LIMANCIN KURMA!!!
Tambaya
Assalamu alaikum, malam menene hukuncin bin kurma wanda ba ya ji sallah?
Amsa
Wa alaikum assalam To dan'uwa limancin kurma bai inganta ba, harma wasu malaman sun hakaito ijma'i akan haka, saboda kurma ba zai iya tsayar da wasu daga cikin rukunan sallah ba, kamar kabbarar harama da karatun fatiha da sallama, don haka binsa sallah zai jawo sallar wadanda suke binsa ta zama ba ta cika ba.
Saidai wasu malaman sun tafi akan cewa, ya halatta ya yiwa kurame irinsa limanci.
Allah ne mafi sani.
Don neman Karin bayani duba : Sharhul-kabir na Abdurrahman dan khudaamah 2\38.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
15\2\2015
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).
→ Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.



0 Comments: