*_KARFE NAWA LOKACIN SALLAR AZUHUR KE FITA?_*
*Tambaya*
Assalm mallm da Allah karfe nawa lokacin sallan Azahar ke fita ?.
*Amsa:*
Wa'alaikum assalam, zababben lokacin Azahar (Muktari) yana fita ne idan tsawon kowanne Abu ya yi daidai da shi. Lokacin masu uzuri (Dharury) na sallar azahar yana karewa idan rana ta fadi.
Shari'a ba ta rataya lokutan sallah da karfe nawa ba, ta rataya su ne da álamomin yanayi kamar yadda aya ta: 78 a Suratul Isra'i ta tabbatar da haka.
Wannan ya sa babu Wata sallah da za'a iya sanya lokacin shigarta ko fitarta na din-din da agogon da muke amfani da shi a yanzu, saboda karfe da mintuna suna iya sabawa da yanayi dağa wani watan zuwa wani, misali wani lokacin rana ta kan fadi bayan karfe biyar, wasu lokutan kuwa sai bayan karfe bakwai, wannan yasa fahimtar shigar lokutan sallah da fitarsu ta hanyar alamomin da sharia ta sanya yake da muhimmanci.
Allah ne mafi sani.
25/01/2016.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.



0 Comments: