun novels a not book, kuma Mama na bata hana ni ba wani lokacin ma ita ke k'aramin gwarin gwiwa da ideas idan na kakare kafin nayi aure na rubuta Aminatu wanda a yanzu na canjawa su da WANI AL'AMARI, na ajiye, sai a 2017 na rubuta a media (Online)_

        *Shekara nawa kenan da fara rubutunki a yanzu?*
_A Online dai 1yr kenan amma a not book gaskiya na d'an jima dan tun a shekarar danayi graduate 2012_

        *Wanne littafi kika fara rubutawa??*
_WANI AL'AMARI_

         *Ko zaki iya tuna me littafin yake k'unshe da shi, sannan kuma wanne irin saqo yake isarwa??*
_Gaskiya bazan iya tunawa ba_

          *Nawa ne adadin littattafanki??*
_Guda uku ne_

         *Kamar wanne da wanne?*
_WANI AL'AMARI, K'ADDARA TAH, GADAR ZARE_

          *Da kyau! Idan aka ce ki zab'i littafi d'aya daga cikin wa 'yannan littattafan naki wanne zaki zaki d'auka??*
_GADAR ZARE_

           *Me yasa kika zab'i Gadar Zare, kuma me littafin yake qunshe da shi wanne saqo yake isarwa??*
_Labari ne mai tattare da darasi, nadama, hak'uri juriya, dan ya kunshi cin amana, fansa, k'arya, yaudara, zalunci, k'addara, munafurci, Labari ne akan mutum 6 wad'anda suka had'u da gwagwarmayar rayuwar duniya da kunci had'i da k'uba mai tattare da tarin bak'in ciki da matsananciyar damuwa_

        *Ko zaki d'an gutsirawa masu karatu kad'an daga cikin labarin?*
_Ga kad'an daga cikin labarin nan: A firgice ya mik'e daga inda yake zaune, yana kallon sauran abokanan nasa fuska cike da hawaye idonsa yayi ja sosai Buga kansa ya fara yi ajikin bango yana ihu yana cewa " sun kashe min kowa bani da kowa yanzu, zaman dirshan yayi a k'asa, yana ihu yana yarfa hannunsa, zumbur ya mik'e ya nufi fridge ya d'auko robar ruwa ya bulbulawa kansa "Akan ido na suka k'one gidan mu, mahaifiya ta, mahaifi na, k'anne na duk suka mutu akan kunne na ina jiyo ihun su_
***************
_"Cikin waye wannan a jikin ki? uban waye yayi miki ciki? bazaki fad'a ba saina kashe ki, wayyo na shiga uku duk irin tarbiyyar dana baki abinda zaki saka man dashi kenan, cikin kuka tace " wallahi Aunty ban sani ba, idan za'a kashe ni ban san wanda yayi min cikin nan ba, nima ganin shi kawai nayi ajiki na, tafiya tayi ta bud'e durowa ta d'auko Qur'an ta d'ora akan ta tace " na rantse da wanda raina ke hannunsa bansan wanda yayi min ciki nan ba. Kanta tayo gadan-gadan tana nizaki rainawa hankali, ta shak'e ta idonta suka kakkafe_
**************
_A cikin gidan yarin yake ihu yana kuka yace " sunci Amana ta, sunyi min butulci, na yarda dasu amma sun ci min amana sun had'a min GADAR ZARE, Amintattu nane suka yi silar zuwa na gidan yarin, sun raba ni da kowa nawa sun raba ni farin cikina,cikin matsanancin kuka yace " wallahi koda zan rasa komai na rayuwata bazan kyale su ba.Sun mun sharri, sun had'a man makirci da GADAR ZARE_
*************
_"Koken a cikin kayana kuma, kafin ya k'ara sa maganar dubbun police sun kewaye shi da bindugogi, Ana cikin haka wayarsa ta fara ringing, dakyar ya samu ikon d'agawa, ji yayi muryarsa ta tintsere da dariya yace " nine, d'an uwanka, kaga yadda nayi wasa da hankalinka ko, na nuna maka halin 'yan Adam Cikin rawar murya yace " mai yasa kaci amanata? " saboda ina santa, ita rayuwa tace kuma mallakina , Wani irin mahaucin ihu ya saki tare da buga wayar da k'asa._

         *Gaskiya ne littafin yaci sunan sa gadar zare, to Ya karb'uwar littafin ya kasance a wajen makaranta?*
_Gaskiya tunda na fara rubuta novels ban tab'a yin wanda yakai wannan suna da karb'uwa dan ina groups a k'alla sun kai 6 kuma kullum rububinsa ake_

       *Masha'Allah, wanne irin farin ciki kike ji yayin da kika ci karo da Masu neman littafin?*
_Ina jin farin ciki sosai, amma gaskiya yanzu na gaji da yawan tambayarsa da ake yawanyi daga farko kasancewar abin da yawa dan a kullum sai naci karo da masu so sama da 30_

          *Hakane, shi wannan littafi na Gadar Zare shin kin kammala shi ne ko kuwa kina kan yinsa ne baki gama ba??*
_Ban kammala ba, dan yanzu haka ina kan labarin mutum na uku a page 23 na tsaya_

          *Da kyau! Ko kin samu wani qorafi game da shi wannan littafi ?*
_Gaskiya har yanzu dai ban samu k'orafin komai sai yabo da addu'a da nake samu daga wajen mutane_

          *Mu koma baya kad'an kan d'aya littafin naki na KADDARATA shin shi wannan littafi akan me kika rubuta shi wanne saqo ya isar?*
_Shi k'addara tah nayi shine akan nuna illar k'awaye, Birthday party, da sakacin iyaye, shima ya k'unshi makirci nadama, Ita yarinya ce k'arama take fad'awa tarkon namiji da k'awarta wanda suke had'a baki da saurayin da Kawarta ta suyi mata wayo yayi sex da ita da sunan ya aure ta har ya bata sadaki ashe ciki ya shiga, shi yaron babansa mai mahaucin kudi ne kuma shi kad'ai Allah ya bashi, dan haka uban ya sake shi ya lalace, ita kuma iyayenta masu rufin asiri ne gidan su gidan tarbiyya ne, As end k'awarta ta tayi recording dinsu lokacin da suke sex tayi amfani da video_

        *Marubuta da dama sukan zab'i lokacin da suke jin dad'in rubutu, shin ke wanne irin lokaci ne kike jin dad'in yin rubutu??*
Gaskiya nafi jin dad'in typing da yamma ko da daddare

             *Da kyau! wacece qawarki ko nace Aminiyarki a harkar rubuce-rubuce?*
 Aisha A Bagudu

             *Muje ga tambaya ta gaba, akwai wani sabon tsari da naga kun fito da shi wanda makaranta zasu biya 200 dan samun cigaban litattafanku shin wanne irin hange kukayi akan hakan?*
Hakan dama ce wacce makaranta da kuma su kan su marubuta zasu san darajar junan su, wannan tsarin yana matuk'ar taimakawa sosai wajen kawo rage zagin writers da akeyi Kuma mun fito da wannan tsarin ne dan muka mu amfana da baiwar basirar da Allah yayi mana a duniya, kuma hakan damace muka bawa masoyan mu ta kasancewa tare damu akoyaushe

             *Shin shi wannan tsari da kuka fitar yana nan zaici gaba da tafiya ko kuwa a'a! Iya kan wa 'yancen litattafan da kuka yi kawai zai tsaya, ya abin yake?*
Eh to gaskiya ni kai na ban gama tantancewa ba amma ina san fara fitar novels dina kasuwa

            *Me zaki ce ga makaranta kan shi wannan tsari, Dan wasu da yawa na kokawa kan shi wannan tsari na biyan 200 kafin a karanta book?*
Eh gaskiya sai dai suyi hak'uri dan an riga an tabbatar da tsarin, da dayake suna samu a banza ai shiyasa basu san darajar saba balle mu kan mu susan darajar mu, da a banza suke kallan mu gani sukeyi ma kamar dole typing ya zame mana, dan haka koyaya writers tayi d'an kuskure sai zagi dacin mutunci take samu daga wajen Readers, Kinga kowa yanzu koda zagin mu suke bazamu ci ciwo ba kamar da da muke yin aikin banza ake kuma bin mu da zagi da cin fuska, Yanzu ko zagin mu mutum yayi iyaci nace ya zagi kud'in sa.

           *Hakane,toh me zaki ce game da batun da makaranta suke cewa tun da can da farko me yasa baku fara bugawa kuna siyarwa ba tunda business kuka maida abun sai a yanzu?*
 To kin san Hausawa nacewa ra'ayi riga ne kowa da nasa, tun farko ra'ayin yin hakan ne bai zo mana ba, amma in sha Allah zamu san abinyi

            *Allah ya nufa, wacce marubuciya ce ko marubuci rubutunsa yake burgeki, Kuma me yasa rubutunsa yake burgeki?*
 Gaskiya marubuciyar data burge ni HALIMA ABDULLAHI K/MASHI ce Ina karanta novels d'inta sosai, amma TAWA TA SAME NI & FUSKA BIYU sunfi shiga rai na sosai, dan bata gajiya da karanta su

            *Da kyau! Wanne abu ne yafi baqanta miki rai a cikin wannan harka ta rubutu, kuma me ya fi faranta miki?*
 Abinda yafi bak'anta min rai shine rainin hankalin readers, Abinda yafi kuma faranta min rai shine naji ana yawan zagi na hakan ke tabbatar min da na isa, kuma ana rage min zubaina

          *Wacce shawara zaki bawa marubuta har ma da su makarantan?*
 Shawarata zuwa ga marubuta su daina aikin banza kuma duk da haka ana zagin su ana ciwa iyayen su mutunci duk abinda zasuyi bazai sa su tsira daga zagin readers ba, Makaranta kuma please ku kasance masu hak'uri a rayuwarsu bawai akan d'an abu kad'an su hau suyi ta yawo da dashi a media ana zagi, kullum suyita magana d'aya ba

             *Me zaki ce game da shi wannan shafi na Duniyar Marubuta?*
Gaskiya shafin ya burge ni sosai yana kuma k'ayatar da jama'a, dan mutane da dama saboda wannan shafin suke siyar ita kanta jaridar

               *A gurguje ko kina da wa 'yanda zaki gaisar?*
 Eh, Mahaifiya Fatima Ibrahim Roni, Mahaifi na Auwal Usman Lagosa, Aunty nah, Halima Sulaiman Yak'ub, My Uncle Ibrahim Khalil Amo, My Bro Usman A Usman, And AA MARA Family & Lagosa Family

         *Da kyau! Muna godiya Bisa lokacin ki da kika bamu da fatan in mun kuma nemanki zaki kuma bamu wani lokacin*
In sha Allah ina godiya sosai, Allah ya saka miki da alkhari Ubangiji ya baki miji na gari


*_Amin nagode qarshen tattaunawar mu kenan tare da shahararriyar marubuciyar littafin hausa wato Hauwa A.Usman wadda aka fi sani da 'Yar Baiwa, Sai nace kuci gaba da kasancewa tare da ni Muhievert india Er india/Er luv/Er Mumcy/Dad/Er gata.lol duk wanda kuka kira ni da shi zan amsa.......... ku tara wani lokacin dan jin bak'uwar mu ko bak'on mu na gaba cikin dhirin.🙋🏻‍♀🙋🏻‍♀🙋🏻‍♀🙋🏻‍♀BIIIIIIIIIIIIIIIIIIIISLAM MAKARANTAAAA😘❤_*


{ 09 December 2018 }
         { 05 : 42 pm }


*Er India Novels Grp📚✍🏻*

Share this


Author: verified_user

0 Comments: