TAMBAYA TA 16
Post By:
Hausa Novels
Tambaya Mabudin Ilimi
TAMBAYA ======== đ malam ina so zan fara yin director a masina antar shirya fina finan hausa ta kanywood shine nake neman shawara daga gare ka, sannan inoso ka fada min ce wa wai shin wannan si na ar ta hallata ko bata halatta ba domin ina gudun shiga cikin haram tacciyar si na a huta lfy. AMSA ===== đ Wannan Haramun ne gaskiya. Sabida haka ka nemi sana'a gaskiya. Ba sai na fadada bayanai ba, ko Su yan films sunsan abinda sukeyi ba daidai bane. Suna Bada gudunmawa wajen lalata tarbiyyar al'ummar musulmi. Wanda da ace yan matan da suke yin film zasuyi aure Su zauna a gidajen mazajensu suje chan Su nemi aljannarsu a tafin kafar mazajensu kamar yadda sauran mata suke zaune a gidajensu, kuma suma mazajen da suke yin film Su kama sana'ar da musulunci ya yarda da ita, to da hakan zaifi musu Alkairi. Wasu suna cewa wai yan film wa'azi sukeyi. Ni kuma Ina mamaki da wannan lamarin. Tayaya matar da ta kasa zaman aure, zata yiwa wata wa'azi akan zaman aure? Ta yaya wanda zai fito a film yana shan taba a idon mutane kuma ace yana yiwa wani wa'azi akan ya dena shaye-shaye.? Ta yaya mutum zaiyi aski na banza akansa wanda musulunci yaja hankalin mai yin irin wannan askin, kuma ace wai wa'azi yake yiwa wasu mutane? Ta yaya mutum yana rawa da mace tayi shigar banza, ta Dame jikinta kuma suce wai wa'azi suke yiwa yan mata da samari.? Kaga wannan ma ae wasa ne ma da tunanin mutane. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876



0 Comments: