*_RUBUCACCIYAR TAMBAYAR SHEIK JAFAR MAHMUD ADAM RAHIMAHULLAH_*
*Tambaya*
Assalamu Alaikum, Malam shin menene matsayin Auren Dole, idan aka yiwa yarinya in taqi auren matuqa tace ita bazata yarda ba, shin taqi biyayya ne ga iyayenta, ko kuma shin ta sabawa Allah da Manzonsa?
*Amsa*
Wa'alaikumus Salamu Warahamatullah Wabrakatuhu.
To wannan bata sabawa Allah(SWA) kuma bata sabawa Manzon Allah ba, idan aka miki auren dole bakyaso kikace bazaki yarda ba, ba wanda kika sabawa, yanzu iyayenki basu da 'yanci da zasu miki auren dole, Manzon Allah ﷺ ya hanasu, yanzu sune suka sabawa manzon Allah da sukayi miki auren dole, ya kamata iyaye susan wannan, wai shin ma, menene kukeso da auren dole, wai shin so kuke 'yarku taje ta dawo-taje ta dawo, ku dai so kuke ta zauna, abin da iyaye bakwa ganewa idan yarinyaku taqi mutun, wallahi ko mutun shi AMIRUL MUMMININA ne shi, in Mace bata sonsa bazata taba masa da'a ba, dalili kuwa shine;
Hakan tafaru da Manzon Allah ﷺ, ya auri wata mata, bayan ya aureta, yasa aka kaita wani gidan gona, bayan an kaita ya shiga inda take tana zaune yace baza kizo ba, sai tacewa manzon Allah, a'a sai dai kai kazo nan gun, sai manzan Allah ya matsa kusa da ita, ya daga hannusa zai dora akanta sai tace masa "A'UZU BILLAHI MINKA" sai manzon Allah yariqe hannusa, bai dora hannunsa a kanta ba, sai yace mata kin nemi tsari ga wanda ake neman tsari gashi, shike nan tashi kitafi gidanku, shike nan sai manzon Allah ya saketa.
Hadisi nagaba, an sami wata yarinya: Iyayanta da suka aurar da 'yarsu atilas wanda taje ta fadawa manzon Allah ﷺ sai ya bata zabi in kinga dama ki zauna, in kinga dama akashe auren, sai tacewa Manzon Allah ﷺ zanyi haquri na zauna, dama nazo ne inma wannan tambayar kafadi amsar, dan iyaye susan basu da ikon tilassawa 'yarsu auren wanda bataso, hadisine ingaccece
Hadisin Mugid da Barira, Barira baiwace ta Nana Aisha, tana da mijinta mai suna Mugid, sai auren su ya mutu, mugid yana matuqar son barira, barira tana matuqar kin mugid, idan yana zaune ta wuce idonsa akanta har sai ya daina ganinta,, har Manzon Allah ﷺ yake cewa Abdullahi Bn Abbas, baka mamakin inda Mugid yakeson Barira, ita kuma tana matukar kinsa, Abdullahi Bn Abbas yace wallahi nakula, Manzon Allah da kansa daya tausaya masa yaje gidan barira, manzon Allah yana da ikon da zaice tazo gidansa, amma da kansa ya tashi yaje inda take yace barira abin daya kawoni wajanki na zo ne danmu tattauna akan aurenki da mugid, sai ta sunkuyar da kanta tayi shuru, sai tacewa manzon Allah Umarni kake bani ko kuma kana bani shawara ne, manzon Allah yace a'a shawara nake baki, sai tace to bana sonshi. Ma'ana inda umarni yake bata dole ne, tabi umarnin manzon Allah, amma tunda shawarace tace bazan aureshi ba, haka aka hakura, Yadda manzon Allah yaji tausayin mugid da sai ya matsawa barira sai ta aure shi, tunda Manzon Allah ﷺ hakin da yake da shi akanka, akaina, yafi hakin da iyayenmu suke dashi akanmu.
Dan haka iyaye akiyaye da yiwa 'yaya auren dole, duk wanda yarinya bata sonsa, ya takura mata ya aureta wannan baisan mai yake ba gaskiya, Anan zamu dakata, sai kuma fitowa ta gaba
Rubutawa:- Sani Muhammad Olan (Diyayi)
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.



0 Comments: