Friday, 6 April 2018




TAMBAYA TA 30

Home TAMBAYA TA 30
TAMBAYA ======== 👇 Malam dan Allah ina tmby ne akan tsintuwa, daga wanne adadin kudine yakamata mutum yayi cigiya idan yatsinta? Mutum ne yatsinci 750 Dari bakwai da hamsin zaici ne kokuwa sadaka zaiyi da kudin kokuwa zaiyita cigiya ne? AMSA ===== 👇 Ya danganta da girman gari. Idan ka tsinci 1000 a gari kamar Kano, ko Kaduna, misali da garinda yake da kusan girma irin wadannan garin, bazakayi cigiya ba, amma idan a kauye koda 500 ko 200 ka tsinta zakayi cigiya. Sabida ya taba faruwa manxon Allah s.a.w suna tafiya da hussain ibn Aliyu bin Abi dalib ya tsinci dabino, har ya kai bakinsa zaici sai manzon Allah saw ya tankwabeshi daga hannunsa ya fadi kasa, sannan yace BADAN INA TUNANIN KO NA SADAKA BANCE, DA NA BARKA KACI. kaga manzon Allah baice da nayi cigiya ba. Sabisa Su Haramun ne suci sadaka AHLIL BAITI. Allah shine masani. ✍ ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Share this


Author: verified_user

0 Comments: