🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲
♻♻ *PWA* ♻♻
_08185819176_
••••••••••••••••••••••••••••••
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
*BIRNIN SAHARA*
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
••••••••••••••••••••••••••••••
________________________________________
_______________________
*ѕtσrч/wríttєn ву✍🏻:*
👉🏻© *_Haiman Khan Raees_*
(℘ᾰ❡ḙ 5)
Banyi aune ba sai kawai naga sun jata zasu koma da ita, shi kuma shugaban dakarun babu abinda yake yi face ƙyalƙyala dariyar mugunta.
Nan take naji wani irin baƙin ciki ya lulluɓeni, ban san lokacin da nayi wata kururuwa mai matuƙar firgitarwa ba, kururuwar tawace tasa gabaki ɗayan sauran fursunonin dake ragowar ɗakunan suka nufo baƙin ƙofar ɗakunan su don ganin mai zai faru. Su kuwa dakarun dake ɗauke da Sadiya tsayawa suka yi cak tamkar an zare musu laka a jikinsu.
Shi kan shi shugaban dakarun sai daya ɗan dakata da dariyar da yake yi sannan ya juyo ya kalleni. A wannan lokaci idanuwana sunyi ja tamkar an gasa Ɗan_Buda a wuta saboda tsabar fusatar da nayi. Mukayi musayar kallo a tsakanin mu, duk da cewa akwai 'yar tazara a tsakanin mu, amma hakan bai hanani jin fitar numfashinsa da sauri da sauri ba. Cikin Fusata na ce dashi:
''kai gafalalle , fanɗararre mara tausayin al'umma. Ka sani cewa sai a yanzu ne na fahimci cewa duk wannan girman jikin naka ya tashi a banza tunda ka kasa tausayawa macen da koda kun sake ba zata iya taɓuka komai ba sakamakon wahalar da ta sha a hannunku, lallai halaka zata wanzu a gareka matuƙar ka sake muka gamu dakai, wawa girman banza kawai,''
Waɗannan kalamai nawa ba ƙaramin Harzuƙa shugaban 'yan fashin tayi ba, musamman ma da yake ganin cewa ya ninka ni girma kusan sau huɗu, don haka sai yayi umurni da a fito dani daga ɗakin da nake.
Koda jin wannan umurni, sai ɗaya daga cikin dakarun da ke take masa baya ya ce: ''Ya shugabana, ka sani cewa mai girma Diana bata bamu umurnin fito da Haiman ko taɓa lafiyarsa ba, don haka ni ina ganin fito dashi tamkar siyowa kanmu ajaline, mai zai hana ka ƙyaleshi in yaso a ranar da za'a gabatar dashi a gaban sarauniya sai ku gabza yaƙi da shi? Koda jin wannan batu, sai jikin shugaban dakarun yayi sanyi. Bayan wani ɗan lokaci sai ya dube ya ce dani: ''A duk faɗin rayuwata kaine mutum na farko daya fara kirana da wawa kuma banza, a duk faɗin garin nan babu wanda baya shakkata walau daga jarumai ko attajirai amma sai gashi yau fursina ya kirani da waɗannan miyagun kalmomi,'' Lallai ka aita laifi mafi girman muni a gareni, kuma daga yau ka ƙulla gaba mai tsanani a tsakanin mu, kuma nayi maka alƙawarin nine sanadiyyar salwantar rayuwarka dama ta duk wani wanda kuke da alaƙa dashi koda kuwa ta zaman ɗaki ɗayane a kurkuku,''
Koda yazo nan a zancensa, sai ya juya ya fice daga sashin mu, yayin da ragowar Dakarun suka rufa masa baya. Mai makon in yi shiru nima sai na bude murya da karfi ina cewa "eho yaji tsoro a bashi ruwan madaci ya kuskure da na gyambo! Su kuma ragowar fursunonin sai suka ɓarke da shewa da tafi, yayin da wasu kuma suka dinga fito da kiɗe_kiɗe gami da raye_raye.
Banyi wata_wata ba na kwance ɗaurin dake ƙafata don dama ba wani ɗaurin kirki bane. Bayan na kwance ɗaurin ne sai na waiga inda Imran yake domin inga halin da yake ciki. Ai kuwa sai naga abin mamaki, Imran ya jiƙe sharkaf da gumi ga hawaye sai fita suke daga idanuwansa tamkar an doke shi.
Shin mene ne ya sa Imran ya jiƙe sharkaf da gumi kuma yake wannan hawaye?
Ina labarin Sadiya?
Ina labarin SARAUNIYA Diana?
Ya zata ƙare a tsakanin mu da shugaban dakaru?
Mene ne yasa ragowar fursunonin ke shewa da murna?
Me yasa Sarauniya Diana bata ƙara yarda mun haɗu ba?
Zan Ci Gaba In Shaa Allaah
_*Phone:*_
08185819176
_*Web:*_ www.haiman.com.ng
_*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees
_*Twitter:*_ @HaimanRaees
_*Instagram:*_ Haimanraees
_*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲
♻♻ *PWA* ♻♻




0 Comments: