Friday, 6 April 2018




TAMBAYA TA 12

Home TAMBAYA TA 12
TAMBAYA ======== 👇 Aslm malam dan Allah tambaya ta ita ce.Shin nafilolin da aka ce muyi kafin da kuma bayan sallar farilla shin sai nayi dukkan su yadda aka fada ko kuwa zan iya yin wacce na samu dama nayi wato wasu daga cikin su. AMSA ===== 👇 Hadisi ya tabbata manzon Allah saw yace, duk wanda yayi sallar nafila raka'a 12 a cikin dare d yini, Allah zai gida masa gida a aljannah. Ga yadda suke :- Kafin asubahi raka'a 2 Kafin azuhur raka'a 4 Bayan azuhur raka'a 2 Bayan magariba raka 2 Bayan isha'i raka'a 2 Idan ka hada sun zama raka'a 12. Sannan ana yinsu ne a daidai lokacin da aka umarcemu, ba yadda muka gadama ba. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share this


Author: verified_user

0 Comments: