Friday, 6 April 2018




TAMBAYA TA 11

Home TAMBAYA TA 11
TAMBAYA ======== 👇 Salam malam barka d warhaka muna jin dadin wannan zaure ubangiji Allah y kara basira malam tambaya ta itace menene hukuncin kitson roba watau (Sangas)hukuncinsa akan wankan janaba Allah y Kara ma malam Lafiya .mungode wassalam. AMSA ====== 👇 Duk kitson da akayi kuma ya rufe gashi gabaki daya, ta yadda mod an zuba ruwa bazai shiga ba, Sabida matsewar wannana robar a jikin gashin, dole idan akazo wankan tsarki sai an warwareshi, idan kuma wanda kike nufi na Sangas shi akwai space idan akazo daure gashi, kenan ruwa zai sami damar shiga cikin gashin kanki, Wannan ba sai an warwareshi ba idan akazo wanka. Kuma ba wani abu, tinda shi daure gashi ne ba karin gashi ba, daman abinda aka hana shine, karin gashi. Ko karin roba ko Karin zare. Allah shine masani. ✍ ZAUREN ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share this


Author: verified_user

0 Comments: