TAMBAYA TA 13
Post By:
Hausa Novels
Tambaya Mabudin Ilimi
TAMBAYA ======== đ Assalam alaikum, Mallam awarwaremin wannan shubuhar? Mallam idan ina rokon Allah wadata sai naga akwai wadanda Sun fini falala su baibasuba Ina nikuma Mai yawan sabo? don haka atunanina su sukafi cancanta da wata sama dani. Mallam awarwaremin wannan shubuhar.. AMSA ===== đ Na farko dai Allah ya rabawa kowa rabonsa na arziki da lafiya da dabi'a tin yana cikin mahaifiyarsa. Inda ace soyayya ce take sanyawa Allah ya yiwa mutum arziki da bai baiwa kafiri ko daya ba. Amma da yake hikima ce irin ta ubangiji yana baiwa wanda yaso Arne ko musulmi. Ko ya baiwa musulmi ya hana arne ko ya hana arne ya baiwa musulmi, ko ya baiwa mace ya hana namiji, ko ya baiwa namiji ya hana mace ko ya baiwa yaro ya hana babba ko ya baiwa babba ya hana yaro, duk wannan hikimarsa ce, Allahu subhanahu wata'ala. Sannan da talauci kiyayya ne daga Allah, to da manzon Allah saw sai yafi kowa kudi a tarihin duniya, amma ya rayu cikin talaucin da ana wata ukku a gidansa ba'a dora tukunya ba Sabida babu. Kenan arzikin ka ko kana gudu zai bika ya kamoka tinda Allah ya kaddara Maka hakan, sannan abinda ba'a kaddara Maka ba komin yadda kake nemansa bazaka sameshi ba. Ko barawo da kake gani, idan yayi sata ba'a kamashi ba, da Ace zaiyi hakuri to wannan abinda ya dauka daman yana daga cikin arzikin da Allah ya kaddara zai samu, da yayi hakuri, Allah zai bashi ta hanyar halak, amma sai ya kasa yin hakuri. Haka idan barawo yayi sata aka kamashi aka kwace abinda ya sata, to daman ba rabonsa bane, da yayi hakuri ma, Wannan abinda ya sata din Allah bazai bashi ba, tinda baya daga cikin arzikinsa, kuma har abada baxai samu ba. Sabida haka, Wannan bazai hana ka roki Allah yayi Maka arziki ba, amma da zaka nemi lahira shine yafi Maka Alkairi, Allah yace LAHIRA ITACE TAFI DAWWAMA GA BAWA. duk da cewar ana samun aljannah ta hanyar dukiya, idan mai ita yake bayar da sadaka da ita, da zamunci da kyauta da dai sauransu. Amma zakaga wani an bashi dukiyar ma, bai wadata kansa ba, bai wadata iyalinsa ba, bai wadata yan uwansa ba, bai wadata kowa ba, baya taimako, shi kansa baici ba. Kaga idan aka baka irin wannan dukiyar ae ka sami matsala. Amma dai ka nema sai Allah ya baka, kuma ka ciyar da abinda Allah ya baka, sai ka shiga aljannar masu kudi a lahira. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876



0 Comments: