Tuesday, 1 May 2018




BIRNIN SAHARA 7

Home BIRNIN SAHARA 7
🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲

♻♻ *PWA* ♻♻

_08185819176_

••••••••••••••••••••••••••••••
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
     *BIRNIN SAHARA*
🏜🏜🏜🏜🏜🏜🏜
••••••••••••••••••••••••••••••

             ________________________________________


   _______________________
         *ѕtσrч/wríttєn ву✍🏻:*
👉🏻© *_Haiman Khan Raees_*
        

            (℘ᾰ❡ḙ 7)

_______________


Sai Imran yayi gyaran murya sannan ya fara bani labari kamar haka:

''Dargazu ya kasance ɗa ne ga sarkin yaƙin wannan birni mai suna Darmusa, kuma a tarihin zuriyarsu ba'a taɓa samun rago ba walau mace ko namiji.

Duk wanda ya fito daga gidan sai ya kasance Sadaukin gaske, babu iya ƙoƙarin da Matsafa da masu bincike basu yi ba domin ganin sun gano sirrin zuriyarsu da kuma yadda za'a samu galaba akansu amma abu ya faskara.
Wani abin mamaki dangane da zuri'ar su Dargazu shine, basu taɓa Jagorantar Rundunar yaƙi aka fita ba tare da An sami Nasara ba, kuma ba'a taɓa kashe koda mutum ɗaya daga cikin zuri'ar tasu a fagen yaƙi ba, sai dai cuta ta kwantar dashi ko kuma kawai a wayi gari ya mutu ba tare da an san dalili ba.

Kimanin shekaru uku da suka gabata, wata rana da sanyin safiya Dakarun Birnin Sahara suka farwa Birnin mu da harin sumame ba tare da mun ankara ba. Koda yake sojojin mu sunyi matukar kokari wajen ganin sun kare martabar ƙasar su tare da dukiyoyin su da iyalan su, amma sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, domin sun ninka mu yawa fiye da ƙima. Daga ƙarshe dai muna ji muna gani aka kama mu a matsayin bayi bayan an kashe mana iyalan mu, a kan idona aka yanka Iyaye na, kuma akan idona Mukarrabban Dargazu su talatin suka Keta Mutuncin matata wacce sanadin Mutuwar ta kenan.

Hakan yasa nayi yunƙurin ganin na hallaka shi da karfin tsafin da na gada daga mahaifina ta hanyar ƙamar dashi izuwa gunki.

Ganin faruwar wannan al'amari ne yasa dakarun Sarauniya Diana suka kama ni tare da ƙanwata guda ɗaya da ta rage a duniya mai suna Humailat, dakarun sun yimin barazanar cewa idan har ban dawo da Dargazu kamar yadda yake a da ba to zasu aikatawa ƙanwata abinda suka aikatawa matata.

Haiman ka sani cewa a duniya bayan mahaifana babu abin da nake so Sama da ƙanwata don haka banda wani zaɓi face na inyi abin da suke so. A lokacin da na dawo da Dargazu mutum ne sai ya ɗauke Humailat ya tafi tare da ita, yayinda ni kuma yayi ta gana min azaba iri-iri tun a hanya kafin mu iso nan.

Bayan mun ƙara so ne sai ya bayyanawa Sarauniya Diana abin da ya faru, da farko taso tasa a hallaka ni, domin a cewarta wai na tozarta Darajar Dargazu a gaban yaransa, amma sai wani Bokanta dake bata shawarwari akan sha'anin Mulkinta ya ce mata kada ta kashe ni wai a cewar sa zanyi mata amfani anan gaba. Daga wannan rana Bokan Sarauniya Ya maida ni tsoho kamar yadda kake ganina haka, shi kuma Dargazu ganin yadda Diana ta fasa kashe ni sai abin ya ba shi haushi, kuma tun daga wannan rana gaba mai tsanani ta shiga tsakanin mu da shi sannan yayi alƙawarin sai ya hallaka ni tare da ƙanwata.

Ga shi yanzu ka ƙara jawo min wata masifar, ni babban ma abin da yafi damuna shine: yau shekaru uku kenan da kawo ni nan amma ko labarin Humailat ban ƙara jin wani yayi ba ballantana ma in san a wani hali take. 

Akwai wani Fursuna da aka kawo nan, shi ne ya fara bani labari dangane da Addinin Musulunci, sai dai ban kai ga Amsar Addinin ba aka zo aka tafi dashi Alhalin har na fara aminta da wannan Addini. 

Kai! Gaskiya ni ta qare min!! Imran ya ƙarasa bayaninsa yayin da ya sake ɓarkewa da kuka mai ratsa zuciyar duk wani mai imani.

A wannan lokaci jikina yayi sanyi matuƙa da jin wannan labari na Imran don haka sai na shiga rarrashin sa ina mai cewa: ''Ya kai Imran, Ka kwantar da hankalinka'', matuƙar ina nan a raye nayi maka alƙawarin saina ƙwato maka Kanwarka daga hannun Wannan Azzalumin Sadauki domin nima ƙanwata ce, kuma nima Ma'abocin Addinin Musulunci don haka kasa a ranka ka zama musulmi da yardar Allaah, abin da kawai nake so kamin shine: kayi min Alƙawarin zaka karɓi addinin Musulunci da gaske ba da wasa ba kuma zaka yi iya bakin kokarin ka wajen ganin ka yada Addinin domin akwai lada mai yawa a cikin hakan. 

Koda jin wannan batu nawa, sai Imran ya kawo gwauron Numfashi ya ajiye sannan yace ''Hmm.. Haiman kenan, ya faɗi yana mai murmushin yaƙe, Sannan sai ya ci gaba da cewa: ''Haiman ina so ka sani cewa, wannan maganar fa ba wai bada labari bane kawai, magana ce ta jarumta tare da nuna isa gami da ƙarfin mulki wanda kai baka da ko ɗaya daga cikin su, tayaya kake tsammanin zaka iya ƙwato min ƙanwata a haka?

''Imran kai dai kawai ka yarda domin ni nasan abinda baka sani ba''. Na bashi amsa ina mai murmushi.

''Kai kuwa mene ne ka sani wanda ban sani ba? Imran ya tambaya cike da mamaki. ''Kada ka damu Imran, lokaci zai baka amsar tambayoyinka, yanzu abin da nake so da kai shine, ka mai maita abinda zan fada maka kana mai aminta da hakan har cikin Zuciyar ka. 

Imran yace "to", daga nan na biya masa kalmar Shahada ya Maimaita. 

Ai kuwa yana gama Maimaitawa sai wani irin bakin hayaki ya lulluɓe shi, bayan wani dan lokaci sai hayakin ya Yaye, kawai sai ga Imran ya dawo Kyakkyawan saurayi majiyin Karfi. 

Ganin wannan al'amari ne yasa Imran ya Wangame baki kamar Bako a birnin Madina, can daga baya sai yace "Kai Haiman! Wannan wani irin SIHIRI ne ka aikata a gare ni? 

Ko da jin haka, sai nayi murmushi sannan nace da shi; wannan ba aikin SIHIRI bane, ikon Allaah Kenan! Abinda ka fada shi ne ya jawo sanadiyar Karyewar aikin Sihirin da aka yi maka. Cewa kayi ka Yarda cewa babu wani abun bautawa da gaskiya sai Allaah, kuma Annabin Sa Muhammad Lallai bawan Sa Ne Kuma Manzon Sa ne! 

Ko da jin wannan batu nawa, sai Imran ya Rungume ni cikin farinciki yana mai cewa; "Lallai Wannan Allaah kuwa da girma yake! 

Ni kuma sai na bashi amsa da cewa; ai wannan ma kadan kenan ka gani daga cikin ikon sa! Daga nan sai na cigaba da yiwa Imran bayanin dokokin Addinin Musulunci da abinda SHARI'AR MUSULUNCI tace akan Muhimman abubuwan da suka shafi rayuwar kowane musulmi. 


Wannan shine abinda ya faru a tsakanina da Imran, matashin da aka maida shi tsoho kuma tsohon abokin gabar Dargazu.

Shin zamu iya fita daga wannan ɗakin lafiya?

Shin Ya labarin Kanwar Imran Humailat?

Me zai faru idan muka haɗu da Dargazu?


Zan Ci Gaba In Shaa Allaah 

_*Phone:*_
 08185819176

_*Web:*_ www.haiman.com.ng 

_*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees 

_*Twitter:*_ @HaimanRaees 

_*Instagram:*_ Haimanraees 

_*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com


🌲🌲*_PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION_*🌲🌲

♻♻ *PWA* ♻♻




Share this


Author: verified_user

0 Comments: