TAMBAYA TA 14
Post By:
Hausa Novels
Tambaya Mabudin Ilimi
TAMBAYA ======== đ Assalamu Alaikum warahmatullah fatan mallam ya tashi lafiya. Tambaya ta itace kawata ce sun kusan shekara suna case da mijin ta a kotu daga karshe sai aka raba auren sai bayan sati uku kuma ta koma alkali ya bata takardan sakin to shin.. 1.akwai idda a kan ta? 2.daga lokacin da alkalin ya raba auren ne zata fara idda ko kuma lokacin da ta karbi takardar sakin ne zata fara?..Nagode AMSA ===== đ Daga lokacin da sakon saki yazo mata a rubuce ko da fatar baki, daga nan ne zata fara lissafin iddarta insha Allahu. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876



0 Comments: