Tuesday, 3 October 2017




Shin Mace zata rama sallar Maghrib da Isha'i idon Jini ya dauke mata kafin hudowar alfijir,?

Home Shin Mace zata rama sallar Maghrib da Isha'i idon Jini ya dauke mata kafin hudowar alfijir,?

Tambaya

Assalamu alaikum

Shin Mace zata rama sallar Maghrib da Isha'i idon Jini ya dauke mata kafin hudowar alfijir,?

Ko idon ya dauke mata kafin faduwar Rana zatayi sallar Azahar da La'asar?

ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﻜﻴﻢ ﺍﻟﻌﻠﻴﻢ .

Amsa:

Idan mai haila taitsarki bayan shigar lokacin sallar isha'i wajibine tayi sallar isha'i din domin tariski lokacinta, haka zatayi sallar magariba domin ana hadasu yayinda aka samu uzuri.
Hakanan idan tai tsarki bayan shigar lokacin la'asar zatayi sallar la'asar da azahar, wannan shine abunda wasu daka cikin shabban Annabi sallallahu Alahi wasallam sukai fatawa dashi, shine kuma abunda jamhurdin malamai sukai fatawa dashi.
Amma idan tai tsarki bayan sallar asuba, ko sallar azhar, ko sallar magariba baztai wata sallah ba sai guda daya kawai, itace sallar datai tsarki acikin lokacinta, ( Asuba ko azahar ko magariba) domin wadannan sallolin ba'a hadasu dawani abu dayake kafinsu.
Ibnu qudama rahimahullah acikin Almugni ( 1/238) yace: Idan mai haila tai tsarki kafin rana tafadi zatai sallar azahar da la'asar,
idan tai tsarki kafin hudowar alfijir zatai sallar magariba da isha'i, anruwaito wannan daka Abdurrahman bin Auuf, da Abdullahi dan Abbas, da dawus, da Mujahid, da Annaka'i, da zuhuri, da rabi'ah, da malik, da lais, da shafi'i, da ishaq, da Abissauri.

Imamu Ahmad yace: gaba dayan tabi'ai sunyi fatawa da wannan maganar sai hasanul basari shi kadai yace: abunda ya wajaba agareta shine sallar datai tsarki acikin lokacinta kawai, itace fatawar sauri dalibansa, domin lokacin sallar farko yafita lokacin tanada uzuri, saboda haka bata wajaba akantaba.
An ruwaito daka malik cewa idan tariski lokacin sallah tabiyu gwar-gwadon yanda zata iyayin raka'a biyar lokaci baifitaba, sallar farko tawajaba agareta, domin gwar-gwadon lokacin raka'a daya shine lokacin sallar farko ahalin uzuri, tawajaba akanta da riskarsa, kamar yanda zata risketa afarkon lokacinta.

Asram da ibnu munzir sun ruwaito daka Abdurrahman bin Auuf da Abdullahi dan Abbas sunce: Idan mai haila tai tsarki kafin hudwar alfijir da gwar-gwadon lokacinda zata iya raka'a daya , zatai magariba da isha'i, idan tai tsarki kafin faduwar rana zatai azahar da la'asar gaba daya, domin lokacin sallah tabiyu shine lokacin tafarko ahalin uzuri, idan mai uzuri yariskeshi wajabcinta yakamashi, kamar yanda wajabcin ta biyu yahaushi.
Wasu malaman kuma sukace: babu abunda zata rama sai sallar data riski lokacinta kawai, amma wacce lokacinta yawuce bazata rama taba, shaik usaimin rahimahullah yarinjayar da wannan maganar takarshe.

Abunda yafi shine aiki da fatawar jamhur din malamai, zatai sallah biyu ahade, bazata rama dukkan sallolin wuni ba, idan kuma tarama iya wacce tariski lokacinta Ana fatan babu komai akanta.

Wallahu A'alam

ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ .

Share this


Author: verified_user

0 Comments: