Tambaya ta (338)
:
Menene hukuncin Azumin wanda yayi mafarki da rana har Maniyyi yafito masa??
:
Amsa:
:
Dangane da hukuncin Fitar Maniyyi ga wanda yake azumi mafi yawan Malamai cikinsu harda Mazhabobin nan guda huɗu wato:
:
_*→(1)---Malikiyya
_*→(2)---Shafi'iyya
_*→(3)---Hanafiyya
_*→(4)---Hanabila
:
_Dukkansu suntafine akan cewa fitar da Maniyyi da gangan ta hanyar da ba jima'i ba yana lalata azumi, danhaka idan Mai-Azumi yayi Istimna'i, ko ya rungumi Matarsa, ko yayi wasa da'ita, hartakai ga yafitar da Maniyyi to azuminsa ya lalace, danhaka Malamai sukace dukkan Mutumin da yasan cewa Sha'awarsa tana da ƙarfin da indai zaiyi wasa da Matarsa Maniyyi zaifito masa to haramunne agareshi yayi hakan da'ita, idan kuwa yayi har Maniyyi yafita to wajibine sai yarama wannan azumin, amma idan yakasance Maniyyin yafitane ta hanyar mafarki kokuma tunani ko kallon Mace batare da yayi wasa da'itaba, mafi yawan Malamai sukace azuminsa bai lalace ba saidai wajibine yayi wankan janaba, amma Mazhabin MALIKIYYA sukace koda mafarki yayi dolene sai yarama wannan azumin,_
:
_Danhaka Malamai sunyi Saɓani dangane da yanayin ramuwar azumin da Mutum zaiyi, Mafi yawan Malamai suntafine akancewa zai rama azumi guda ɗayane kawai batare da yayi wata Kaffara ba, domin Nassin yin Kaffara yazone akan wanda yayi Jima'i da Matarsa da rana, Saidai Mazhabin MALIKIYYA suntafine akancewa idan Mutum yayi Mafarki har yafitar da Maniyyi to azuminsa ya lalace kuma dolene sai ya rama batare da kaffaraba, amma idan wasa yayi da Mace ya rungumeta ko ya Shafata ko yayi Istimna'i har yafitar da Maniyyi, to wajibine sai yayi ramuwa tare da Kaffara, domin sunyi Ƙiyasine akan hukuncin wanda yayi Jima'i da Matarsa da gangan da rana,
:
_Amma. Mazhabin ZAHIRIYYA suntafine akan cewa wanda yafitar da Maniyyi da gangan ta dukkan wata hanyar da ba Jima'i yayi da Matarsa ba* sukace azuminsa yana nan bai lalace ba, domin babu wata Hujja afili Ƙarara daga cikin Al-Ƙur'ani ko Hadisi datace azuminsa ya lalace, to amma Saidai maganar Malaman da sukace azuminsa ya lalace tafi Ƙarfi,
:
_Amma maganar da tafi inganci wacce mafi yawan Malamai sukafi rinjayar da'ita shine, fitar Maniyyi ta hanyar mafarki baya karya azumi, domin Ɗan-Adam bashi da wani iko na ya'iya hana kansa yin mafarki alokacin da yake barci ba, hakanan magana mafi inganci fitar Maniyyi ta hanyar tunani ko kallo shima bayar karya azumi, amma duk dahaka ba'ace Mutum yarika sanya irin wannan tunanin acikin Zuciyarsa ba, amma fitar Maniyyi dagangan tahanyar wasa tsakanin Ma'aurata, ko tahanyar Istimna'i, wannan kam yana lalata azumi, kuma za'ayi ramuwane kaɗai batare da Kaffaraba, amma idan Mutum yayi jima'i da Matarsa da gangan da rana, tofa koda baikawo Maniyyiba ramuwa da Kaffara sunhau kansa:_
:
(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)
:
ωαηαη sнιηε gωαяgωαdoη ɗαη αвιηdα ιʟιмιη мυ dαкυмα вιηcιкεηмυ үαкαι zυωα gαяεsнι, dαηнαкα ιdαη αηgα ωαηι кυsкυяε αcιкιη αвιηdα мυкα яυвυтα тo αηα'ιүα ғαɗαкαя dαмυ мυgүαяα, тαяεdα кαωo нυננα мαι ƙαяғι:
:
Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:
:
*"المغني لإبن قدامة"
:
*الشرح الممتع" (6/234)
:
*"المجموع للنووي" (6/349)
"""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""
Daga Zauren
Fιƙ-нυl-Iвadaт
""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""
AMSAWA
Mυѕтαρнα Uѕмαи
08032531505
""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє"
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Menene hukuncin Azumin wanda yayi mafarki da rana har Maniyyi yafito masa??
Home ›
Tambaya Mabudin Ilimi
›
Menene hukuncin Azumin wanda yayi mafarki da rana har Maniyyi yafito masa??
Post By:
Hausa Novels
Tambaya Mabudin Ilimi



0 Comments: