Monday, 16 October 2017




MALAM MENENE HUKUNCIN WANDA YAKALLI BLUE FILM (BF) DA RANA YANA AZUMI HAR YA FITAR DA MANIYYI KUMA BAIYI WANKABA HAR SALLOLIN AZAHAR DA LA'ASAR SUKA WUCESHI???

Home MALAM MENENE HUKUNCIN WANDA YAKALLI BLUE FILM (BF) DA RANA YANA AZUMI HAR YA FITAR DA MANIYYI KUMA BAIYI WANKABA HAR SALLOLIN AZAHAR DA LA'ASAR SUKA WUCESHI???

MALAM MENENE HUKUNCIN WANDA YAKALLI BLUE FILM (BF) DA RANA YANA AZUMI HAR YA FITAR DA MANIYYI KUMA BAIYI WANKABA HAR SALLOLIN AZAHAR DA LA'ASAR SUKA WUCESHI???

                           Tambaya

Malam minene hukuncin wanda ya kalli Blue Film (BF) da rana yana Azumi har ya fitar da Maniyyi kuma baiyi wanka ba har Sallolin Azahar da La'asar suka wuce shi???

Domin naji kace wanda yayi mafarki da rana yafitar da maniyyi azuminsa yananan.‎ Shima wannan kenen a zuminsa yananan?

                              Amsa

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN. Lallai wannan kayi babbar ta6argaza. Bakada azumi sannan sai kayi kaffarar guda sittin (60) duk da wanda kakarya zakayi (61) kenan babu hutu.
Domin wannan ba uxury bane a wajen Ubangiji gangancine kayi. Koda mai matar aure ta sunnah an haramta masa ya sadu da ita da rana acikin watan azumi, sai yayi kaffara.
.
.
.
Balantana kai daka tafka sa6on Allah kana kallon kafirai maqiya Annabi Muhammad (S.A.W) suna tafka Masha'a har kafitar da maniyyi, sannan kake taqama da wanda yayi mafarki da rana.
.
.
.
                  HUJJA ANAN ITACE:

Duk wanda yake bacci baisan a inda yakeba, hankalinsa baya tare dashi, sannan koda wani abu zai sameshi acikin baccin nasa bashida ikon kare kansa kamar yadda zai iya a zahiri.

Kamar yadda yazo a hadisai cewa: An dauke alqalamin rubutun zunubi akan mutum uku (3).
1. Qaramin yaro.
2. Mahaukaci.
3. Maiyin bacci har saiya farka.
Wadannan mutanen dukansu hankalinsu baya tare dasu.

Amma banda wanda yasha giya yafita daga hayyacinsa, domin wannan shine yajawa kansa. Saboda haka zaka rama azumi guda (61) bayan sallah.
.
.
.
.
Sannan inajan kunnen matasa maza da mata suguji yin (Chatting) a cikin watan azumi saboda gudun afkawa fitina irin wannan.

Allah ka shiryi matasanmu maza da mata ka aurar dasu ga ma'aurata nagari.

Rubutawa:- Ãbûbäkår Êkâ.

______________________________________

» Zauren SHEIKH JAFAR MAHMUD ADAM

Share this


Author: verified_user

0 Comments: