TAMBAYA TA 15
Post By:
Hausa Novels
Tambaya Mabudin Ilimi
TAMBAYA ======== đ Aslm mal. Wani yanayi NE inmace nada ciki miji bazai saketa ba. AMSA ====== đ Akwai yanayin da idan mijin ya saki matarsa to anan ya aikata Haramun, sannan kuma akwai yanayin da idan mutum ya saki matarsa ya aikata abinda bai dace ba. Misalin mutumin da ya saki matarsa alhalin tana cikin jini, anan ya aikata Haramun. Sabida hadisi ruwayar Bukhari da Muslim daga Abdullahi Dan umar Allah ya kara masa yarda yace, lokacin da ya saki matarsa alhalin tana cikin jini, sai mahaifinsa umar ya tambayi manzon Allah saw, nan da nan manzon Allah yace ka umarceshi ya maidata. Da wannan ne ma babu sabani a wurin Malamai akan cewar ya zama wajibi nan da nan za'a maidata. Inda wasu suke ganin wannan sakin ba za'a sanyashi a cikin lissafi ba, daga cikin masu wannan ra'ayin akwai shaikul Islam ibn taimiyya, da ibnil kayyimun jauziyya da sauransu, Sabida manzon Allah saw ya ambaci wannan sakin da suna sakin bidi'a. Ita kuma. Bidi'a ba'a karbarta ta kowacce fuska. Wadansu malaman kuma suna ganin kamar wannan sakin za'a sanyashi a cikin lissafi, amma za'a maidata, idan kuma na ukku ne to ba za'a maidata ba, daga cikin masu irin wannan ra'ayin akwai malaman mazahaba gabaki daya, Mala'iku, abu haniyfa, imamushshafi'iy da Ahmad ibn harbal. Wannan bayanin idan ka duba littafin, FIQHUL WAZIH ALA MAZAHIBUL ARBA'A ZAKA SAMI WANNAN BAYANIN da FATAWA WA AHKAMUL MAR'ATIL MUSLIMA da Kuma IHKAMUL AHKAM sharhu Umdatul Ahkam. Sannan yana daga lokacin da bai dace mutum ya saki matarsa ba, sannan kuma idan har ya saketa a irin wannan lokacin bata saku ba indai har mutum ya saki matarsa, shine idan yana cikin rashin lafiya, yaga ba makawa mutuwa zaiyi, sai Malamai sukace ya saketa ne Dan ya haramta mata cin gadonsa, anan ma Malamai sukace bata saku ba, Wannan shine bayanin da Malamai sukayi. Sakin da Kuma bai kamata ba shine, mutum ya saki matarsa alhalin bata masa komi ba, haka kawai Dan yaga wata zai aura, indai ba da wani dalili ba, Wannan zaisa sunansa ya baci a idon mutane, kenan ya zama mai auri saki, sannan mata basa ganewa, Sabida duk lokacin da namiji ya saki wata, Sabida zai aureki, to kema haka zai miki, da yaga wata kema sakinki zaiyi. Amma Su mata suna ganin kamar burgewa ne Ace an sai wata Sabida ita zata shiga gidan. Allah ya sawwake. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876



0 Comments: