:
Assalamu alaikum
:
Wai dan Allaah dolene idan mace zatayi wankan haila sai ta tsefe kitson dake kanta?
:
Amsa
:
Wa alaikumussalam
:
Gaba dayan Malaman fiqhu sunyi ITTIFAQI akancewa wajibine akan mace ko namiji idan yazoyin wankan tsarki yagame dukkanin kansa da ruwa cikinsa da wajensa, saboda fadin Manzon Allah(ﷺ) cewa:
:
إن تحت كل شعرة جنابة، فاغسلوا الشعر وأنقوا البشر، (رواه أبو داود)
MA'ANA:
Lallai akarkashin kowanne gashi (na jikin mutum) akwai janaba, danhaka kuwanke kai kuma kutsarkake (wanke) fata,
:
To amma dangane da maganar kwance kitso alokacin wanka mafi yawa daga cikin Malaman Mazhabobin MALIKIYYA, SHAFI'IYYA, HANAFIYYA, suntafine akancewa indai har mace zata zuba ruwa kuma yashiga cikin kanta sosai to badole bane sai takwance kitson dake kantaba, amma idan ruwan bazaisamu damar shiga cikiba inba'a kwanceba to anan yazama wajibi akanta saita kwanceshi,
:
Amma Mazhabin HANABILA sunsabawa wannan fahimtar, domin kuwa cewa sukayi wajibine sai mace takwance kitson dake kanta idan zatayi wankan haila dana biki, amma bazata kwanceba idan awankan janabane, hujjarsu tacewa dolene sai ankwance kitso, shine hadisinda Manzon Allah(ﷺ)_ Yaceda A'ISHA:
:
*إنقضي شعرك واغتسلي، (رواه إبن ماجه)
MA'ANA:
Kikwance kitsonki sannan kiyi wanka,
:
To amma mafi yawan malamai sundauki wannan hadisine amatsayin cewa MUSTAHABBINE_ kwance kitso, domin wannan hadisin na A'ISHA acikinsa babu hujjar cewa wajibine saboda bawai alokacin wankan haila bane Annabi(ﷺ) yace da'ita haka, yafadi hakane alokacin datake cikin harama da aikin hajji amma tana al'ada:
:
Danhakadai Malamai sukace magana mafi inganci itace MUSTAHABBINE kwance kitso amma ba WAJIBI BANE, domin babban abinda ake bukatadai shine ruwa yasamu shiga cikin kai sosai yadda zaitaba fatar kai shikenan wanka yayi, domin koda mace ta tsefe kitsonta indai bata zuba ruwa yashiga cikin kantaba to wankanta baiyiba, danhaka bawai tsefewar ake kalloba, shigar ruwa cikin gashi ake kallo, idan yazamana ruwan bazaishigaba harsai in antsefe to anan tsefewa tazama wajibi kenan,
:
Mai neman karin bayani sai yaduba wadannan litattafai kamar haka:
_↓↓↓_
:
*المجموع (1/215)
:
*المغني (1/1257)
:
*الإنصاف (1/1256)
:
*بدائع الصنائع (1/34)
:
WALLAHU A'ALAMU
DAGA ZAUREN
FIQHUL-IBADAT
Rubutawa:
Mustapha Usman
Ga masu sha'awar shiga zauren_
FIQHUL~IBADAT sai su aiko da cikakken sunansu ta Whatsapp zuwaga wannan lamba.
:
Mustapha Usman
+2348032531505
:
*_
Domin samun shafinmu dake FACEBOOK sai ashiga wannan ↓link kawai ayi ""LIKE""
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/



0 Comments: