🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲
♻♻ *PWA* ♻♻
_08185819176_
••••••••••••••••••••••••••••••
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
*BIRNIN SAHARA*
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
••••••••••••••••••••••••••••••
________________________________________
_______________________
*ѕtσrч/wríttєn ву✍🏻:*
👉🏻© *_Haiman Khan Raees_*
(℘ᾰ❡ḙ 6)
Cikin hanzari na ruga ind Imran Yake na dafa kafaɗarsa ina mai cewa: ''ya kai Imran mene ne ya same ka haka kake ta wannan uban gumi kamar wanda ya haɗiyi kunama?''
Maimakon Imran ya bani amsa, kawai sai ya sake ɓarkewa da kuka abinsa.
Koda naga haka sai na miƙe tsaye ina mai cewa: ''Kaga Imran, kodai ka sanar dani abinda yake faruwa ko kuma in ƙyaleka inyi tafiyata tunda kaga na kwance kaina''.
Koda jin wannan batu, sai nan da nan Imran ya natsu sannan ya ɗago kai ya dube ni. Har a wannan lokaci idanuwansa basu daina zubo da hawaye ba. Bayan wani ɗan lokaci sa ya buɗi baki cikin wata irin raunananniyar murya yace dani: ''Ya kai Haiman kasani cewa ka tono tsuliyar dodo kuma ka ɗauko ruwan dafa kanka sannan kuma ka shafamin kashin kaji sababin baƙaƙen maganganun da ka furtawa wannan shugaban dakaru,''
''kai dai kawai ka tsorata da shi ne Imran, amma babu wata damuwa dangane da maganganun da na gaya masa,'' na bashi amsa cike da nuna tsantsar rashin damuwa. ''hmm Haiman kenan, Imran ya faɗi yana mai murmushin takaici, sannan yace dani ''watau Haiman na fuskanci baka san ko wanene wannan shugaban 'yan fashin ba ko?
''Waye shi? Na tambaye shi.
''Sadauki Dargazu kenan in baka sani ba ka sani.
''Haha! Dargazu kuma ? Wannan wane irin sunane haka?
''Idan har zan baka amsar wannan tambayar, to hakan na nufin sai na baka tarihinsa koda kaɗan ne domin ka fahimci irin mummunan Jafa'in da ka jefa mu ciki.
Ganin yana nema ya tsinke da Labarin da ba shine a gaba na ba yasa nace mishi "malam dakata! Ni fa yanzu babban Buri na shi ne in fita daga wurin nan in kama kaina, kai kuma sai kokarin bani wani labari kake yi, kai kasan irin bakin cikin da nake ciki sakamakon bakin yanayin Da Masoyiyata ta shiga a sanadi na kuwa? Kasan wane irin hali Mahaifana zasu shiga in suka neme ni suka rasa? Kawai ka daina wannan KUKAN dadin ka zo mu hada hannu mu fita a wurin nan". Duk I wannan zance nawa na yi shi ne cikin Harzuka saboda gani nake bata min lokaci kawai zai yi.
Har na gama wannan bayani nawa kan Imran yana Sunkuye bai Dago ba kuma bai ce komai ba, can bayan wani dan lokaci sai ya dago kansa, abinda nagani a wannan lokacin ba karamin tayar min da hankali yayi ba domin sai da na Razana.
Ba komai na gani ba face tsantsar Fusata da Harzuka da suka bayyana karara a fuskar Imran, idanuwan sa sun kada sunyi Ja kamar an ciro karfe daga wutar makera. Cikin wata irin Fusatacciyar Murya mai cike da bacin rai ya fara magana da cewa:
"Kai Don Tsabar Duhun JAHILCI da ya maka yawa har ni zaka gayawa zafin rasa masoyi? Ni zaka nunawa damuwa da mahaifa? Ni zaka nunawa zafin rai? A Yayinda yake wannan maganar yana yin ta ne yana MATSOwa inda nake ba tare da ya ma sani ba. A zahiri ni fa bana wuce Kalubale don haka Abu na farko da Zuciya ta ta Raya min shi ne in mayar masa da martani in yaso ayi wadda za'a yi Bera ya zubar da garin Kyanwa. Amma sai nayi tunanin kada fa in kara sanya kaina cikin wata Jarfar, don haka kawai sai na kwantar da kai na bude baki cikin murya mai taushi nace da shi: ka Gafarce ni yakai Imran, ka sani cewa ni na kasance yaro ne mai karancin hankali da sanin ya kamata, don haka ka manta kawai da abinda ya faru ka bani labarin da kace zaka bani matukar hakan zai bamu damar fita daga wurin nan.
Yayinda Imran yaji na tausasa kalamai na, sai ya Koma inda yake tun da farko ya zauna ba tare da cewa komaiba. Ganin haka yasa nayi wata Sassanyar ajiyar zuciya sannan nima na samu wuri na zauna kawai na zubawa Imran ido.
Bayan wani dan lokaci, sai Imran yayi gyaran murya sannan ya fara bani labari kamar haka:
Zan Ci Gaba In Shaa Allaah
_*Phone:*_
08185819176
_*Web:*_ www.haiman.com.ng
_*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees
_*Twitter:*_ @HaimanRaees
_*Instagram:*_ Haimanraees
_*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲
♻♻ *PWA* ♻♻




0 Comments: