Assalamu alaikum
Meye hukuncin mutane biyu su kwana a bargo daya.??
AMSA
وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،
Amsar wannan tambaya tana a karkashin wannan hadisi na Abdullai ibn Amr ibn al-Aas (radiyallahu anhu).
```عن ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮﻭ ﺑﻦ ﺍﻟﻌﺎﺹ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ : ﻗَﺎﻝَ ﺭَﺳُﻮﻝُ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ: ﻣُﺮُﻭﺍ ﺃَﻭْﻟَﺎﺩَﻛُﻢْ ﺑِﺎﻟﺼَّﻠَﺎﺓِ ﻭَﻫُﻢْ ﺃَﺑْﻨَﺎﺀُ ﺳَﺒْﻊِ ﺳِﻨِﻴﻦَ ﻭَﺍﺿْﺮِﺑُﻮﻫُﻢْ ﻋَﻠَﻴْﻬَﺎ ﻭَﻫُﻢْ ﺃَﺑْﻨَﺎﺀُ ﻋَﺸْﺮٍ ﻭَﻓَﺮِّﻗُﻮﺍ ﺑَﻴْﻨَﻬُﻢْ ﻓِﻲ ﺍﻟْﻤَﻀَﺎﺟِﻊِ.```
_(ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ (495) ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ "ﺻﺤﻴﺢ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ"
An karbo daga Abdullai ibn Amr ibn al-Aas (radiyallahu anhu) yace; Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) yace; Ku umarci 'ya'yanku da suyi sallah idan sunkai shekara bakwai. Kuma Ku dakesu Idan sunkai shekara goma (basa yin sallah), kuma ku rarraba su a makwancinsu (a raba musu shinfida idan sun kai shekara goma)._
(Abu Dawuda, 495). Albani ya inganta shi a Sahih Abi Dawuda.
```ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﻨﻮﻭﻱ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ:
ﻻ ﻳﺠﻮﺯ ﺃﻥ ﻳﻀﺎﺟﻊ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﻭﻻ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻭﺍﺣﺪ ﻓﻲ ﺟﺎﻧﺐ ﻣﻦ ﺍﻟﻔﺮﺍﺵ ، ﻭﺇﺫﺍ ﺑﻠﻎ ﺍﻟﺼﺒﻲ ﺃﻭ ﺍﻟﺼﺒﻴﺔ ﻋﺸﺮ ﺳﻨﻴﻦ ﻭﺟﺐ ﺍﻟﺘﻔﺮﻳﻖ ﺑﻴﻨﻪ ﻭﺑﻴﻦ ﺃﻣﻪ ﻭﺃﺑﻴﻪ ﻭﺃﺧﺘﻪ ﻭﺃﺧﻴﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﻀﺠﻊ.```
_*"ﺭﻭﺿﺔ ﺍﻟﻄﺎﻟﺒﻴﻦ (7/28)"*_
Imam Nawawi (rahimahullah) yace:
Baya halatta ga namiji ya kwanta tareda namiji (a shimfida guda), ko kuma mace ta kwanta tareda mace (a shimfida guda), koda dayansu yana a gefe daya na shimfidar. Idan yaro ko yarinya suka kai shekara goma, ya zama wajibi a raba yaron (a shimfida) tsakaninsa da tsakanin Mamarsa, Babansa, yar uwarsa (kanwa ko yayarsa), da dan uwansa a wajen barci. (Dole ne ya rika kwana a shifidarsa shikadai).
Rawdatul taalibeen, 7/28).
Saboda haka bai halatta mutum biyu su kwana a shimfida guda idan shekarunsu sun kai goma (10).
* Namiji bazai kwanta shimfida daya da wani namiji ba.
* Namiji bazai kwana da wata mace wacce ba matarsa ba a shimfida daya. Wannan haramun ne.
* Mace bazata kwana da wata mace ba a shimfida daya.
* Mace bazata kwana a shimfida daya da wani namiji wanda ba mijinta ba.
والله أعلم،
**********************************
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
Tambayoyin Musulunci
Whatsapp Group



0 Comments: