TAMBAYA TA 947: 🕋🕋🕋
lDAGA ZAUREN
MATA MUMINAI
Assalamu alaikum
Malam macece ke haila Har yakai wata daya yana zuba Sai ya Dauke daga bayan ya dawo yanamata wasa da hankali Kuma jinin ya koma baqi hadda ciwon mara Taje asibiti andubata antabata magani Amma Har Yanzu bai denaba pls ataimaka mata da wata hanya in akwai
AMSA
```WA'ALAIKUMUSSALAM....```
Kibi daya dagacikin wadannan in sha Allah zaki samu sauqi:
Kisami Zuma ki zuba acikin Ruwa me zafi na qaramin kofi se ki karanta ayoyin RUQA aciki seki zuba Garin barkono rabin qaramin cokali seki Sha sau 2 ko 3 Arana Alokacin da Al'adan take zuwa, kidinga Sha sau 1 kuma idan ba lokacin Al'adabane.
Kisami Ruwan Sanyi ko qanqara kisa a tsumma ko a leda kisashi aqasan cikinki na tsawon Minti 20, sannan se ki dunga samun guri ki huta seki dunga Mai-maita haka aduk bayan awa 4. Kuma kidinga yawan shan Ruwa me Sanyi tare da karanta wadannan ayoyin ruqan aciki. Kidimga yin wannan a ranakun Da Al'adan yake zuwa.
Kina iya samun qaramin kofi na Ruwa ki zuba Ruwan Apple kaman qaramin cokali 1 ko 2 karki tace duddugan seki hada da zuma ki dunga karanta ayoyin Ruqa aciki kisha sau 3 aranakun da Al'adan yake zuwa.
Yin amfani da abubuwa masu vitamin C kaman lemun tsami(amma in akasha dayawa yanakawo ciwon kaman gudawa), dakuma motsa jiki duk yana kawo rage zuban Al'ada.
Allah yasa mudace.
.
.
Amsawa:
Malam Yusuf Salisu Kaduna
Via MATA MUMINAI 📚
+2348108407420
+2347033537189
+2347035269582
Domin kasancewa damu ta shafinmu na facebook se abi ta wannan hanyar a shiga ayi like
https://www.facebook.com/MATA-muminai-1841397762846865/
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.
Subhanakallahumma wabihamdika ash hadu anla ilaha illa anta astagfiruka wa'atubu ilaika".



0 Comments: