SHIN ZAN IYA YIN TSARKI DA RUWAN ZAMZAM?
Tambaya:
Malam wani ya tambaye ni, shin zai iya yin tsarki da ruwan zamzam, saboda ya ji an ce yana kara karfin mazakuta, to gaskiya malam ban sani ba, shi ne na ce bari na tambayi Fukaha'u ?
Amsa:
To dan'uwa ruwan zamzam ruwa ne mai albarka, kamar yadda ya zo a hadisi cewa : Waraka ne ga cututtuka, Suyudi ya kyautata shi a Jami'ussagir, duba Faidhu Alkadeer 3/489.
Saidai duk da haka ya halatta ayi tsarki da shi a zance mafi inganci , saboda ba'a samu dalilin da ya hana hakan ba, ga shi kuma daga cikin ka'idojin malamai duk abin da ba'a samu nassin hani akansa ba a cikin mu'amalolin mutane, to ya halatta.
Sannan sahabbai sun yi tsarki da ruwan da ya bubbugo daga hannun Annabi S.A.W, ruwan zamzam kuma ba zai fi wannan ruwan daraja ba.
Don neman Karin bayani duba: Hashiyatu Ibnu-abiidin 1\180 da kuma Insaf 1\27.
Allah ne mafi sani
Amsawa: Dr Jamilu Yusuf Zarewa.
Gabatarwa: Abu-Unaisa.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________
» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).
→ Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu *(07036073248)* ta whatsApp.



0 Comments: