TAMBAYA TA 17
Post By:
Hausa Novels
Tambaya Mabudin Ilimi
TAMBAYA ======== 👇 Assalamu alaikum malam dan Allah inaneman shawara akan zamantakewar aure aure za.amin acikin wannan satin nagode. AMSA ===== 👇 To yar uwa naji dadin wannan tambayar, Sabida da alama kin shirya zaman aure ne ba shiririta ba. Shiyasa ma kike neman shawarwari na gari. Na farko dai yar uwa, ki yadda da cewar zaman aure, zama ne na hakuri, hakuri da kishiya, hakuri da miji, hakuri da yayan mijin da kika aura, hakuri da makwabtansa, hakuri da yan uwansa da dai sauransu. Kike Kyautatawa iyayen mijinki da yan uwansa, kina bin mijinki sau da kafa, bin umarninsu, hanuwa akan hanin da yayi miki. Kike Tsaftace gida da daki da jikinki, Tsaftace zuciyarki da imaninki. Karki dauki zuga wadda xa'a kaiki ga cin mutuncin mijinki ko kishiyarki ko yan uwan mijinki ko yan uwan kishiyarki. Kyautata girki mai dadi kuma akan lokacin da mai gida yake bukata, kinsan mu MAZA🕺 muna son abinci mai dadi. Godiya da yabawa mai gida akan duk abinda ya kawo miki, karki zama mai renuwa akan duk abinda mai gida ya kawo miki. Karki fita sai da izinin mai gidanki, inda kika tambaya kuma nan zakije, karki wuce inda baki tambayi mijinki ba. Ba kowacce unguwa bane yake fita da mace daga gidan mijinta ba, Sabida wasu matan suna lalata Nasu auren, Su gyara na wata. Karki dorawa mijinki abinda bazai iya yimiki ba. Ki cire kyashi da kwadayi da zalama da kwawa da naci akan abida bazai amfanar dake duniyarki da lahirarki ba. Ki guji bacin ran mijinki komin kankantarsa. Karki shigar da wani gidansa sai da izininsa, karki baiwa wani dama ya shiga gidanki bare ya wuce dakin da kike surru ke da mai gidanki ba, sai da izinin mai gidanki. Ki kula da sallar nafila da addu'o'i na Alkairi akan Allah ya budawa mijinki da sauran musulman duniya gabaki daya. Da Addu'ar Allah yaci gaba da kawo muku zaman lafiya, ya tsareku daga sharrin shaidan. Ki kula da azumin nafila idan zaki iyayi, ki kula da dukiyar mijinki, tufafinsa, kudinsa, gidansa, da duk wani abinda ya kawo gidansa. Allah ya baku zaman lafiya, yasa Alkairi acikin aurenku. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876



0 Comments: