Monday, 10 December 2018




YA KAMATA KI GANE WANNAN!

Home YA KAMATA KI GANE WANNAN!
🎍 *YA KAMATA KI GA NE WANNAN* 🎍


🎍➖Da ace mace zata iya bambance tsakanin *haƙƙoĆ™inta* da kuma *Ihsani ko kyautatawa* wanda mijinta zaiyi mata, lallaikam da ta samar da kashi 50% na zaman lafiyar da ake samu a zamantakewar Aure.

🎍➖ *HaƙƙiĆ™in ki* sune abinda zaki riĆ™a bibiya, karki bari a tauyemiki su. Amma *Ihsanin* da mijinki yasabayi miki, liĆ™aci zuwa loĆ™aci, kar kirika É—aukarshi a matsayin *Dole* ko *haƙƙinki* ne sai ya yimiki, wanda kike mayar da shi idan har baiyi miki ba za ki iya cimasa kwala. Wannan fa ganin damarsa ne tare da kyautatawa irin ta zamantakewa.

🎍➖Lallaikam idan *mijinku* yasauke *haƙƙoĆ™in ku* da suke a kanshi, baiyi son kai ki son rai atsakani ba, to sauran kyautatawar da zaiyi muku kuma sunansu *Ihsani*, kuma shi *Ihsanin* ya danganta ne da yadda zai fifita wacce tafi nuna masa kulawa tare da tarairayarsa a matsayinsa na mijinta, wanda yasa zuciyarsa ke Ć™aunarta fiye da ke.

🎍➖ Shari'ah zata tuhumeshi wajan fifita É—aya akan É—aya, wajan tauyewa É—aya haƙƙoĆ™inta, amma *Shari'ah* ba zata tuhumeshi akan fifita É—aya akan sauran wajan *Ihsani* ko yadda zuciyarsa zata *Ć™aunaceta* ba, matuĆ™ar ya biya mata haƙƙoĆ™in da suka rataya akansa.

🎍➖ Za ki iya samarwa da kanki cuta da rashin kwanciyar hankali matuĆ™ar kika dâge akan dole sai mijinki ya nuna miki Ć™auna kamar yadda yake nunaw Abokiyar zamanki Ć™auna, ko dole sai ya ruĆ™a daidaita muku sahu wajan *Ihsani*, ya kamata kisan cewa wannan ganin damarsa ne ba wai haƙƙinki bane, ballantana har kiriĆ™a tayar da jijiyoyin wuya akansu ba. Baiwar Allah hankalinki bazai taÉ“a kwanciya ba, kinyi bankwana da nutsuwa matukar zaki riĆ™a sanya idanuwa akan *Ihsanin* da akeyiwa abokiyar zamanki, abinda yakamata kiyi shine kiyi *Ć™oĆ™arin* karki bari atauye miki *haƙƙinki*, da kuma duban me takeyiwa mijin ne na kyautatawa da har yake kyautata mata sama da ke ? wanda ke ba kya yi masa?

Allah yakyauta kuma yakara tabbatar da dauwamammiyar soyayya tare da tsoron Allah atsakanin ma'auratanmu. Ameenn.

*Idris M Rismawy*

Share this


Author: verified_user

0 Comments: