WANDA AKA YIWA KYAUTA BAI AMSA BA, HAR YA MUTU, SHIN ZAI SHIGA RABON MAGADA?
Tambaya
Assalamu alaikum. Dan Allah Ga wata tambaya ta gaggawa. Wata baiwar Allah ta sayi kaya da niyyar baiwa 'yar uwarta, amma kafin ta bata sai 'yar uwar ta rasu. Shin wannan sayayya ta shiga cikin kayan gado? Na gode.
Amsa
To dan'uwa ba zai shiga rabon magada ba, saboda kyauta ba ta tabbata sai an amsa, Wannan ya sa lokacin da sayyadina Abubakar ya yiwa 'yarsa Aisha kyauta ba ta amsa ba, Har mutuwa ta zo masa ya soke kyautar, ya mayar da ita dukiyar magada. Kamar yadda Malik ya rawaito a Muwada'i a hadisi mai lamba ta: 717.
Wannan ita ce maganar mafi yawancin malamai.
Don neman Karin bayani duba : Al'umm na Shafi'I 4\64, da Bada'iussana'i'i 6\8.
Dr. Jamilu Zarewa
13\4\2015
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________
» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).
→ Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu *(07036073248)* ta whatsApp.



0 Comments: